CHAPTER 49
Sarki yace me ke faruwa ne? Akace wata baiwa ce ta sha gaban mu. Yace tasha gaban mu kuma? Ko tana da wani magana ne ku ce ta karaso. Yana zaune yaji ance mai martaba gani yace lafiya kika sha gaban mu yana dago da kansa daidai sanda yake ida tamabayar. Kafar munira har rawa yake tana bude baki zata yi magana sai ta fashe da kuka dukda kuwa ba haka taso ba tace kaza nake nema ban lura na sha gaban ku ba a yafe min mai martaba ayi min afuwa.
Sarki kuwa dai bai ma jin me take cewa yace FATIMA.
Miko hannu yayi zai taba fuskan ta taja baya tana goge hawayen ta. Nutsuwa yayi ya kalli waziri shin ko shima yana ganin me yake gani. Murmushi kawai waziri yayi sarki yayi masa rada cewa ya sa wani bafade ya nema mata kazan dan yaga suna yin latti shi kuma tafiya zai ya kamata su fita daga gari da wuri.
Ko da suka fita daga kofan gari matsowa sarki yayi kusa da waziri murmushin fuskan sa na kara fadada yace waziri waziri kunya ne ma ya kamashi ganin sarkin nasu ya koma matashi. Sarki yace waziri kallonshi waziri yayi sarki yace wannan yarinyar bata yi maka kama da fatima na ba?
Kallon gefe waziri yayi yace mai martaba suna dibi sosai saide fatima ta fita haske.
HOTAN FATIMA MAMAN YARIMA UMAR
HOTAN MUNIRA / LAILA
(Ga masu karatu a WhatsApp da Facebook zaku iya ganin hotan a wattpad)
Sarki yace hakane hakane yaushe aka kawo ta ? Waziri yace a cikin bayin shekaran nan tazo mai martaba yace me yasa ban ganta ba? Me ya hana ta zuwa? Girgiza kai waziri yayi cewa bai sani ba. Shiru sarki yayi can yace mai zaka ce idan nace zan aure ta? Waziri yace mai martaba bani da hakkin saka baki a cikin iyalin ka. Murmushi yayi yace ai ni nake tambayan ka.
Waziri yace mai martaba ina ganin ka fara mayar da ita kwarkwara bayan shekara sai ka aure ta saboda gudun hassada kar a cutar da ita. Jinjina kai sarki yayi yace shiyasa na nemi shawaranka. Da badan rayuwar jama'a tana da anfani ba da na daga tafiyan nan. Dan dariya kawai waziri yayi shima sarki sanda ya dara hakan yasa wasu daga cikin fadawa wanda suka baza kunnuwa murmusawa dan sun dade basu ga sarkin su yana annashuwan irin haka ba. Idon sa har kyalli yake yi.
.......
A bangaren su yarima kuwa takowa kabor yayi ya tsaya dab da fuskan yarima umar yace dan kanina idan kana son zaman lafiya ya zama dole ka bani yarinyar nan. Yarima yace idan naki fa? Juyawa yarima kabir yayi sanda yake bakin kofa yace sai muyi takun saka takowa yarima yayi ya dafa kafadan sa yace a bawa yarinya zabi.
Munira kuwa tunda aka danka mata kazar ta bata nufi ko ina ba sai inda suka rabe da kawayen ta suma sun taho hanyar da tabi dan basu ga kazar ba ganin kazar a hannun munira yasa suka washe hakwara tare da fadin kin samo ta. Munira tace kaza ne ba mutum ba. Nana tace ban gane ba asma tace kince an samo TA. Karban kazan nana tayi tace eh baku ganta ba yan mata ce fa.
Dariya suka fashe dashi sannan suka koma bangaren nana can wajen la'asar munira tace muje mu gaida sarauniya shiryawa suka yi suka shiga kansu tsaye ba'a tsayar dasu ba tunda suna tare da nana kuma kowa yasan matar yarima kabir ce.
Gaishe da sarauniya sukayi ta amsa tama kallon munira kwanan ta nawa da tafiya har ta fara yin kumatu. Taso ta kebe da ita ta fara kulla mata amma wani abu yace kar tayi gajen hakuri ta bari su kara kusanci tukunna.
