CHAPTER 43
A fili kuwa yace banda yau din dai yamma tayi gobe in munyi sallahn asuba sai a daura menene cikakken sunan ta? Yarima kabir yace zan aiko a fada maka abba yana kaiwa nan yayi godiya ya fita direct bangaren shi ya nufa ya aiko mukarrbain shi wato kamal zuwa bangaren bayi yace a tambayo masa sunan nana. Yayin da ya saka bayin sa mata suka fara dibo masa kayaiyaki masu kyau daidai gwargwado tunda yasan nanan baiwa ce bata da kayaiyaki sosai.
Ko da bawan sa kamal yaje sallama yayi aka bashi izinin shiga yace wacece nana? Bayi shida ne suka nuna ta yayin da asma ta dafa kafadan nana tace me ya faru kamalu ? Kamal yace sunan nana na hakika nake nema asma tace ga ka ga ta nana tace sunanan nana a'ishata abdullahi godiya kamal yayi ya juya kowa in ya kalli junan sa alamun kinsan me ke faruwa sai su girgiza kai komawa bakin aikin su sukayi yayin da kamal ya sanar da shugaban sa kabir usilin sunan nana.
Da daddare ali yana zaune yana cin abinci munir yazo zama yayi a gefen sa aliyu yace yariman yana ciki ka san san da son cin littafi dariya munir yayi yace wajen ka nazo. Aliyu yace in nama na kazo roka bazan baka ba fa yauwa. Dariya munir yayi yace ni fa yarima ne ko ka manta ne dawo da kwanon sa daidai yayi yace kuma fa haka ne dadin abinci ne yasa na mance me ya kawoka toh? Munir ya matso kusa da shi tare da rage murya yace na dai san zuwa yanzu ka fahimci baban takarda yana son kanwata ko? Aliyu ya gyada kai munir yace toh yauwa abu mai sauki nake son ka taimaka min a bayan gari ta gabas ba ta arewa inda kuke zuwa ba akeai wata rijiya toh yau abin da mukayi munje mun duba ba macizai da makamantan su lafiya lafiya.
Aliyu yace kai ni kana bata min lokaci yi bayani mana dan samari munir yace ka taho da yarima ni kuma zan taho da kanwata sai mu saka su a rijiyar su kwana hakan zai kara dankon kauna tsakanin su. Aliyu yace toh amma ai basuda aure nake ga hakan bai dace ba. Munir yace ka manta ita baiwar yarima ce, ta hannun daman sa ce? Abinda ya mallaka ce.
Aliyu yace kuma haka ne fa ashe de wani zubin kana da tunani toh an gama mu hade kawai musabaha sukayi munir ya tafi sai dadi yake ji.
Washe gari kamar yadda suka shirya bayan sallar azahar aliyu yace wa munir suje shan iska shima munir yace wa munira ta raka shi zaije leken asiri yana zargin wasu na kokarin kashe yarima. Ba bata lokaci taje ta nemo asma don ta rakata tunda taji yace wajen gari zasu ai kuwa ko da su yarima suka isa aliyu yace shugaba naji ance a rijiyar nan akwai wani ruwa me zaki duk daular nan babu ya ita amma sai ta bushe saide har yau idan ka sunsuna zaka ji sansanon ta.
Yarima yace haba aliyu yace sosai ma bari muga tsugunawa aliyu yayi ya sunsuna kamar da gaske yace tabbas tana da sansano na sanshi kuma ban sanshi ba yarima yace muji yana zuwa bakin ta aliyu ya hankada sa kadan tare da fadin zaka zame ai kuwa yarima ya tsinci kansa a rijiya yaga ba tautau ba komai har karen miski aka shimfida a kasa da randa sagowa yayi ya kalli sama da nufin yiwa aliyu magana yana hade rai yace kai me haka banason irin wannanwasan me hakan ? Ko sake maka duskan da nake yi ne. Aliyu yace kayi hakuri shugaba na kamin ya buya bayan bishiya. Can ya hango su munira yayi sauri zuwa ya taro su ya fara bin asma ya raba mata hankali munir yacewa munira muje in ta hadu da mutumin ta kamin su gama sai mu bata sa'a daya.
Munira da bata maida hankali ba dukda abin da tayi da hatsari dan haka ta bishi igiya ya daura yace zaki fara shiga ne ba san sanda ta dira ciki ba ita wannan ba yau farau ba aikuwa taji ta tim aka mutum tashi tayi ra kade jikin ta tare da kallon munir tace ka shigo ma... tsayawa tayi da magana lokacin da kwakwalwar ta ya tuna mata aka wani ta fado bismillah tayi ta daka wani kara har sanda wasu tsintsaye suka fure damke mata baki yarima yayi ta fincike jikin ta ta gurde kafanta sai lokacin taga shine dagowa tayi ta kalli munir tace munir? Shiru kai munir shiru igiyar da ta hawo dashi ma ya janye.
Yarima yace me hakan ke nufi tace me ko hakan ke nufi da irin maganar ta yarima yace "me ko akan ce ufi?" Waje ya samu ya zauna ita ma zama tayi tace ya zamuyi ? Bata mishi rai maganar tayi yace yunwa ce zata kashe mu da sauri ta mike ta fara ihu ku taimake mu amma shiru asmi kuwa ko da ta tambayi munira akace tana wajen yarima bata zargi komai ba tunda taga aliyu tasan duk inda yarim yake suna tare munir yace yarima yace su tafi zasu dawo tare tace to a wani waje suke ban lura da sanda kuka tafi ba munir yace zan fada miki a hanya daga nan yayi gaba ya kyaleta ta biyo su da sauri dan tana tsoran maciji.
Can bayan la'asar wasu masu tsinkan magani suka jiyo sautin su nan suka kawo musu agaji mujira tana dinigishi tayi kokarin hawa igiya amma ta fado tsaki yarima yayi kamar yar tsana ya daurata a bayanshi kawai ya kama igiyan ya fito da su wani hadiri ya hadu sosai munira tace la na dauja har anshiga sanyi kusan sati 3 ba'ayi ruwa ba kan ta karashe magana aka kece da ruwa sisin gwal guda yarima ya bawa mutanen nan wanda sun zo ne daga wani kauye ya dale dokin sa dan shi a doki yazo yace wa munira kama ni tace na'am haniya dokin sa tayi saboda jan linzamin da yayi ba shiri munira ta damke shi suka fita a guje cikin ruwa iska yana cika musu kofan hanci.
A FUWAN KWANA BIYU KUN JINI SHIRU WANI GASA NAKE SON NA SHIGA KUMA ZAN BUKACI VOTES DINKU INSHA ALLAH FATAN ZAKU NUNA MIN KAUNA
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top