CHAPTER 34

Baki da hanci da ido ta saka tare da tsayawa a inda take saboda abinda idonta yayi arba dashi.

Tabbas wajen ya mata kyau da shike ginin da ne toh daki da parlour  duk a hade suke kawai bangaren gado ne aka dan kewaye shi da hijabi (labule) haka bangaren wanka ma amma kuwa ba dai girma ba dan yayi a hada dakunan su na bayi guda biyu wanda bayi ashirin ke kwana a kowanne.

Tsaki tayi tace ba kowa a ciki ma an kunna aci balbal an barsu ana asaran mai. Motsin sautin kafa taji yasa da sauri ta buya a bayan wajen sauya kaya. Shigowa yarima yayi ali na biye dashi sun dawo daga wajen mai martaba suna tattauna batun fada. Shiru yayi jin motsi a wajen hakan yasa yayi wa aliyu alamu da hannu cewa su fita.

Bayan sun dita sun rufe kofa ne yace sai ka fito ai. Kafa ya hango kamin aka janye da sauri. Dafe kai yayi yace yaushe zaka girma ne munir ? Matsowa ya fara yi wurin hakan yasa munira ma tayi gaba. Jinjina kai yarima umar yayi yace fine ! in haka kake so kewayawa suka fara yi can yarima umar yayi ajiyan zuciya yace na rasa me ke damun kabir kullum shi burinshi yayi kafada da kafada da ni. Shiyasa kaf gidan nan nafi yarda dakai kar ka ci amana ta kaji ko mun.......

Ji yayi an masa cakulkuli ta baya yana juyawa yaga munir hakan yasa yace munir? Da yatsa ya nuna wajen canja kayan ya sake kallon munir yace toh idan ba kai bane a can......

"Fadawa!" Ya daka musu kira su uku suka shigo aliyu a gaba annurin dake fuskan yarima ta dauke yace ku ciromin ko waye a bayan can. Tsugunawa munira tayi a ranta tace innalillah,hasbiyallahu, subhanallah,qul a'uzu bi rabbin nas, Allahu la'ila me ma zan karanta ne?😫

Tsayawa dogaran yaga sunyi basu cacumo mutumin da ke bayan wajen ba. Yarima yace uhm ? Aliyu yace mace ne yarima yace kusa tayi tafiya toh. Takwabi suka saita mata a wuya ta turo baki tana shiri kuka sai huhhura hanci take tace waiyo ummaaaa😫😢

Tsayawa tayi da kukan ganin yarima tace ruru? Dama haka takan kirashi idan tana kuka sanda take karama. Munir ne yayi saurin cewa kanwata? Kai matsar da takwabin nan. Washe baki yayi yace me kike yi anan? Oho kinzo neman yayan ki ne har kin yi kewata? Yadda ya fada kai kace yan uwan ne a gaske ko sunsan juna.

Hannu yarima ya nade a kafada yace ku yanke mata kai yana mai zuwa ya zauna akan kujera munir yace ku tsaya ku tsaya yaya kar ka kashe ta na santa fa ba ta da hatsari a gare mu. Munira da ranta ya baci cikin tsawa tace kai ruru wani abu ya same ka ne da ka dawo gida? ta karashe tana d'ana baki tare da yin mitsi mitsi da ido.

Munir yace "dama bani kika zo nema ba kanwata ?" Tace "kai dalla matsa." kamin da sauri kafa kamar machine tazo wajen yarima tace ruru wai da gaske baka gane ni ba? Shayi ya kurba yace aliyu me kuke jira.

Munir ne ya rungume shi yace yaya! Dan allah kar ka kashe ta. Sanda ya sake kurban shayin sa kamin yace kurkuku. Aliyu yace an gama. Kurkukun mata aka kaita ba laifi kai kace normal dakunan bayi me amma an saka karafuna.

..........

Washe gari rabi ta sanar da yarima abinda ya faru yanda munira ta bace musu da kuma yadda suka samin labarin yarima ya saka ta a kurkuku.

