CHAPTER 45

Sake fadin waye tayi amma shiru dan haka ta lalumo wukan ta ta rike tana budewa yayi saurin rike hannun tare da daukota yaje ya ajiyeta a bakin gado. Komawa yayi ya rufe kofa kamin ya dawo ya zauna a gefen ta.......

Kallon shi ta tsaya yi yayin da ya zauna kawai baice komai ba kuma bai taba komai ba. Can munira idan ba wani magana ni zanyi bacci ka koma bangaren ka. Tana kaiwa nan ta kara dalewa tsakiyar gado. Riko hannun ta yarima yayi yace na kasa bacci tace toh zata sake kwaciya ya ce ki sosa min kai.

Kallon shi tayi kamin tace kawo kan matsowa yayi tace ka min tsayi da mamakin ta kawai taga mutum ya dauraata kai a cinya tsaki tayi kawai ta fara sosa masa kan can ta dauka yayi bacci har ta fara gyangyadi taji yace nagode bata amsa ba taci gaba da sosawa tana nazarin da in akace ta fadi me take tunani itama ta manta(wai dan Allah ni daya ce me nazarin babu ko dai wasu ma sunayi? Ku fada min a comment section)

Jin shirun yayi yawa yarima yace ki bani labari tace me zan fada ma. Yace kawayen ki aikuwa cikin zumudi ta fara basa labarin su nana da asma da shiriritar da suke yi saide tana boye wasu abubuwan maimakon tayi masa karya domin tasan nauyin karya da gulma a musulunci.

Sabanin yanda mutanen mu yanzu suka mayar da abubuwa biyun nan jiki. Bazai ma yuwu ace sun wayi gari har su kwanta basu yi ba ko a sani ko cikin rashin sani. Saide abinda basu sani ba shine gulma yana daya daga cikin manyan zunubai Allah ya kwatantashi a matsayin cin naman mutum cikin suratul hujrat (surah 49 ayah na 12):

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اجْتَنِبُوا كَثِيرًا مِّنَ الظَّنِّ إِنَّ بَعْضَ الظَّنِّ إِثْمٌ وَلا تَجَسَّسُوا وَلا يَغْتَب بَّعْضُكُم بَعْضًا أَيُحِبُّ أَحَدُكُمْ أَن يَأْكُلَ لَحْمَ أَخِيهِ مَيْتًا فَكَرِهْتُمُوهُ وَاتَّقُوا اللَّهَ إِنَّ اللَّهَ تَوَّابٌ رَّحِيمٌ

ma'ana ya ku wanda kuka yi imani ku guji yin zato (akan yan uwan ku ) domin shi zato a karan kansa zunubi ne, kuma kar ku dinga leken asirin yan uwanku (wato shisshigi da neman aibin wani) kuma KAR KUYI GULMA, SHIN DAYA DAGA CIKIN KU YANA SON YACI NAMAN DAN UWAN SA DA YA MUTU NE?  TABBAS KUN KYAMACI HAKAN. TABBAS ALLAH ME KARBAN TUBA NE ME RAHAMA."

(Lallai ya zama dole ne ku iya bakin ku masu karatu asan me za'a dinga fadi kar hira tayi dadi ayi ta shafci fadi. Irin shafci fadin nan ne ya janyoa aka yiwa maman mu nana aisha kazafin zina. A kiyaye harshe a gyara zuciya ayi anfani da LOKACI mutuwa bata bada notice.)

Haka har tayi bacci ta bingire lokacin yarima ya dade da yin bacci. Washe gari assalatu ya tashi yarima yana bude ido ya ganshi ba inda ya saba kwanciya ba sanda ya dauki yan sakanni komai ya dawo masa waigawa yayi aikuwa yaga fuskan munira 'kiu tana kallonsa dukda akwance takawai kanta ta dago. Ganin gasan kallon ba zai kare ba yasa tace kafa na. Da sauri ya tashi ya zauna tare da dan sosa kai yace ni zanje nayi sallah tace tom bayan ya fita ma zama tayi har saida kafanta ya daina mata zafi jini ya bi ya koma aka daura auren kabir da nana yarima umar ya danyi mamaki dan sam mahaifin sa bai sanar dashi komai a kai ba amma dai sai ya dauke kai.

Wajajen hantsi asma na wanki nana tana wanke wanke suna hirar in sun sami lokaci zuwa yanma su kaiwa munira ziyara wata baiwa ce ta shigo da gudu me suna lantana tana haki har sanda ta tsinkawa mutane dayawa zuciya. A gaban nana ta tsaya nana ta mike da sauri tana fadin me ya faru dan tasan anzo an tambayi sunanta dama a tsarge take karde siyar ta za'ayi? Wannan tunanin ne yasa nana neman takalmi ta fara kuka zata tafi wajen munira ayi wani abu kar a rabata da uwar dakin ta.

