CHAPTER 32

ABIN DA YA GABATA KAMIN NAJE HUTU: munira ta yiwa yarima kabir karya ta ganyar sanar dashi sunan ta nana kuma shide ta masa. Bayan munira ta cece ran sarauniya kulu, sarauniya tace munira ta dawo wajen ta inda tace zatayi tunani. A yammaci ne munira ta fita neman yarima umar inda garin gulma ta shiga inda allah bai saka ta ba....

Fatan na same ku lafiya?

CIGABA:
Wani zubin zaman daji yayi domin kuwa ba tare da ta bata lokaci ba kamar yar biri ta dale bishiyoyi tana zuwa wajen ruwan taga maza uku ba riga. Ihu zatayi tana shirin rintse idanu amma dai ta tsaya sake kalla da kyau tayi taga tabbas yarima ne. Ta mance a sama rake kawai ta saki reshe akayi asha ruwan tsintsaye da ita sai jinta tayi a ruwan fadam.....

Ji tayi ta kurbi ruwa ba ta inda ya dace ba wato kofar hanci 🤭😂, ba 'bata lokaci ta fiddo da kanta mutane uku ta gani sun zuba mata idanu. Itama zuba musu na mujiya tayi tana jira taji yarima ya kira sunan ta amma shiru hakan yasa ta dauka ko farin ciki ne ya sandarar dashi ta rungume shi tare da fashewa da kuka cikin magana irin nata tace ka tafi ka barni a wajen su sanda nasha wahala na same kaaa😭 sakala kafan ta tayi a kunkimin sa tare da kewaye wuyansa da hannunta kai kace uwar da za'a kwacewa jariri ne. wani majaujawa taji anyi da ita zuwa sama ya kara lafta ta cikin ruwa danna kanta yayi har saida yaji ta daina motsi.

Kamar wani kura jijiyan kanshi har mikewa suke kai kace a filin yaki yake ya fito daga cikin ruwan domin a tunanin shi an aiko ta ne dan ta kashe shi. Fadawa ne suka shigo da sauri kamin suka tsamo munira.

Haka kawai yarima kabir yaji bari yaje ya jiyo abinda yarima umar ke kullawa wa kannan sa dan haka ya saka kayan sa ya fito ko da ya jiyo hayaniya tunda ya doso wajen bai wani damu da ya kara saurin takun sa ba.

Yarima jabir da munir da fadawa kuwa tsayawa kallon munira sukayi dan de ba wanda yasan ta kuma ba kayan bayi bane a jikin ta domin kuwa ta zama baiwar sarauniya amma ba'a bata sabon kayan tan ba tunda bata koma bangaren sarauniyar ba dan haka kayan da ta taho dashi daga gida ne a jikin ta hijabin nan kuwa duk wujijjiga ta da akayi yana nan bai fita ba.

Yarima munir ne yace wannan dai kayan ta ba na gidan fada bane kuma ba shigan bayi bane da ita sannan kuma bamuyi bakuwa ba balle muce bakuwa ce. Yarima jabir uban masu hankali 😁 cikin kasa kasa da murya yace in haka ne tana da hatsari da kuma farmaki ga rayukan mu.

Malam bafade ali ne ya kalli yarima da ke saka kayan bayan fitowa daga wanka yace ya zamuyi da ita kenan ? Duk da kuwa maganar nashi bai nuna da yarima yake ba. Ba tare da yarima ya yi tunani ba yace ku kashe. Abin da yasa ya fadi haka kuwa shine sanda ta rungume sa yaji wuka a jinkin ta hakan yasa ya yar da cewa kashe su tazo yi. Ita kuwa wukan kare kai ne abin ka da ta saba rayuwar daji bata yarda da mutane sosai ba.

Muryan yarima kabir suka ji yace hakan ba zai faru ba. Kallon shi yarima Umar yayi shima ya kalle shi suka yi kallon kallo yarima kabir yace sabuwar baiwar da na siya ne jiya dan haka ko me tayi ni ya kama ta na hukun ta ta tunda a kar kashi na take kuma abin da hanun dama na ya mallaka.

