CHAPTER 40

DEDICATED TO AsmeebashBashir SaniHauwa

Tsaki tayi tace da na bari kaji karfe kadan kila da ka gode min. Kar fa ka batamin rai kasa na nemi saki. Mujir ne ya karaso ya mika mata dokin ta yana mata sannu sannan ya karasa fada itama kwafa tayi taci gaba da takawa sudai fadawa nasu ido ne kowa yazo ya wuce sai sugan shi da jini.

Washe gari yarima munir ya samu yarima umar. Daga ganin fuskan sa yarima yasan da abin da ya kawo sa dan haka yace menene? Hade rai munir ya sake yi yace yanzu kai abinda kayi ka kyauta. Kallon shi ta gefen ido yarima yayi kamin ya rufe idon baki daya yace me kuma nayi idan aron samir ne bazan baza ba kaga jiya ma ya tsorata.

Munir yace abinda ya kawo ni kenan yanzu kai ka kyauta ace kanwata ta cece ka amma ko godiya baka mata ba akan ido na ka sauke ta daga dokin ka.  Yarima yace banda ita ka taba ganin wani ya hau doki na? Munir yace dukda haka ranka ta ceta fa. Ajiyan zuciya yarima yayi yace bari na biya bashi tunda ba don allah tayi ba kamin gaba gaba a fara cewa ita ta haifeni. Yanzu me kake so ayi? Munir yace kawai kayi mata kyautuka.

Aliyu ne yayi gyaran murya, bude ido daya yarima yayi yace kana da magana ne ko shawara. Dan sosa kai aliyu yayi kamin yace ni a ganina mai zai hana ka bata wani matsayi fadar ka? Yarima yace me zaisa nayi hakan ? Wani magana ya rada masa a kunne jin jina kai yayi alsmar yadda kamin yace tamam anjima sai kaje kace gobe ina neman ta.

Munir da aliyu ne suka kalli juna aliyu yace matsalan naji ance sarauniya ta dauke ta a ganina sai kaje da kanka. Tashi yayi yace miko min riga na toh. Miko masa aliyu yayi ya shirya basu ma lura da lokacin da munir ya tafi ba.

Bangaren sarauniya suka nufa aliyu ne yayi sallama. Sarauniya da mugun mamaki ta gyara zama jin ance wai yarima ne yazo wajen ta jin jina kai tayi a ranta tace aikin kallamu kamar yankan wuka ban tsammaci zaizo da wuri kamar haka ba. Lallai duk addinin nashi shara ne tunda ko addu'an kariya baya yi. Tunda suke sau 3 ya taba shiga bangaren ta 2 yana matashi daya bayan ya zama saurayi.

Iso tasa aka yi masa ko da ya shigo gaishe ta yayi ta amsa tana fara'a har yanzu mamaki bai bar fuskan ta ba. Tace da na me ya kawoka? Ji yarima yayi kamar ta tsula masa bulala dan bakin ciki in ka ga yadda tayi magana kamar da gaske. Shima fadi yayi mama na alfarma nazo neman wajen ki ta ma kasa rufe farin cikin ta tace toh ina jinka.

Yace akwai wata baiwa ne da na gani toh kamin na dauketa sai akace kin riga ni shine nace idan ba damuwa ina so ki bani ita. Sarauniya tace toh wacce baiwa ce wannan? Yace bansan sunanta ba amma dai tana da nauyin harshe haka kamar tsamin baki in tana magana bayi uku basu san sanfa suka furta laila? Aliyu yace itane.

Shiru sarauniya tayi domin kuwa ta dauka gimbiya yazo nema amma dai bata baci ba ita dai burin ta kawar masa da hankali daga kujeran mulkin ne ta raba masa hankali dan haka indai baiwa zata iya abinda gimbiya ta kasa hakan ma yayi. Murmushi tayi dan bata yi tsammanin munira zata yi amfani da wuri haka ba tace toh kaga dai ina sonta sosai amma tunda dana ne ya nema zan bashi saide ina da sharadi duk sanda na nemeta zata dinga dawowa wuri na. Yace ba damuwa sallama yayi mata kamin yasan inda dare ya masa dan ji yake kamar akan 'kaya yake.

Da daddare wata baiwa lungui ake cema mata dan tsabar narkewar ta kamar kulya ko hararan ta kayi saide kaga kwalla yana bin kumatun ta😂 aikin ta daya ne goge takalman mutane sai cin tuwo.

Ita aka aiko bakin ta har rawa yake yi kamar wanda tayi sata tace babbar mu laila sarauniya tace ki hada kayan ki gobe zaki koma bangaren yarima. Munira tace aiya yaya na ya tausaya min yaga ina da ciwo kice wa munir kar ya damu ai aikin da nake ana ba mai nauyu bane ba sai ya bukaci na koma wajen sa ba.

Hadiyan yawu lungui tayi murya na rawa tace ba shi bane babban yarrimman ne hade rai munira tayi tace kabir? Girgiza kai lungui  tayi tace tsoran fadan sunan sa nake yi munira tace jabir? Girgiza kai lungui tayi mikewa tsaye munira tayi ta hadiye yawu tare da fadin na shiga uku dama kallon da ya min jiya nasan da akwai matsala wanban wani irin mutum ne ko me nayi tunda na ceci ransa kamata yayi ya rabu da ni. Allah kasa kar yace amin bulala waiyo Allah na.

Da gudu lungui ta fita ganin yanda muniran ke batun bulala ita de in kamason ka fanta a gaba gaba toh ace miko akushi lokacin itane sahun farko.

Washe gari munira ta hade kayan ta dama ba a wargaje suke ba ta fauki bargon kauna😁 ta nufi bangaren yarimaisan ta ke da wuya shugaban bayin bangaren sa me suna hansai da yatsa tayi mata alamun tazo munira ma da ta saba a mulki dukda kwanaki ladan ne dauke kai tayi kamar bata ganta ba.

Wuce ta tayi tana tambayan ina wanda zata nuna min daki na? Kafadar munira hansai ta dafa tare da fadin idon ki a sama yake ko baki ganni bane munira tace ai sannun ki ta dauka da wata kurman kike naga kina aiki da yatsa. Hansai tace Allah shafaffiya da mai? Cigaba da tafiya munira tayi kamin ta juyo kadan tace shiyasa nake dauke idanu.

Da shike hansai ma ta jiku wajen iya salon tsiya bata nuna ranta ya baci ba tace muje aani daki ta shiga da gadaje 20. Goma ta hannun dama goma ta hagu irin gadajen da masu labule ne ko wacce in zata kwanta ta sauke nata dukda kuwa gadajen duka a jikin juna suke. Ko wani bari wato side idan shugaban swajen namiji ne to za'a katange barin bayin sa mata saboda fadawan sa maza na shiga da fice a takaice za'a iya cewa a fadan kowa da gidan sa kuma gidan ma kowa da side dinsa.

Kowa na ta gyara gadonsa wasu na tattare kayan su wasu na share dakin wani gado a can dungu hansai ta nuna mata ko kqtifa babu a kai tace ga can gadon ki. Kallon ta munira tayi don neman karin bayani domin bata gane me ke gudana ba tabe baki tayi tace yamzu anan bangaren zaki na zama kina karkashin yarima kuma a dakin kananun bayi zaki zauna saboda ke karamar baiwa ce anan. Wani dariya ne ya kufce wa munira kawai ta fita ta nufi bangaren yarima kamar kura.

WANNAN NA JIYA NE A JIRA NA YAU ANJIMA INSHA ALLAH TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top