CHAPTER 5

Kifi ne yace ni de yanzu ba wannan ba sarauniya bayan anyi tirka tirkan nan fa jin sin ki fa ya fada ruwa ki cire mana shi Dan karnin jini ya dame mu ta sauri ta fada ruwan tare da fadin kaini wajen.

Niki niki ta janyo shi ta fito da shi kamin ta fada gefe tana haki tare da fadin kai wannan katon banza nauyi ne dashi. Yanzu ya ma za'ayi na dauke shi? Kifi ne yayi Mata sigina yana dariya, dariya itama ta fara bayan ta dauki hannu suka fara kallon yimla doki, baya yayi yana girgiza kai ta riko shi caraf cikin sauri tace idan ka dauka min shi zan maida kai Dan daki na.

Cikin kunkuni yace sai kace nace ina son zama Dan dakin ki... tace me kace? Yace cewa nayi kaf zamanin nan babu ya ni Dan haka sai kinyi min alkawari bazaki sayar ni ba. Tace toh ni kaga ina hulda da mutane ne?

Daura masa tayi suka kama hanya suna neman hanyan gidan ta Dan bata taba zuwa nan ba. Dokin yace Anya kuwa kinsan hanyan gidan ki? Tace kai ba inda ban sani ba a jejin nan. Tafiya suke, yanzu ne anjima ne yace ke me magana da halittu nifa na gaji kinsan hanyar nan kuwa ? Tace yanzu mu tsaya anan na duba wannan mutumin kar ya mutu.

Sauke shi tayi tace kai wallahi in katon nan ya kuskura yaki gode min da hannuna zan kashe shi mtsww sai kace me cin duwatsu. Wasu abubuwan ta tayi ta duddura masa magani tare da daure masa kai da tsumma Wanda duk cikin jakanta take yawo da su. Allura ta ciro ta tsittsikara masa numfashi ya ja da karfi tare da furzar da ruwa a hankali a hankali ya bude idon sa. Yana mai tari tare da furzar da ruwa.

Hada ido sukayi yana mai kokarin zama, hannu tasa zata taimaka masa da sauri ya bige yana me dafe saitin kirjinsa. A tsorace ta ja baya tana mai bata rai. Yace wacece ke? Da ido kawai take kallon sa. Yace me nake yi a nan? Gwagulatu tayi masa Wanda ke nufin ji wani maganar banza.

Dariya yimla yayi yace halin Dan mutum yayinda matashin ya furzar da iska saboda haushin da suka fara bashi Dan be gane ko Abu daya da suke fada ba. Mikewa yayi han lokacin hannun sa na kan kirjinsa zai fara tafiya amma jiri ya kwashe sa. Hakan ya fadi rabas. Cikin borin kunya da hade rai yace ba faduwa nayi ba Tuntube nayi.

Ita de da ido take binsa Dan tasan ko tayi masa magana aikin banza ne kalmomin da ta iya ba wani yawa garesu ba. Daga toh, hakuri, eh, ah ah sai nagode.
Shi kuwa matashin tunani yake wannan daga ganin ta kasan dariyar daji ce saide ni bana tuna komai ban ma San inda na fito ba. Amma dai dokin nan daga gani nawa ne saboda kyawun sa.

Kokarin hawa yayi yimla yace baisan zancen ba. Amma da shike yasan sirrin doki sanda yayi yanda yayi yimla ya fara tafiya da gudu ta biyo su tana ta gagulatun ta inda take fadin kai mara mutunci Wanda be San abin arziki ba. Ka bani doki na da ma ban taimaka ma ba. Ka tsaya nace!

Har kusan tafiyan kaso 1 cikin 6 na sa'a sukayi wato minti Goma amma yaga ko gezau bata yi ba sai ma karfin da take kara yi. Gashi kafanta ko takalmi babu duk tabi ta taka kayoyi yana jini tsayawa yayi ganin haka sannan ya sauko daga dokin ya fara jansa suna tafiya a kafa. Yimla cikin haki yace ba kika ce ke ce me mulkan dakin nan ba? Ki sa wani maciji ya sare mana shi mana.

Tace ai tunda ya bani wahala sai yayi min aikin bauta tukun barshi mu koma cikin ahali na. Hamma yimla yayi yace ni de yunwa nake ji. Matsowa tayi kusa da shi ta warce linzamin yimla da ke hannunshi sannan ta tsaya domin yaci abinci.

