CHAPTER 4
Bangaren yarima kuwa tafe yake zuwa ga mahaifinsa bayan anyi sallan la'asar amma ba'a fada mahaifin nasa yake ba yana bangaren sa ne hakan yasa ba kowa a sai dogarai.
Sallama ne ya sanar cewa yarima umar ya iso sarki ya bada dama ya shigo sanna yayi musu alama da su basu waje.
Gaisawa sukayi yarima yace abba naji ance kana nemana. Sarki yace haka ne umar kaga ko wace shekara yan uwan ka kabir ko jabir ke zuwa zagayen shekara kaima wannan shekaran Kaine zaka je tunda ba su kadai na Haifa ba.
Yarima yace ABBA ba musu nake ba amma kana ganin babu wata matsala? Sarki yace karka damu farouq ai kaima da na ne ba su kadai na Haifa ba. Insha Allah ka shirya nan da sati biyu zaka kama hanya kuma dai ka sani tafiyar wata zakayi.
Zanso kayi aiki da motar nan kasan Wanda na siya wata biyu da suka wuce shekaran jiya aka kawo min ita.
Murmushi yarima yayi yace abba kaide kanason yin rayuwa kamar na turawan nan dubi masarautar mu ma kamar ba masarautar hausa ba.
Shima sarki murmusawa yayo yace ba wai inason yin rayuwar turai bane ina dai son al'umma suma su ci gaba ne a dinga aiki da technology. Yanzu banda cikin gidan nan ina ake aiki da telephone? Kaf kasar nan ban da masarautar nan da wani na can gabas su waye suka iya turanci?
Hakan yasa kaima na koya maka yaren turanci saboda ban San sanda rai zaiyi halinsa ba. Ni inaji a jiki na wata rana zai zamto sai da yaren su zamu yi aiki saide tsorona kar al'umman musulmai su shagala da koyan ilmomin su har su kai ga kwaikwayon su. Ranan da zai kasance aurarrakin my ya dawo irin nasu,shigar mu irin nasu, addini ma mun fara kwaikwayon nasu, duk wani shagula da suke yi sai al'umma mu sunyi ranan bansan inda zan saka kaina ba.
Yarima yace tabbas ABBA na fahimci abin da kake guje ma al'umma domin abdullahi bn Umar yace manzon Allah yace: "duk Wanda ya kwaikwayi wata al'umma toh yana tare da su." Hadisi sahihi Abu dawood ne ya rawaito hadisi na 3512 idan banyi kuskure ba.
Alamu sarki yayi masa alamun baiyi kuskure ba yarima yaci gaba da fadin toh ABBA Kaga kuwa idan al'ummar mu suna da hankali ko da wasa duk wata al'ada ko celebration da ba na musulunci ba zasu guje shi fintinkau.
Yanzu de ba damuwa zan je da izinin Allah, mai martaba Allah ya kara nisan kwana. Daga nan sukayi sallama yarima ya koma bangaren sa.
A kwana a tashi ba wasa har anyi kwana biyar da maganan sarki da yarima. Yarima na zaune a dakin zama(parlour) jakadan sa ya shigo ya sanar da shi gimbiya hauwa tazo.
Sanda yayi kusan minti Goma bayan ya tattare duk fefofin da yake rubutu da su. Yace wa jakada Ali yaje yace Mata yana bacci kamin jakada Ali ya fita ta turo kofa ta shigo bangaren yarima (courtyard) doagrai ne suka sanar cewa gimbiya hauwa ta shigo hakan yasa yarima ba Dan yaro ba ya Mike ya fito farfajiyan sa.
Wani mugun haushi gimbiya hauwa take bashi domin yar kanwar maman su kabir ne wato yar uwar su ce (cousin) saurauniya ke son ta lika masa ita yayinda yake gudu. Idan kana neman muna fuka Wanda ta iya kissa a fuska annabi musa zuciya fir'auna kar kaje da nisa kawai a tafi wajen ta.
Tayi kokarin kashe sa amma bai mutu, ta hada sa fada da mahaifin sa amma duk yanda aka bata sai sun sake shiryawa. Toh wannan Karen tayi masa shiri babba Wanda idan baiyi wasa ba zata Dana masa Kari ta zuba masa guba.
Kallo daya yayi wa gimbiya hauwan kamar na second 10 a karo na farko da ya Dade yana kallonta. Murmushi tayi ta dago kafa zata tako ta karaso ta mai kisisi na yace Ali in ta gama ganin yanayin gidan nawa ku rakata wajen umma (sarauniya).
Bayi Mata dake safa da marwa suna hidima saura kiris su fashe da dariya saboda yarima zai yarfa ka ko a jikin sa gashi ya iya gatse. Komawa dakin sa yayi ya jira Ali domin su gama hada kayan tafiyan sa Dan gobe zai kama hanya sannan ya roki alfarmar mai martaba yana so ya badda kama saboda kawo masa hari (assasination).
Nan sukayi sallama da mai martaba dan tun la'asar suke tare har sai bayan sunyi sallar Isha'I tukunna ya dawo dakin sa domin tashin asuba zasuyi.
Ko da asuba tayi ta yarima yayi sallama da kowa ya kama hanya bayan awa kamar 8 wani bafada ya zo da sauri ya fadi gaban sarki da sauri waziri yace kai me hakan? Kana so ka rasa ranka ne kake nema ka sa Allah ya tuhumi sarki? Tashi ka tsaya ka yi magana mutumin banza kawai.
