CHAPTER 54 (FINALE)
Baiwar tace mene? Suka ce eh mai martaba ya gaiyace ta. Baiwar tace in haka ne toh ai labari ya canja kuma magana ta girmama kenan sabuwar kwarkwarar sarki , laila TANA DA KW*RTO?
Ranta dadi domin tasan cewa in ta kawo labarin nan za'a bata kyauta me tsoka. Komawa tayi da labarin ta gari na waye wa ta dawo nan fa ta sanar da dayar mantar sarki mai suna suraiya.
Cikin jin dadi suraiya ta ma kasa zama tace aiko yanzu zan koma na sanar da me martaba da sauri bayin ta suka ce ya shugaba bamu da sheda kinsan in bazamu iya bada shedu 4 ba bulala ta hau kan mu. Suraiya tace kuma kun fadi gaskiya toh yanzu ya zamuyi?
Daya daga cikin su tace me zai hana a sa mata ido duk maotsin ta ai dole ta bamu wani abin zargi. Suraiya tace haka za'ayi da kaina zan dinga zuwa mata yini ta Allah ba nata ba.
A take ma ta tafi bangaren munira bata dawo ba sai dare bayan ta tabbatar ta sanar da yan sa ido su saka daga yazo su kira mai martaba su garkame kofofi.
Saide fa kamar yarima ya sani har kwana 13 ya wuce bai zo ba sau biyu yazo da rana amma jin muryan sauran matan baya kwankwasawq in de yaji muryan munira ya tabbatar lafiyan ta kalau shikenan.
Saide hakan ya damu munira gashi yanzu bata da sakat kamar da inde zata fita sai da bayi dama ko taje wajen yarima ko su asma ne toh suna zuwa wajen ta.
Gashi bata da sakat dan kullum kafar siraiya yana gidan gata da kaudin tsiya. Munira kuma batason tace zata fita suraiya taga kamar ta wulakan ta ta. Itako suraiya ta dage dan gani take randa bata zo ba ranan zaizo. Toh amma in daya daga cikin fadawan fada ne fa?
Bazai zo ba ai tunda yasan tana nan mai zai hana kar tazo gobe ta mike zata yi wa munira sallama munira ta sake rugawa ban daki da gudu tana harar wa. Wani abu ne ya fadowa suraiya idan ta lura jiya da daddare munira tayi amai bayan sunci abinci sai suka barshi a cewa man shanun dake ciki ne.
Yau sau uku tana harar wa duk sanda zata yi alwala suraiya bata lura ba amma yanzu kam. Wani ras taji kar de cikin mai martaba ne da ita? Wannan wani irin shan layi ne haka?
A zauce ta fita ta ma rasa me zata yi bayan sun iso barinta baiwarta tace me zai hana mu rubar da sauri suraiya ta mare ta tace ke mahaukaciya duk rsshin imani na bazan iya yin kisa ba bazan iya yin shirka ba ai kishin ba hauka bane.
Da sauri baiwar ta russuna kai tace tuba nake shugaba ta subutan baki nayi. Niko nace kaji yar air bata gari banza. Wannan maganan ds baiwar tayi yasa suraiya taji jikin ta yayi sanyi tayi nadamar sa idon da tayi wa munira toh amma namijin da aka ji a dakin ta fa? Da sauri ta kalli baiwar tace kar ki ce min batun nan ma kazafi kika mata?
Da sauri ta girgiza kai tace wallahi gaskiya na fada shugaba ta . Kwafa suraiya tayi bata de gama yarda da baiwar ba. Amma ta sha alwashin ta cire hannun ta daga al'amarin kami ta kife da ita. A hakikanin gaskiya ma munira tana dan burgeta dan duk zuwan su dukda munira tasan takurar ta suke bata taba nuna musu gajiyawa ba.