Kallonta kawai yake yi da sauri ya dauke kansa saboda zafin da ya sake ji a kirjin sa ya rintse idanu. Ita kuwa shafa yimla tayi tace mu tafi. Yimla yace ba mu tafi ba kinga yamma ya soma kawo kai kinde San hanya ko? Tace na sani mana na sani kaide muje.

Tafiya suka fara yi su uku matashin yace wai ke kurma ce ko kuwa Dan ki bani haushi ne? Dauke kai tayi kamar bata jishi, shima dauke kai tayi Dan yaga yarinyar da rainin wayo tazo masa.

Can de tayi ajiyan zuciya tace yimla na bada gari gaskiya ban gane hanya ba. Wani birki ya ja cikin korafi yace da kinyi magana ai da kinyi magana ni gaskiya na gaji kinga daga nan ba inda zan motsa. Rissinawa yayi ya kwanta abin sa, turo baki tayi ta tsuguna tace yimla karka bani kunya mana kaga wannan halittar yana kallon mu kar aji kanmu,  juyar da kai yimla yayi ya gutsiri ciyawar sa.

Furzar da iska tayi matashin yace ke nifa kun fita daga kaina zanyi nan ke kiyi nan kar mu sake haduwa. Cikin bacin rai ta tashi ta handeshi tare da fadin da ni nace ka biyo ni? Yimla yace kinsan ba gane me kike cewa take ba ni duk kin hana ni bacci. Shurin yimlan tayi da kafa tace kaima ka tafi bana sonka.

Yace jimin matar nan alkawarin da kika yi min kenan? Cikin tsawa yace kai ka sani tayi gaba abin ta. Shima matashin nan gaba yayi bayan ya dauki yimla. Leke leke ta fara Dan ta fara jin tsoro amma dai bata koma ba.

Wasu kwarangwal ta gani a zuzzube har sanda cikin ta ya bada sauti motsi taji a bayan ta AI kuwa ta zunduma da gudu inda ta tsinci kanta a cikin wani kogo. Lungu ta samu ta fiskanta ta dukun kune saboda sanyi. Tace Allah na gaskiya ka kare ni daga sharrin ranan daji kar su cinye ni. A haka har bacci ya kwasheta.

Shi kuwa matashin nan Wanda zuwa yanzu nasan wasu sun fara harshen yarima ne toh shine. Tunda ya juya ya nufi arewa yana tsintar itatuwa da yaayi saboda ajiye zango. Wani kogo ya kalla yace hakan yasa a kofar kogon ya kunna wuta. Zomon da ya farauto ya gasa shida yimla suka sha dimi kamin suka shiga ciki suka kwanta bayan sun tabbatar babu wani Abu me illa a ciki.

Wani dutse yarima ya gani a gefe hakan yasa yayi matashin kai da shi yana kokarin tuno waye shi kuma daga ina yake? Ji take akwai abinda ya dace yayi amma baisan menene ba. Ashe sallah ne baiyi ba shiyasa abin ke damun sa.

Daidai lokacin sallar asuba ya bude ido saide babu abinda zaiyi. Motsi Morsi yahe anayi a kasan sa da sauri ya tashi ya zauna. Dutsen da yi matashin kai ne ke motsin hakan yasa ya dauka ko akan damusa ya kwanta. Takwabin da ke kunkumin sa ya zaro. Ware wa tayi daga dukunkunen da tayi tare da mika saide a zabure ta Mike tare da daukan dutse zata jefa Dan a tunanin ta arnan daji ne.

Da yatsa ta nuna shi tare da fadin eyi wato kai? Shima yace ke? Ba nace kiyi kudi nayi arewa ba? Murkude baki tayi tare da nufin wajen kogon. Wani sanyi ne ya bugo ta bata San sanda tayi baya ba. Tuntube tayi yimla ta fada bayan yarima Wanda ya durkusa yana kokarin daukar guntun zomon sa na jiya Dan mugun yunwa yake ji.

Bugawa kirjinsa yayi a take ya dafe saboda zafin da ya sake yi masa.....

TOH FA GA YARIMA GA MUTUNIYAR KU, WAI YA ABUN ZAI KASANCE NE? ZANSU KOMA GIDA KO KUWA? PLEASE AYI COMMENTS, VOTING SANNAN KAR A MANTA DA SHARING.

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top