Hakan yasa yarima kabir ya tafi wajen yarima lokacin yarima munir ma yaje ya narke masa akan cewa idan baya son muniran ne shi ya bashi baiwar yana so.

Yarima kabir ne yayi sallama bai jira an amsa ba yace yace yarima fatan kana lafiya a takaice yarima yace um yarima kabir yace naji ance ka saka baiwa ta a kurkuku. Yarima yace um ta keta layi ta shigo har bagare na dan ta kashe ni. Murmushi yarima kabir yayi yace Umar kenan haka dabi an ta yake tana da rawar kai kuma sabuwar shigowa ce ba'a koya mata ladabi da nutsuwa ba. Wanda hakan na daukan mako 2 ne.

Takaddan da yarima ke karantawa ya rufe sai yanzu ya daho ya kalle su yace akwai banbanci tsakanin rawan kai da kokarin kashe yarima me jiran gado. Wani kaya yarima kabir yaji a zuciyar sa.

Zama shima yayi ya kalli yarima yace um mai jiran gado kace ai wanda har yanzu ke nufin baka zama sarkin ba. Idan kana so zan iya bar ma kujeran yarima me jiran gado ba zan taba nema ba ko an sauke ka amma kamin hakan sai ka cika sharadi 3.

Shiru yarima yayi dukda yasan kaso tamanin akwai yuwuwar karya yarima kabir yale amma bari ya bishi a wasan da yazo da shi hakan yasa yace ina jin ka.

Yarima kabir yace na 1 bazaka taba kashe baiwata laila ba. Gira daya yarima ya daga irin da gaske kake? Ni na dauka ma wani abu zaka fada. Yarima yace na biyu? Kabir yace na biyu cikin kwana  uku ka tara saka hannun mutane dubu goma a daular nan cewa kai suke so a matsayin yarima mai jiran gado ko mutuwa kayi kar a daura ni. Na uku kuma sai nayi tunani.

Munir ne yace yaya ta yaya za'a yi ya samu sa hannun mutane dubu goma a kwana 3? Ai hada su kadai ma aiki. Koda sun hadu zai dauki sama da kwana uku kamin su gama saka hannu kawai kace bazaka bar masa gurbin ba ni kar kuyi fada. Kabir yace zabi nashi ne ba naka ba. Yana kaiwa nan ya nufi waje tare da fadin kar ka manta da baiwa ta.

Munir yace yaya kar ka damu zan ciro ta. Ajiyan zuciya yarima umar yayi wannan yarinyar wace irin sa'a ce da ita?  Tafiya kurkuku yayi ya ciro ta suna tafiya a hanyar  su na dawowa tace yaya na nagode yace ba ni zaki godewa ba ki gode wa yaya na. Tace yarima?  yace eh.

yarima kabir yake nufi ita kuma ta dauka yarima uamr ne. Yace maza kije ki huta gobe akwai aikin da zan yi tace aiki kuma yace eh zamu karbi sa hannun mutane dubu goma hakan na da muhimmanci sosai ma yarima kuma zai bashi umm za'a iya cewa 'yanci. kasa kasa tace nide nasan bazai manta da ni dole akwai wata matsala dake damun. Ya zama dole na taimaka masa.

Tace yarima zan iya zuwa na taimaka ? Yace eh hakan zaiyi kyau ke sai ki tayamu karban na mata. Tace an gama sai da safe. Komawa bagaren su ta kwanta tana murmushi kamar wata shashasha. Nana da asma suka kalli juna kamin suka girgiza kai dan sun kasa gane me ke gudana a kwakwalwar kawar tasu.

KU BIYONI DAN JIN YADDA ZA'A KAYA A GABA WANI ALBISHIR AN KUSA AZO INDA KOWA KE JIRA AMMA SAI KUN DAN KARA HAKURI KADAN KAMIN AZO AMMA SOON YARIMA DA MATAR SA ZASU HADE.

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top