Bata taba nuna ta gaji ba tana da kawaici. Suraiya haka ta dunga nazari toh yanzu ta zauna da zuciya daya da munira taje da gaske mazinaciya ce ya kwabe da ita? Tayi shiru ne ko ta fada? Tagumi tayi tace Allah ka yafe min rashin Ilimi na jahilci mugun abu ne yanzu dubani ban ma san me ya kamata nayi idan ana zargin mutum da zina ba.
Bari nayi shiru kawai.... toh amma fa abu daya da na sani shine ko mata zina tayi da de dan mijin ta ne. Dan haka.... da sauri tasa aka nemo mai magani ba bata lokaci suka tabbatar mata da zargin ta ba shakka munira tana da ciki ai bata yi wata wata ba dare yana yi ta nufi wajen mai martaba dukda ba'a kira ta ba.
Tana shiga ya kalle ta da murmushi yace surwiya lafiya dai ko ? Kina da wani matsala ne ? Girgiza kai tayi tace albishir na zo maka dashi mai martaba yace toh Allah yasa muji me kyau. Zama tayi a gefen sa tace zamu samu karuwa murmushin dake fuskan sa ne ya fadada yace kina da juna biyu? Girgiza kai tayi da sauri tace ba ni bace yace wace?
Tace kanwata ce, dariya yayi yace ai kannen naki yawa gare su tace lailar mu ce. Take dariyan sa ya dauke tare da mikewa ya zauna yace ban gane laila ba. Tace laila mana sabuwar kanwata yanzu na kira shugaban ingozomomi ta tabbatar min kamin nace bari na zamto ni zan fara taya ka murna.
Yake ya mata yace gaskiya kinyi abu me kyau kije ni zan huta tace baka min kyauta ba yace gobe zan baki kinji? Da jin dadin ta tace toh godiya nake ita sam bata ma lura da sauyin yana yin sa ba. Kawai tayi tafiyar ta tana tunanin abun da zata tambaya matsayin kyautar ta.
Mai martaba kuwa ba bata lokaci ya nemo shugaban ingozomomi ta tabbar masa yaji da kunnen sa. Shi da yake shirye shiryen mayar da ita matar sa ta 3 a daura musu aure wannan wani irin abu yake ji. Dafe gefen kirjin sa yayi numfashin sa na canjawa ya rubuta waraka da hannun sa ya aika wa waziri cewa gobe kar a kawo ni al'amuran shugaban ci. Wannan ba fatimar sa bace sam ba ita bace kwantawa kawai yayi a haka har bacci ya kwashe shi yaki yayi.tunanin komai.
Munira kuwa taji me ingozoma tace dan haka dan haka sai jiran yarima take.ai kuwa wannan karan ko da yazo yaji shiru kusan dakika goma kwankwasawa yayi kamin ya gama munira tace shigo shigo mijina shigo.
Jin haka yasa yarima ya shigo da sauri har yana kurje guiwa ya fito daga kasan gado yace lafiya hannun shi ta rike tace zamu zama iyaye ruru zamu zama iyaye! Yarima yace kice Allah. Da sauri ta gyada kai yace Alhamdulillah maza sa takalmin ki yanzu kam dole ne muje muyi wa mahaifina bayani dama mako 2 nake jira nasan zuwa lokacin in mun fada masa bazai masa illa ba.
Munira gobe sai ka fada masa... me yasa baka zuwa... ? kodan gara ma da baka zo ba.... yace nakan zo amma ina jin hayanin su suraiya shiyasa bana shigowa..daga nan suka canja zuwa hiran sunan da zasu sawa dan ko yar....
Safiya na zuwa yarima ya shiga wajen mai martaba a fada bayan sun gaisa yana kokarin ya nemi kebencewa dashi amma sai yayi tunanin kar wani abu ya same shi ace kokarin kashe sa yayi kawai sai ya fasa. Daidai lokacin aka shigo da munira kamar kaza tana fadin ku sake ni me nayi ne ganin ta cirko cirko cikin maza ga wasu lafiyaoyaun bayi mata guda biyu a gefen ta suna muzurai bata taba ganin su ba sai ranan.
