CHAPTER 37

DEDICATED TO ihatsat05 , phauxy_S and Aishatuummulkhari bara muga su waye zasuyi comment dayawa gobe nasu ne

Kofan dakin shi ya kalla yace YARINYA DAGA YAU KINA KARKASHIN SHUGABANCIN YARIMA UMAR ABDULJALAL.

Fita yayi daga sashin sa sai bayan yayi isha'i ya dawo Ko da ya shiga samu yayi ta samu lungu ta bingire da bacci da alamu itama bata san sanda baccin ya dauke ta ba matsowa yayi kadan yana kallan ta yana duddubawa dan tabbatar wa da tayi bacci ba wai likimo tayi ba kamin yaji ta zaro wuka ta burma masa.

Juyawa yayi zai kira aliyu dan ya bemo bayi su tafi da ita wani abun yace masa kyaleta ta kwana kila in taga ta samu dama in tana da wani manufa zata aiwatar dan haka ka dinga bata kofa da daman maki. Shiru yayi yace kabir bana son abinda ke gudana amma tunda haka ka zaba.......

Aliyu zai kirq ya cicciba masa ita ya daura ta a gado sai yace toh shi kuma aliyu a su wa zai taba ta? Cire hulan sa yayi tare da tunanin da alama dai ya fara jingina sosai a jikin aliyu komai aliyu wani abu yace mai saboda ka yarda dashi ne.

Daukan ta yayi a ransa yace sai kace fanko anya ba azabtar da bayin nan ake anan hana su abin ci ba? Ya daurata a abin zama wanda zamu iya cewa kujera ne a lokacin su dogo ne sosai mutane biyar ma zasu zauna akai. Mayafi ya dauko ya rufa mata zai cire mata hijabi wani abu yance ina ruwan ka? Idan ma mutuwa zatayi menene naka a ciki? Bawa kanshi amsa yayi da babu sannan ya rage kayan cikin sa yar ciki kawai ya bari ya dauko wasu litattafai yana rubuce rubuce.

Nazari ya fara shin yarin yar ma ta yi sallah kuwa ? Bata rai yayi yace menene matsalar ka da ita ne kayi rubutun ka ko ka nemi waje ka kwanta.
Rife littafin sa yayi ya fara bin wutan da aka kunna yana karkashewa yaji munira tana magana kasa kasa murmushi yayi yace dama nasan za'ayi haka ta kasa hakuri na kashe wutan kamin ta aikatar.

Me son abin ka ya fika dabara sa'a nawa tayi tana kwance kamar me bacci? Tsugunawa yayi a gefen ta amma kuwa cira yake tayi kule yayi cas ji yayi ta riko kafadan sa da hannu ya dunkule hannu zai naushe ta yaga ta cabe fuska a baccin hawaye ya zubo mata tace karki barni yayi sadiya in tayi wasu sumbatun ta sai tayi shiru shide a hankali ya zare kafadar sa nemi wuri ya shimfida hakarkarin sa.

Washe gari ko da ya tashi ya sauko bismillah yayi zai rarumi takwabin shi ganin ta a kwance dan shi ya mance da ita ma kwata kwata tsaki yayi yace kai yarima me ka dauko wa kanka ne ka tashi wannan abin ta fita daga dakin ka da rayuwar ka. Takawa yayi bayan ya saka riga nai nauyi ya buga ta sau daya a kafa tare da fadin kamin na dawo daga masallatu bana son na ganki ko da ya karashe maganar ya kai baki kofa kamin ya wuce munira kam kara shigewa bargo tayi sanyin asuba ya sauko bata ma san yana yi ba.

Hantsi ya kawo kai wajen 8 yarima ya dawo ya samu mutuniyar tayi wani balance a take ranshi ya baci dan ya sake mancewa da akwai halittar ta ma kawai ya ganta har yanzu tana bacci. Duk sanda ya ganta har d'aci yake ji a harcen shi tsabar yanda yake kin ta.

Cewa aliyu yayi ya tsaya daga bakin kofa gani tayi cilli da hijab dinta saboda birgiman da tayi kafar ta daya a kasa.  Yaye bargon yayi ai kiwa kamar ruhin ra aka yaye ta mike zaune da sauri tana me riko bargon tare da fadin zan jefe ki nana wallahi asma ku kyale ni.

Jan bargon yayi ta ja ya ja ta ja tare da bude ido tana fadin neman maganata akeyi ne ? Ganin yarima ne yasa tace sai yanzu ka sanni ko? Tana sake jan bargon ja yayi dama ransa a hade yace zaki sake ko yaya ? Iya karfinta tasa ta finciko bargon ai kuwa ta hada da mai bargon dan yarima da ke tsaye bai tsinci kan sa a ko ina ba sai a kan ruwan cikin munira dagowa yayi idan shi ya runo saboda bacin rai zai daka wa aliyu tsawa zaisa ayi wa munira hukuncin yi mata wanka da ruwan sanyi kawai sai ga munir ya shigo yana gyara hannun riga yana mai fadin yaya ka manta ashuwakinka a .....

Kwana yasha da sauri saboda ganin su da yayi tare da fadin asuba ta gari cikin tsawa yarima yace asuba ta gari a gudan ku baka san sallama bane ko bazaka girma ba?

Hakuri yarima ya bashi yayin da munira ta nannade cikin bargon tayi kur da ido kamar zomo. Kallo daya yarima yayi mata tasan me ake nufi da sauri ta tattara kwamutsan ta ta nufi bangaren bayi domin ta hade kayan ta dan komawa bangaren sarauniya tunda tun jiya tayi alakwari saide tun daga hanya da ta fito duk bayi da masu aiki kallon ta suke suna tamabayan ina ta samo wannan bargon kuma amsa daya suke bawa kansu yanzu ita baiwar sarauniya ce kila ita ta bata shi kyauta. 

Koda ta shiga da asma taci karo tana kwashe kayan wanki da dauri ta watsar dasu nana dake shanya sabo ma ta saki bokatin da ruga da gudu harda hawayen ta tace uwar daki na ina kika tafi tana mai fadawa tare da rungumar munira hakuri munira ta fara basu asma tace wallahi in kika kara bamu tsoro irin haka bazamu sake kulaki ba .

Kowa muka tamabaya sai yace bai ganki ba duk hankalin mu ya tashi muje daki kinci abinci? Girgiza kai munira tayi nana tace bari nace na karbo miki yayin da ita da asma suka shiga daki kallon bargon da ke hannun ta asma tayi tace ah ah wannan kuma fa daga ina kika samo shi? Rungumewa munira tayi tare da waahe baki tace wannan yare ne da bazaki fahimta ba sannan ta subaci bargon.

Tagumi asma tayi tace Allah na gode maka aljanune dake ko kuwa hirar da mukeyi ne da ke ya miki girma yasa kika fada a soyaiya da babu ? Murmushi kawai munira tayi tare da rike hannun asma tace tayani daure kaya na. Asma tace hasbiyallahu wa ni'imal wakil toh ai shikenan.

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top