CHAPTER 38


DEDICATED TO S35807 hadizayakubu3 Hafnancy

Tagumi asma tayi tace Allah na gode maka aljanune dake ko kuwa hirar da mukeyi ne da ke ya miki girma yasa kika fada a soyaiya da babu ? Murmushi kawai munira tayi tare da rike hannun asma tace tayani daure kaya na. Asma tace hasbiyallahu wa ni'imal wakil toh ai shikenan.

Hada kayan ta sukayi tsaf sannan suka rakata har bangaren sarauniya domin taga makwancin ta da aikin da zata dinga yi. Gaishe da sarauniya inda cikin fara'a ta bada umarni ayi wa munira nuni da dakin ta lokacin suna tare da gimbiya hauwa. Su munira suna fita ne take jiyo gimbiya hauwa na fadin ni fa rabon da na kallesa har na manta a haka za'a yi auren bata ji me sarauniya tace ba saboda nisa da suka fara yi.

Budan baki tayi ganin dakin da aka kaita ya kai dakin ta na gida kyau in bai fishi ba ma kai kace yar masu kudi ne wai ita babbar baiwa da gudu ta fada kan gadon ta tana washe baki ta tattale kafa. Baiwar sarauniya wanda matsayi daya aka basu da munira hakan yasa ta kulu iya kuluwa. Rai a hade tace wa munira ke nan fada ne ba gidan ku ba ki nutsu ko baki koyi tarbiya da dabi'un fada bane.

Asma ne tayi caraf tace tunda kinyi abinda aka saka ki kin nuna mata dakin ta ai sai ki koma ko? Kar shugaba ta neme ki budan baki tayi zatayi magana munira tayi saurin janyo nana da asma ta hankada su gadon ta tana cewa ya kuka ji lauhi ? Tsaki hindu tayi ta fita. Asma ne tace bari na karbo miki kayan ki naji ana nuna wani daki wai anan zaki karba gyada kai kawai munira take kamar kadangaruwa har yanzu ta kasa rufe baki.

Da sauri da sauri take tafiya bata san sanda tayi karo da wani abu ba jinta tayi ruwa ya jika ta tun daga sama ta dago fuska tamau aliyu ne rike da bokati yana fadin Alhamdulillah Allah na gode maka. Wani karago asma taji a ranta bata san yanda akayi zuciya ya dibe ta ta falla masa mari ba.

Ficewa tayi daga bangaren ma baki daya shi kuma yana binta da gudu yana fadin baiwar Allah baiwar Allah ki tsaya kiji. Waigowa tayi tana huci tace idan baka daina bina ba sai na kara maka wani marin ji yadamda ka jika min hijabi na gashi ban wanke dayan ba.

Tsayawa yayi abin tausayi abin dariya da yar bokatin shi a hannu wanda sarauniya ne tasa aka yi rubutu wai dan yarima yayi wanka dashi hankalin sa ya dawo kan gimbiya. Hakan yasa suka nemo aliyu tunda shine mukarrabin yarima suka bashi ruwan saide shi kuma tunda yaji ana ya tabbata yarima yayi wanka da ruwan dumi yasan a kwai matsala yana tunanin yanda zaiyi da ruwan yasa bai ga asma ba jin ya zuba wa wani ruwa yasa ya tsaya dan bada hakuri saide ganin wanda ke gaban sa da kuma lura da yayi da cewa ruwan ya zube yasa yayi hamdala shi kanshi bai san hamdalan dan yaga asma bane ko dan ruwan ya zube.

Domin kuwa shekara 1½ asma ita ke kai kayan wanki shide yasan yana sonta saide baya son ya take dokan addini ya same ta ya fada mata kuma baisan me uban dakin sa yarima zaice akan hakan ba shiyasa yayi gum da bakin sa.

Nana kuwa da ta gaji da jiran asma sai ta fita dan neman ta wata baiwa ta tamabaya tace kamar taga ta fita ranta a bace. Dawowa wajen munira nana tayi tace mata kan asma ne ke ciwo ta koma daki ita ma zata tafi dama basu gama ninke kaya ba.

Karbo kayan ta munira tayi ta canja tana farin ciki ta samu freedom sosai yamzu kam zata yi duk yadda taga dama fitowa tayi ta nufi wajen sarauniya tare da tamabayan akwai abinda zata yi? Sarauniya tace mata babu sai gobe zaki fara aiki yau kawai ki nutsu ki gane kan wuri. Godiya munira tayi tare da neman izinin fita taje tayi sallama da kawayen ta na da sai kace tana da wasu kawayen inda sarauniya tayi mata izini.

