CHAPTER 48
Da fara'a yarima yace ya girme ni ai yana saukowa daga gadon tare da saka riga. Ba tare da ya daure ba dan haka kirjin ahi duk a waje yazo kusa da ita tana jan baya. Sanda suka kai bakin kofa yace ke bakya jin kunya ne? Dan sosa kai tayi tace ya kamata na nuna naji kunya? Da ka ganta kasan kanta ya cushe. A kunnen ta yace kin kara birgeni.
.......
Yarima kabir ne yayi sallama tare da shigowa bangaren yarima umar bisa ga gaiyata ko nace kira da yarima umar din yayi masa domin su tattauna abu me mahimmanci kamar yanda aka sanar masa. Ko da ya shiga fuska a hade takaici ya tsaya masa ya ma rasa yanda zaiyi da nanan da ke bangaren sa shi de yasan ba ita yake nema ba. Toh kode dagaske wancan din aljana ce?
Jin muryar aliyu yana sanar dashi ya shiga a karo na biyar ne yasa ya dawo daga nazarin da yake yi tare da shiga. Zama yayi ya kara hade rai ya kalli yarima gyara zama yarima yayi tare da masa nunin abun sha dake gaban su yayi da yake kurban nasa.
Cigaba da kallon sa yarima kabir yayi ba tare da ya kula bismillah da aka masa ba. Yarima umar yace bazan bata maka lokaci ba batun matar ka da ka aura ban san dalilin ka na auren ta ba amma kuwa dukkan alamu ya nuna bata son ka kuma na sani ka sani haramun ne yiwa mace auren dole.
Bude baki yarima kabir yayi yace ban dai san sanda muka fara shiga rayuwar juna ba saide kuma wanda na aura ba itace wacce nake so ba. Ban san me ya faru ba amma dole ne a nemo min nana. Budan bakin yarima zaiyi magana ya jiyo ana shigowa barin sa da gudu wannan dabi'a ce da ba'a saba ba. Dan haka ya dauka ko wani sako ne me mahimmanci za'a isar.
Kallon kofa sukayi dukan su biyu sai ga mutuniyar ta shigo tare da fadin ban bar dan kunnena anan ba? Bata tsaya damuwa da kallon su ba ta dale gadon tana dube dube a tunanin ta aliyu ne.
A hankali yarima ya mike yazo gefen ta yace muna magana da yaya na ki koma daki zan duba miki kinji da sauri ta waiga jin wanda ke dakin ai kuwa suka hada ido da yarima kabir wanda ya daskare a inda yake zaune kamar an like shi da super glue.
Farat daya kuma ya zabura ya mike ya da sauri yace gatanan haba nide nasan akwai wani abu a kasa umar wato kaine ka boye ta ko? Kallon ta yarima umar yayi alamun kin fahimci me yake fada.
Dukda munira tasan ita ta janyo duk abinda ya faru dawowa gaban yarima tayi domin ya tare ta ta turo baki tace eh naji din na maka karya ba sunana nana ba sunana laila , nana yar uwa ta ce yanzu da ni dince karfi da yaji zaka min? Wallahi ka sakar min nana na dukda saki abu ne me muni dole kayi ta can ka karata bazamu auri mutum me mugun hali irin nake ba.
Uarima ne ya dan bubbuga kafadan ta yace ki tafi wajen asma kuje ku duba nana zan yi magana dashi gwaliyo tayi wa kabir ta bata rai tayi waje abin ta.
Nan fa yarima umar ya rufe kofa sanda gaban aliyu wanda ke waje ya fadi dama yaga yanda munira ta fito rai a turbune. Kallonshi tayi tace kace wa matar ka mu hadu a wajen nana ni na tafi can yace toh a dawo lafiya shugaba ta.
Ko da ta isa bangaren nana da wata baiwa tana binta a baya da wani abu a rufe daga gani kyauta ce ta kawo wa nana. Suna shiga ta samu nana a bakin gado tana zaune tana ta goge hawaye da sauri munira ta karasa wajen ta rungume juna sukayi cikin damuwa munira tace kar ki ce min cin zalin ki yayi? Girgiza kai nana tayi munira tayi ajiyan zuciya tace zo kiga me na kawo miki maza sa hijabin ki fitowa sukayi
Munira tace wa nana bude nana tana budewa ta daka tsalle dan tsabar jin dadi kaza ce a cikin keji ba abinda nana ke so kamar kaza in kuwa kana son kaga bakin ta a washe to tayi mota dashi. Ai kuwa da igiyar sa an daura a jikin sa yanda ba zai ji masa ciwo ba zunguran kazan nana tayi suka fita da gudu suna ta kewaya wajen sai dariya take munira tace nikam me abun dadi a nan wai? Nana ta mika mata igiyan tace gwada ki gani fara gudu sukayi da munira amma me kazan ka fa sai ya nufi kofa ya fice saboda asma da ta bude take shigowa a lokacin nana tace asma ki tare amma ina ya zille juyawa tayi suma suka fice suka bai kazan da gudu saide ina yayi wani kwanan.
Dan haka suka rabu kowa ya kama wani hanya neman kazan munira tace ita zata bi hanya waje a ranta kuwa so take ta dubo su zul dinta. Dukda yarima yasa an musu daki ana kai musu abinci ta dade bata gansu ba.
Tana tafiya tana maimaita haddar ta saide aya daya fa ya makale dan haka ta lula can bata an kare ba tsawan da wani bafade ya daka mata ne yasa ta dawo dai dai. Sai lokacin ta lura kowa ya tsaya da tafiya an buda wa sarki hanya domin zaiyi tafiya ita kuma tana gaban tawagar su.
Sarki yace me ke faruwa ne? Akace wata baiwa ce ta sha gaban mu. Yace tasha gaban mu kuma? Ko tana da wani magana ne ku ce ta karaso. Yana zaune yaji ance mai martaba gani yace lafiya kika sha gaban mu yana dago da kansa daidai sanda yake ida tamabayar. Kafar munira har rawa yake tana bude baki zata yi magana sai ta fashe da kuka dukda kuwa ba haka taso ba tace kaza nake nema ban lura na sha ganan ku ba a yafe min mai martaba ayi min afuwa.
Sarki kuwa dai bai ma jin me take cewa yace FATIMA.
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
miss untichlobanty 💕
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top