CHAPTER 51

Yarima kuwa shiru shiru yana jiran sarki amma bai dawo ba har ya gaji ya fita yawon neman mai martaba dan har la'asar ta wuce shi kuwa mai martaba yana fita ya shiga kasuwa duk mai saida wani abu kawai dukiya yake ajiye musu yace duk wanda yazo siya abu su bashi kyauta ranan dama haka yake yi ko wani idi har na kwana 3 toh yau da ya samu mai kama da fatin sa ta zama nasa dole ne ya nuna farin cikin sa sai bayan azahar ta gota ya nufi makabarta dake bayan gari yaje yayi wa fatin sa addu'a sosai wanda dama yakan je yayi duk sanda ya samu dama sannan yakai wa kabarin mahaifan sa ma ziyara ya nema musu gafara a wajen Allah.

Bai dawo gida ba sai bayan la'asar sannan ya isa fada nan aka sanar dashi cewa yarima yazo neman sa bayan magrib yarima ya dawo har wata rama ta kama shi bayan anyi isha'i ya biyo mai martaba sarki yana ganin sa yace yaron albarka baka san irin farin cikin da nake ciki ba yau.

Wato ji nake kamar mahaifiyar ka ce ta dawo mun lallai hakuri baya bada mutum, tabbas a wannan karan zanyi iya kokarina na bawa laila gaba daya lokaci na fiye da wanda na bawa fatima saboda kar nayi dana sani. Idan na rasa ta a karo na biyu ban san ya zanyi ba.

Tunowa yarima yayi da labarin da aka bashi cewa ciwon zuciya mai martaba ya afku ne sanadin mutuwar mahaifiyar sa da ba don tawakkali ba da tabbas shima ya bar duniya. Saide har yau abinda aka kasa ganewa shine yanda akayi mahaifiyar yarima ta fado daga doki har ya janyo haihuwar ta lokacin sa bai yi ba.

Dan dariya mai martaba yayi yace kash kaji ni na koma kamar yaro dana kuma yau shine abokin wannan zance? Rike hannun yarima yayi da dan jin kunyar maganan da yayi yace naji ance kana nema na akwai wani magana ne? Yarima be san ya aka yi ba amma sai ya tsinci kansa da fadin dama... dama taya ka murna zanyi.

Shafa kansa mai martaba yayi yace Allah yayi albarka dana yana kaiwa nan ya shige ciki. Yarima kamar an masa duka ya tafi sashin sa ya ma kasa tunani toh me zaice ga matar sa can a dakin mahaifin sa in yayi magana tabbas baya shakku zuciyar mahaifin sa bugawa zaiyi a wajen wani irin hanya zaibi ya baiyana masa ?

Aliyu ne ya taro sa da sauri dan kamar zai fadi tun safe banda ruwa da dabino 3 ba komai a cikin sa. Aliyu ma ifon sa yayi ja kamar zaiyi kuka ganin yanayin abokin sa kuma shugaban sa. Baki na rawa yace aliyu ya zanyi tayaya zan fada masa cewa matata ce ba tare da na kashe sa ba? 

Da sauri aliyu yace ba batun nan ba batun mutuwa yarima da ke son yayi kuka yace wallahi sa gaske yake son ta aliyu yace toh ba sai musa ya dena santa ba ? Tanda kasan aradu da dangwale shi ya mike a take da kyau ya rike hannun aliyu yace allah kar ya nunan ranan rabuwan mu aliyu fada min me kake so inde ina da iko zan baka.

Sosa kai aliyu yayi yace asma nake so yarima yace an gama.... gobe zan tsiri gaida duk matan baba na su biyu ne da kuyan 6 ko? Aliyu yace in banda munira ba? Daidai lokacin sun iso dakin yarima yace banda ita mana matata ce kana ganewa ko? Gobe zanje "duba lafiyar su " daga nan zanga ya bangaren da za'a bawa munira yake yanda zan dinga shiga ta sirri kuma sai mu tattauna yanda zata sa mai martaba ya daina son ta.

Bangaren me martaba kuwa yana shiga wajen munira da kayan dadi iri iri bayi ma sunyi layi a barinsu ana cin dadi  dukda dama suna cin dadi amma na yau na daban ne. A lungun gado ya hango munira dake nade cikin mayafi  sallama yayi ta amsa kasa kasa.

Cikin lallami yace laila fatan kinzo lafiya? Ita kuwa me gaskiya biden bakin ta cewa tayi sun fame min ciwo na tana fashewa da kuka shi kuwa ya dauka shagwaba ce tabbas bata da maraba da fatiman sa. Yace subhanallah ya akayi haka  yana me matsowa dan nuna damuwa. Jan majina tayi tace share su kawai.

Daidai lokacin da ta kalli fuskar ra ne ta tuna cewa fa wannan sarki ne dan haka ya sufce mata na dan dakikai. Dawowa daidai tayi. Dukda cewa muryan sarki da yarima.yana dibi kamarsu yafi bacuwa domin kuwa sarki kamar yarima idan ya tsufa haka zaka ganshi kawai yarima.ya fishi tsayin fuska da kafa sai haske kadan saboda mahaifiyar sa.
Yace toh dare a cikin cikin dare kinyi sallah? A take munira tace bana yi hakan yasa ma ta fara tunani al'adar ta fa ta dan gota lokaci ya kamata zuwa yanzu har yazo ta kusa gamawa ko ta gama ma. Share tunanin tayi jin sarki na fadin kice zaki barni ni kadai kenan.

Tashi yayi ya kabbara dama yana da alwalar sa kuma da ma ko bai san ma bata salla ba shi bai yi niyan taba ta ba domin rashin hankali ne ace dole sai anyi ranan da aka kai amarya sunnah ce ba dole ba idan har matan bata shirya ba hakkin ta ne akan mijin ya jinkirta.

Idan ma ya kagu toh saide a nemi wata hanya bawai ya fara tsoratar da ita da cewa in bata yadda ba mala'iku zasu tsine mata wannan gaskiya amma a dena murda hadisi. Kuma in da gaske tsinuwar ce ta damu mazan ai ba wannan zunubin bane kadai duk macen da ta fita gida zirin gashin ta a waje tana sane sai mala'iku sunkira sunan ta tun daga kakan ta na 8 wato generation 10 sannan su tsine mata. Duk macen da ta fita tana sanye da turare manzon Allah yace mazinaciya ce har sai ta koma gida kuma tayi wankan tsarki.

Kuma 1 daga cikin mutane 3 da manzon Allah yace yan wuta ne wato guarantee sai sunje shine kasiyatun ariyat mata dake fita babu hijab ko an saka hijab amma shara shara ne ko yana like mata. Idan taro zaki sai kisa abaya amma dole ne kar ki daure da igiya ko ki siya wacce ke kama jiki ko baya rufe ko ina sannan basa fadawa mata cewa sa safa dile ne saboda kullu mar'atu aura sai fuska da hannu.

Yanzu duk wannan gwaramar basa fadawa mata amma da yake can su zasu ci riba to sunfi kowa bakin jan hadisi.

WATO SABON LABARIN DA ZAN FARA KO? MUGUN DADI NE DASHI KUMAN KUNSAN BANYI NOVEL IRIN WANDA KUKA SABA GANI NAFI SO NA KAWO MUKU ABINDA BA'A TABA BA. WATO KU JIRA SANARWA KAWAI.

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

miss untichlobanty 💕

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top