Cikin rawar murya yace mota, motan da yarima ya fita da ita ta kama da wuta a kauye na biyu da ke gaban su. Sannan ta kone kurmus mutum daya ne yasha shine jakada Ali shima Dan akan doki yake tafiya biye da su yarima a baya.
Shigowa da jakada Ali akayi Wanda sanadin yana kokarin ya bude kofa ya ciro yarima ya kona hannunsa saide ya ce dogarin da ke tuka motan ya fada ruwa lokaci da motan ke kobo. A take sarki ya bada umarni a tafi a je a ciro gawan bafaden saide be rufe bakin sa ba ya yanki jiki ya fadi.
Cikin matsanacin farin ciki kabir ya nufi dakin mahaifiyar sa domin yayi Mata albishir burin su ya cika.
........
Yarinyar kuwa bayan ta nufi hanyar barin cikin gari da la'asar Dan yau gaba daya ba dadi take ji ba. Wasu dattijawa ne taji suna gulman ta cewa AI kashe mahaifiyar ta akayi hakanyasa ya fara dawo Mata sosai jiri yana kwasan ta bata ma San inda take tafiya ba.
Tuntube tayi ta fada karkashin wata bishiya hakan yasa ta jingina tare da rufe idonta har bacci ya kwashe ta jin ana sallama yasa ta bude idonta... bude ido tayi saide bata ga kowa ba, kogi ta gani a gabanta. Hakan yasa ta fara waige waige, ji tayi ana cewa gamunan a nan fa, gwagulatu tayi Wanda ke nufin a ina?
Jin muryoyi tayi suna fadin ke gamu nan a kasa, cuwe ne fa baki gane ni ba? Tunani ta fara ina tasan cuwe yace cuwe shugaban shashimami. Dariya tayi tace AI sai kace min shugaba cu ne ni na dauka tsuntsu ke magana shine yake kasa kasa da murya.
Malam cu yaushe gamo ka Dade baka kawo min ziyara ba. Me kuke yi anan AI tafiya ce me nisa daga gidan ku. Yace sarauniya ayi mana uziri ai mun yi kaura banba daya (sati daya) da ya wuce saboda nan din mukan samu abinci fiye da cikin gari. Dama so muke in komai ya daidaita na aika Dan aika ya sanar dake saide kash yau bil adama suka zo da wani karafunan su suka kunna mana wuta Wanda iya abin da na sani banda ke ba me shiga nan wajen.
Tace kai haba tana me kama haba ? Toh me ya faru? Yace toh nima dai ban sani ba iya abin da na sani shine mun fita neman na ci mun dawo muka ga anyi mana gobara, toh tile tururuwa ke fada min amma mai zai hana ki tambayi faho kifi shine ke yawan fitowa shan iska daga ruwa. Mude gefen bishiyan nan zamu dawo zamu zama makotan gara. Mun de nemi alfarma kar su cinye bishiyar.
Mikewa tayi tana fadin ubangiji na gaskiya ya taimaka nide bara in tam.... kamin ta karashe maganar ta tajiyo haniniyan doki yana tafiya kamar bayason yayi Wanda abinda yake fada shine kai wallahi na gwaru na kwaso ishin ruwa, Dan an arena min wayo shine za'a dani, kaf zamanin nan ba doki ya ni wajen kyau da jarumta. In na kara ganin shugaban nawa sai nayi masa wutsiya. Kai amma tafiyan kwana 3 ba wasa ba. Ni daga nan gabas na nufa. Waiyo baya na yana mai mika wuya domin yasha ruwa.
Bata kula sa ba ta durkusa tare da fadin faho, faho fito ka sayar min da labarai... kamin ta rufe baki bmfaho yace guda nawa zaki ba da ? Tace 5 yace shiyasa nakeson harka da ke. Ina kwance a nan wurin gabanin tanfare (goman safe) naji yo kara na dauka kifa duniya za'ayi sai naga wata bakar Abu ta taho ji kake....
Doki ne ya datse shi ta hanyar cewa na shiga uku, me zan gani mutum na magana da kifi, Kode nayi gamo ne. Yarinyar tace ba gamon da kayi nice sarauniyar wannan daji kuma aljanin dake cikin ta muna zaman lafiya saide bana ganin su kuma bana jinsu sai sun ga dama. Mu mun yarda da uban giji na gaskiya ne saide bamusan sunan sa ba.
Dokin rasa abun cewa ma yayi, cikin in ina yace sunan sa Allah ni kuma sunana yimla. Kifi ne yace ni de yanzu ba wannan ba sarauniya bayan anyi tirka tirkan nan fa jin sin ki fa ya fada ruwa ki cire mana shi Dan karnin jini ya dame mu ta sauri ta fada ruwan tare da fadin kaini wajen.
TOH FA ANA WATA GA WATA
SHIN KUNA SON YARINYAR TA RIKI YIMLA KO DE TA BARSA YA NUFI GABAS KAMAR YADDA YA KUDURA? KUNA GANIN BAFADE NE A RUWAN KO YARIMA? IN YARIMA NE YAYA ZATA KAYA TSAKANIN SU. KUNA JIN DADIN LABARIN NAN?
A SAMBADO MUN COMMENT SANNAN AYI VOTING.
Miss untichlobanty
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top