Lantana ta rike hannun ta tace nana nana ..... yanzu yanzu naji sabo da habu suna hira wai an daura auren...aurenki.

Asma tace mene? Kayan da take kokarin shanyawa ta saka ba tare da ta damu ko zaiyi datti ya mayar mata aiki baya ba. Zuwa tayi ta dafa nana tace maza mu tafi mu samu laila kawai ta nufi wata kofa kamin ta juyo a rikice ta ma manta hanyar dakin su kai kace ita aka daurawa auren. Nana ko banda idonta ba abinda ke motsi a jikin ta.

Rokon Allah take ayi kiran sallahr asuba dan ta tashi daga mafarkin da take yi tome ma ake nufi da an mata aure ? Kamar ya? Sai kace wasan yara? Aure shirme ne da kowa zai dinga aiki dashi bai lura da me yake cewa? Kawai gani akayi ta juya ta fita da gudu tayi hanyar waje asma dake fitowa a daki tama gyara hijabin ta da ta nada. Janyo mayafi tayi ba tare da damuwa ko na waye ba tabi bayan nana da gudu domin ta suturta ta.

Munira tana waje tana duba masu aiki a madafa tare da tamabayan su ko akwai abinda suke bukata suka amsa da babu sai kalle kalle take tana koyan yadda suke dafa abincin su kuwa sai kiya mata suke don sun karbi kaddara yanzu tafi karfin su da shugabar su ma.

Nana da ta gani a tsaye ta kafe ta da ido kamar gawa sanda ta danyi tsalle saboda yadda ta tsorata. Tace bismillah nana ya haka kamar aljana kinzo kin kafe ni da ido? Fadawa kirjin ta nana tayi saboda munira da asma sun fita tsayi asma duk ta fisu dan ta dan fi aliyu tsayi ma dukda shi ba gajere bane nana kuwa baza'a ce mata wada ba amma gajeruwa ce.

Kuka ta fashe dashi tace bana son na rabu dake uwar daki na. Munira shafa kan nana take itama tana shirin yin kuka dan ta dauka laifi nana tayi za'a kashe ta tace me ya faru nana na? Ko me kika yi kar ki damu zan yi wa yarima magana yasa baki bazaki rabu dani ba baza'a kashe ki ba nana cikin shessheka da haki tace aure aka min fitar dani za'ayi daga fadan.

Wani hura hanci munira tayi tace wasan banza kenan wa zai miki aure ba da sani na ba? Ince ke mallaki na ce. Munira ta fada cike da mantawa cewa yanzu a zaman bayi suke dukan su biyu.

Finciko hannun ta munira tayi tace zo muje bangaren karatun yarima ta nufa dukda ko mata basa shiga sai da izinin sa tare ta dogarai zasuyi aliyu ya tsawatar musu yana me yiwa munira iso bata ma bi ta kansa ba ta fada ciki ta samu yarima ya dawo yana karatu saide ba wannan ne a gaban ta ba.

Zaman dirshen tayi a gefen sa duk bacin rai da kurarin da ke fuskan ta a take ya sauya da abin tausayi 😢kamar yarinya ba kunya ta bare baki😫 harda rike bakin rigansa tuni hawaye ya fara zuba tace RURU za'a tafi min da nana naaaa😭 kar ka bari a tafi min da ita dan Allah ka dawo da ita nan.

Ajiye littafin yayi fuskarsa dauke da mamaki da damuwa tare da rashin fahimta yace me ya faru? Sallama suka ji kamin suyi magana ayi yace bayin yarima kabir ne ranka shi dade. Yarima yace me ya kawo su? Bayan aliyu ya tambaya suka sanar dashi. Muryan asma aka jiyo tana fadin wallahi bazaku tafi da ita ba. Shigowa tayi itama saide sauran matan har yanzu suna waje aliyu yace shugabana wai sunzo daukan amarya ne. Zasu je a shirya ta da la'asar za'a yi walima ta maza daban mata a bangaren sarauniya bayan magriba za'a kaita turaka.
Asma tace ku da turankan ub*n ku. Kukan takaici yana sufce mata. Yayin da wani bafaden yarima kabir ya daga hannu ya dauke ta da mari.

ZAN DINGA YI MUKU UPDATE SAU 3 A SATI INSHA ALLAH HAKAN BAZAI TAKURI KARATU NA BA KUMA KUMA BAZAN BARKU SHIRU. NAGODE SOSAI DA HAKURIN DA KUKE YI DANI ALLAH YA BAR MU TARE

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top