Fitowa tayi kowa ya hadu da ita sai tayata murna ake tana godiya wasu kuma na gulman yaushe ma ta shigo fadan har ta shiga babban matsayi a bayi banda manyan bayin sarki ba wanda ya kai na sarauniya matsayi.

Wajen su nana taje anan asma ta fadi abin da aliyu yayi mata tana shirin fashewa da kuka munira tace ga nawa nan ki saka mana ga kayan aiki na ma ai tsayin mu daya zai miki duka dayan kuma wanda na cire yau idan aka wanke sai nana ta dauka a rage mata tsayi. Godiya dukayi mata.

Washe gari ta baje tana baccin asara yanda aka saba yanzu dai babu asma da nana da zasu tashe ta. Dan haka sanda rana ya fallo ta tukun tasan gari ya waye dirowa tayi daga gadon ta tsare kamar wanka zatayi tayi alwala tana me istigfari dan tana iya kokarin ta wajen ganin ta kiyaye dokoki dukda bata dade da fara musuluncin ba tunda a baya cikin dabbobi tayi rayuwan ta.

Wankan tayi tare da yin alwala tayi asuba sannan ta shirya tsaf cikin kayan ta ta nufi bangaren sarauniya da ruwan shayi sallama tayi wanda yayi daidai da lokacin da sarauniyar ta fito daga wanka dayan baiwar ta tana tayata shiryawa. Ajiye butan shayin munira tayi.ta gaida sarauniya sarauniyar ta amsa baiwar ta gama taje mata kai.

Sannan ta kalli munira tace aikin mu shine mu kasance ko wani lokaci muna gefen shugaba saboda dauko ajiye da miko sannan kuma mune yan aikan ta masu bata shawara kuma masu rike mata sirrin ta. Ta karashe maganar tana hararan munira. munira tace na fahimta.

Hakanan munira ta hau bakin aiki takan yi shirmen ta ko a jikin ta hakan kuwa yana bawa sarauniya nishadi sosai shiyasa duk inda zata tana tare da munira wani zubin takan sallami dayar amma har sai zatayi bacci munira ke tafiya. Hakan ya tsaye ma wancan a rai dan lokaci daya munira rayi mata juyin mulki.

Wata rana munira ta nemi izinin fita daga fada inda tace zata kai ziyara wa tsoho uban dakin ta ne amma a faskiya wajen su zul zata. Cikin jin dadi ta fara nuna musu kayan ta zaro wani dan abu tayi tace ga hatimin matsayi na ya kuka ganshi zul ne ya kwace ya fita da gudu yimla ma ya bishi suna dariya cillo tayi da takalman ta itama ta bisu suna gudu suna dariya wanda al'umma ba fahjmta suke ba.

Har suka fara fita daga gari basu ankare ba buya sukayi a bayan wani dutse itakuma munira ta dauka shiga kogon sukayi hakan yasa ta shiga da sanda dan tayi caraf ta kamasu. Magana taji wanda ta tabbata ba su bane sai ta saurara. Wani ne taji yace ya zama dole ne mu kashe yarima umar domin kuwa shi ya bada shawara a yaki garin mu bayan yarima kabir yace kar a yake mu. Wani yace ni dama ban taba daujan shi a shugaba ba domin kuwa idan ya hau kujeran nan kashin mu ya bushe ba yadda za'ayi muci gaba da harkokin mu. Gobe jumma'ah idan an tashi daga sallah yakanje farauta shi da bafaden sa daya a cikin kayan gama gari dan badda kama duk abinda ya kama sai ya baiwa marasa karfi a fadin sa yana so yayi sadaka da gumin sa. Muryan wani taji daga ji va zai wuce shekara 18 ba yace ta ya akqyi ka sani?

Dayan yace muna da kada a bangaren sa daga garinmu kafan yake dukda ba kowa yasan yana zuwa ba shi kafan ya sani. Dariya suka sheke dashi sukace shikenan ai mun temaka masa zamu mayar dashi gida ranan juma'a.

A hankali munira ta zame ta koma fada ganin ta tafi yasa su yimla binta sallama ta musu bayan sun koma gida sun fahimci wani abu na damun ta amma basu tambaye ta ba dan gani suke yanzu ta shiga mutane jar su mata shisshigi taji haushin su.

Direct bangaren yarima ta nufa domin yi masa gargadi...........

KAR A MANTA A YI MIN RUWAN COMMENTS TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top