Kallon ta yarima umar ya sake yi kamin ya tako zuwa inda yarima kabir yake cikin daidaituwar murya yace ka tabba ta kana son ka kare macijiyar nan? Murmushin gefen baki yarima kabir yayi yarima umar yace ana tuhumar ta da laifin kokarin kashe dan sarki ne kuma kace baiwar ka ce? Yarima kabir yace kanina kana tuhumar ni na aiko ta ta kashe ka be? Murmushi yarima umar ma yayi yace ba ko daya yaya na. Ka dai kiyaye she wouldn't be always this lucky. (Ba kowani lokaci bane zatayi sa'a)

Yana kaiwa nan ya fita aliyu yana binsa a baya. Bayi mata yarima kabir yasa aka nemo suka dauke ta suka kaita bangaren shi tare da sauya mata kaya dan kar sanyi ya shiga jikin ta.
Yarima umar kuwa ko da ya koma bangaren sa ransa ya baci sosai kallon aliyu yayi yace ni yaro dan shekara biyar ne da zai kalle ni yace min sabuwar baiwar da ya siyo ne?

Ruwa aliyu ya miko masa yana me fadin Allah ya huci zuciyan shugaba na. Yarima yace ka saka wa yarinyar nan ido ko saka wani wanda ka yarda dashi a dinga fadamin duk wani motsin ta kaji ko? Aliyu yace an gama shugaba na.

Munira kuwa ko da ta tashi ganin fuska tayi daf da nata ta kalla aka kalle ta ta kalla aka kalle ta ihu ta kwala tare da tashi ta zauna itama baiwar ihu tayi dan bata tsammaci munira zata bude ido ba. Abinda yasa kuwa tazo daf da fuskan ta take kallon ta shine ta ga kamar ta santa amma bata tuna inda ta santa ba.

Saukowa munira tayi zata fita baiwar ta tare kofa munira tace ki matsa min baiwar tace kar ki sani a matsi yarima kabir yace kar a barki ki fita in kin tashi a kira shi. Komawa munira tayi ta zauna tare da laluma jikin ta taji wukan ta yana nan hakan yasa ta sauke ajiyan zuciya tare da cewa baiwar zata sha ruwa baiwar tana cikin zuba ruwa munira ta mike da gudu ta fita dai dai lokacin yarima kabir zai shigo dan haka tana ganin shi ta tsaya.

Murmushi yayi mata yace nana a ranta tace innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Yanzu duk girman fadan nan sanda na kara haduwa da wannan mutumin ? Zama yayi tare da yi mata alaman ta zauna zama itan ma tayi yace a kawo mata abin ci tace ta koshi yace umar ni nake baki.

Shiru tayi kamin tace naji zanci amma ina da sharadi murmushi yayi dan abin dadi yake masa yanda ta kalle shi ba wani tsoro wai tana da sharadi da wasu bayin ne da suna kokarin yin fitsari dan tsoro yace ina jin ki. Tace zaka barni in tafi kuma bazaka takura min ba. Yace na yarda tace toh ka fita yace an gama tashi yayi ya fice yana tunani shirirtar ta imdai tana cikin fadan ai haduwa ta zama musu dole dukda baisan daga wata duniya ta fado ba ko ina ta nufa dan haka shima kallon bafadan sa yayi yace masa ka sa mata ido ka dukga sanae dani koami game da ita.

Naman zomo aka kawo mata aikuwa ba ta lokaci sanda ta gutsira ma kamin tayi bismillah dama ta shiga ruwa yayi mata flushing din abinda taci. Zul ne ya fado mata a rai hakan yasa ta fita bayin suna kallan ta ba wanda ya hana ta dan yarima kabir yace a barta ta shiga kuma ta fita duk sanda take so. Lambu ta nufa direct ta fice ta wannan ramin da ta taba fita. Da sassarfa ta shige tana kokarin ta kira sunan zul ashe ma ya jiyo kamshin ta ai kuwa ta hangosu da gudu shi da yimla sun nufo ta.

Rungume su tayi kamin ta fashe da kuka ganin yanda zul dinta ya rame saboda baya samun wada caccan abin ci. Yimla dokin dai bai canja ba dan yana cin ciyayi dama yimla shi macijai da su shaho ko mugayen tsuntsaye yake ci toh nan kuma duk babu su shi kuma zama da munira yasa ya zama mai tausayi. Hakan yasa saide yaci abinda ya dan samu wani zubin ma ciyawa yake ci dan ya rayu dukda ba abincin sa bane.

Naman munira ta bashi tare da fadin ku zo mu tafi yawo yan uwa na. Yimla yace ina muka nufa. Munira tace kasuwa mutumi na tare da delewa tana mai shafa kanshi. Zulma kam sai sude baki yake dan ya samu nama ya ci.

DEDICATED to AMAL SUNUSI

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top