Suna shirin tafiya a hanya suka hadu ds gimbiya hauwa bangaje kafadar nana sai kace kishiyar ta ce. Munira cikin ba'a tace wasu de kamar ba jinin sarauta ba sai a dauka tsintar su aka yi. Da sauri ta juyo amma sai tayi ajiyan zuciya tayi murmushi tace ko ba komai yar tsintuwan ta iya magana irin na mutane. Munira zata amsa ta asma tayi caraf tace wa gimbiya wanda bai iya magana ba yafi mai bakin maciji da ta bude dafi ke fitowa.
Nana ta ma riga ta fice abinta. Sallama suka ui wa juna kowa ya tafi muhallin sa rayuwa kenan sun shigo a baki bangare daya na bayi dukannsu amma sun zo sun wuce wanda suka sama wato asma in wasu ne hassada ne zai kama su sai de a ko wani bangare na rayuwar su tana tare da su.
Bayan magrib yarima ya dawo munira tana daki lantana tana koya mata saka (lanatana itace yarinyar da ta fadawa nana an daura auren ta kuma itace ce baiwar da aka bata) hamma munira tayi tace kai ni gaskiya wahala ne dashi gashi sanyi daf damu yake zuwa yanzu ko hular sanyi ne na sakawa yar..... shiru tayi a zuciya ta karashe _yarima na._
Lantana tace kar ki damu zaki koya ai bari na koma wajen uwar daki na. Nan dai suka rabu haniniyan dokin da munira take ji da gaishe gaishe ya tabbatar mata yarima ya dawo dan haka ta fito da gudu tana dariya tace yarima yarima ladidi da ke washe baki wa yarima a take ta hade rai ganin munira ta juya ta koma daki.
Yarima ne ya kalli aliyu yace ka raba musu ko. Aliyu ya amsa da toh. Tare da sanar da su a hau layi lokacin fadawa sun gama kunna aci balbal. Dan haka aka dauko warakan biyan albashi. Haka yake a fadan saboda adalci har bayi ana biyan su albashi sannan duk ranan asabar na satin karshe a wata ana bari su tafi kasuwa don siyan abinda suke so.
Rike hannun munira yayi yana lakace mata hanci suka nufi sashin sa yana fadin menene yasa habibiya ta farinciki. Murmushin ta ne ya fadada tace dama yau na fara koyan saka ne shine nake so na nuna ma ya ka gani? Shafa kanta yayi yace yayi kyau yan mata na.
Kinci abinci ne yan mata tace ah ah kai nake jira. abincin su ta dauko ta kawo suka fara ci suna hira bayan sun kammala tace kanaso in koya ma? Ya ce me kike magana akai tace sakan nake nufi. Duk yasan bazai iya koya ba saboda tai farin ciki yace eh cikin farin ciki ta mike ta dawo kusa dashi zata zauna. Da sauri ya zaunar da ita a cinyar sa, cire dan kwalim kanta yayi amma bata ma lura ba.
Saboda hankalin ta yana kan sakan da take ta bayani, ita da take yar koyo karfin hali wai zata koyar. Can bayan kamar dakika goma yarima yace yan mata ba tare da ta kalle shi ba tace na'am yace bacci nake ji ki dumama min gado na da sauri ta mike ta tsaya tace ban yarda ba. Ashe surutun banza nake ta yi tun dazu na dauka ma kana jina.
Yace toh shikenan bara na dumama abina hawa yayi ya kwanta lekan shi ta tsaya take yi tace da gaske wai kayi bacci bai kula ta ba kuma dama idan shi a rufe. Matsowa tayi ta leka fuskan sa taga idon sa a rufe tace da sauri haka, kara tayi jin an janyota rufe bakin ta yayi da nasa, ta zare ido kamar mujiya.
Yace za ki kurmanta ni itakam ta kasa magana tayi lunkui kamar jaririyar kulya. Ba wanda yayi magan can yace farillan sallah guda bawa ne? Ruf da ciki tayi tace guda......
KU BIYONI A CHAPTER NA GABA TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top