Sarki yace idan zaku iya tunawa wata daya da wasu makonni da suka wuce na dauki laila a matsayin kwarkwara ta kuma har nake shirin auren ta saide tunda nake ba abinda ya shiga tsakanin mu. Matsalar shine jiya shugaban ingozomomi ta tabbatar min cewa tana dauke da juna biyu. Dan haka dole ne na kawar da kazan ta irin ta daga kasa ta.
Munira na jin haka yaushe zata bari ta mutu bata ga dan ta ba dan haka tace Mai martaba kayi min afuwa kayi min rai karka kashe ni. Cikin izza sarki da kansa ya sauko zai falla Mata mari yana fadin mutuwa ta wajabta a gareki maciyiya amanar sarki.
Kabir ne ne ya rike hannun sa yace mai martaba kazantar ta yafi karfin ka daura hannun ka a kanta. Najasa ce!
Da kafa kabir ya hankadeta tare da fadin dogarawa ku kamata ku daure ta kar a bata ruwa na awa talatin sannan a dinga Mata bulala 10 bayan awa daya bayan awa 30 din ku daba mata mashi a ciki ku tabbata ta soki mahaifarta ya fito a zubar da shegen da ke cikin jikinta a tabbatar ta fadi waye ubana idan ba haka ba a dinga yankan naman jikin ta har sai ta fita daga haiyacin ta!
Kamin ya rufe baki yaji an dauke shi da wani zazzafan Mari Wanda yasa har sanda ya rufe idon sa. Cikin kururuwa yarima Umar yace naga Wanda ya isa ya taba ta. Wannan cikin nawa ne kuma banga Wanda ya isa ya taba min jini ba!
Shiru wajen ya dauka domin kowa ya sha jinin jikinsa cikin rawar baki mai martaba yace kai Umar me kace? Yarima yace Allah ya kafarta wa ABBA wannan cikin nawa ne. Zaman dabas mai martaba yayi tare da sauke kai. Bayan wasu dakinku cikin wani kururuwa yace SHIMA KU KASHE SHI!
Da sauri waziri yace mai martaba kar kayi hukunci cikin fushi. A ka'ida ba kashe sa za'a yi bashida aure fa.... datse shi yarima yayi yace ina da shi. Zuba masa ido kowa yayi jin me yace. Kamar ya yana da aure? Kamin su dawo dai dai yace matata ce ita. Nan yarima ya kwararo jawabi kusan na minti talatin Allah ya gani banda karfin rubutawa amma de a takaice bayani ya musu.
Mai martaba shiru yayi ya rasa me zaice jinin shi ne ya harba a take aka mayar dashi daki saide fa su lokacin basu san wani hawan jini ba.
A takaice de.... daga karshe mai martaba ya sa musu albarka kuma ya karbi kaddarar sa, yarima kabir shima ya karbi kaddarar sa ya bawa nana hakauri yace su fara sabo dukda basa son juna wata rana zasu fara. Asma da aliyu dama ana so ana kaiwa nasuwa ne dan haka aka sa musu rana. Yarima munir kuwa.... ya fado daga bishiyan mangoro ya karya kafa😂
Assalam alaikum
IDAN HAR KUNBI LABARIN NAN HAR ZUWA KARSHE NA GODE TABBAS KAUNA CE KADAI ZAI KAWO HAKA AMMA KAR KU DAMU ZAN TAHO MUKU DA LABARI MAI NA DABAN MAI SUNA (MATAN CANJI) ZAKU JI SANARWA INSHA ALLAH IN HAR NAN DA SATI BAKI GA SANARWAN BA TOH FA BA'AYI MIKI SHARING BANE KI MIN MAGANA TA 08146448881 SAI IN SAKI A GROUP DINA.
NAGODE!
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top