CHAPTER 25
Nana tace kar ki damu AI nima an cika min saide ni ba na kuyanga za'a saka ni ba. A mai bauta za'a sa ni kinga idan aka zabe ni sai kice kina so in zama jakadiyar ki. Munira a ranta tace AI tun kamin a zabe ni zan zabe ki dan ni da aure na. Nan de suka cigaba da sabgogin gaban su.
Washe gari mahaifin su ya tura a Nemo dukan su biyu domin su yafi a dinka musu kaya domin kuwa a ka'idar sarki baban yarima idan aka kawo bayin yaga alamar yunwa ko duka ko rashin sutura me kyau zai hukun ta uban gidan wannan baiwar Dan bayason zalinci a cikin masarautar sa.
Allah sarki baisan yan Mata masu yanci ake kyautar masa ba dukda a ciki harda bayin ma toh amma ana smuggle (simogal) din masu yanci ma hakan yasa masu kawo bayin suka kafa doka kowani uban gida dole ne ya dinka wa baiwar sa sutura masu tsada kamar na yaran sa.
Lokacin munira ko tashi daga bacci batayi ba samun wannan sako yasa nana tashin ta daga bacci baki a Dane ta tashi ko bude ido bata yi ba ta zauna a bakin gadon tana muttsika hanci nana tace shugaba yana neman ku. Tsaki munira tayi zata koma bacci nana ta riko ta da sauri tace uwar daki karki kwanta shugaba ne yake neman ki yanzu. Ajiyan zuciya munira tayi badan ranta yaso ba tayi kokarin yin wanka.
Nana ne tace uwar daki ina so in tambaye ki kuwa. Munira ta kalle ta tace uhm? tana goge idon ta. Kasa kasa da murya nana tayi tace a iya tunawa na kin gama al'adan ki da kwana 5 kika gudu. Shiru munira tayi Dan bata gane me take fada ba domin kuwa bata San me ake nufi da al'ada ba. Nana tace toh dam umm naga bakya sallah bansan ko ban lura bane amma sai naga naje nayi ke bakiyi ba.
Cikin rashin ganewa munira tace "ban'ane(bangane) ba" nana tace tace abin mana kai uwar daki ya zaki ce baki gane ba. Shiru munira tayi Dan kuwa wannan karan an ritso ta an fadi abinda batasan inda ya dosa ba. Menene sallah? Menene al'ada? Hanyar tsiranta daya tayi aiki da tikitin mantuwan ta. Dan haka tace na manca(manta) nan dai nana ta zauna ta Dan Mata bayanin iya ilimin da take dashi inda za'a rantaba kuwa ta rantaba don garin ba wani garin Ilimi bane kuma basa nema balle suyi aiki dashi sude gasunan kara zube.
Nabila kuwa ba tare da ta bata lokaci ba ta isa wajen tare da gaishe da mahaifin su sannan ta zauna. Kallon ta Dan masani yayi yace Mata ga yadi nan ki zabi Wanda kike so guda biyar za'a dinka miki tace toh na gode abba. Zaba ta fara yi lokacin munira ma tazo wani dake hannun ta mai shurin kala munira ta kalla bata San sanda ta tsuguna ta shafa ba tana mai bude baki saboda kyan da ya Mata.
Nabila tayi niyan ajiye wa amma ganin munira tanaso toh bari ta kara gyarawa kanta suna hakan yasa tace yar uwa ta idan kina so ne bari na bar miki Dan da naso na dauka. Baban su yace indai kina so toh ki dauka karki bata. Maman laila ta kalli nabila tace a iya abin da na tuna bakison kalar nan. Ta karashe tana tsare ta da ido. Sunkuyar da kai nabila tayi maman laila tace nofa na gaji da munafurcin ki Dan haka in bata min rai kike son yi da safiyar Allah ki tashi ki fice.
Dan masani ne yace haba maman laila ya kike min haka me yasa zaki korar min da diya? Toh ki kiyaye ni. Mikewa tayi tace in ita bazata bar nan ba ni zan bari tunda ta fini a wajen ka.
Nan ta fice suma suka zabi yaduka ba tare da kowa yace kala ba. Da yamma ne nabila ta kawo wa munira takalman da ta hada Mata murmushi munira tayi cikin jin dadi zata karba da ido nana ta Mata hani karabakh tayi ba tare da saurari nana ba domin takalmin ya Mata kyau wani Sawu biyu nabila ta sake nuna Mata tace kinga nawa ma iri daya da naki na mana yanda Aidan muka shiga fada kowa zaisa cewa mu yan uwa ne. Murmushin munira ne ya fadada ta rungume nabila tare da ce Mata na gode.
Sannan ta ajiye matan gefen na nabila tace ma nana ta kawo musu ruwa. Nabila tace amma yanzu ya za'ayi da rashin iya maganar ki sosai karfa hakan ya janyo aki azaban ki. Murmushi kawai munira tayi. Tace anyi ta in aduwa(zanyi ta yin addu'a) laila tace haka ne kam.
Kallon shimfidan da ke kan gadon munira tayi tace gaskiya shinfidan nan ya min kyau sabo ne ko? Daga kai munira tayi daidai lokacin nana ta kawo shayi tana har hada rai murmushi kawai munira tayi ta dauki takalman ta saka tare da fita da gudu Dan taje ta nunawa maman laila wacce take zaman maman ta yanzu Dan ita gani take Allah ne yaso ya bata sabon iyali tunda nata sun kita kuma sun kora ta.
Nana ne ta bita a guje yayin da nabila tayi wani murmushi ganin yadda munira ta fita da gudu sannan tace a sauka lafiya tana wani Dan iskan dariya. Daukan Mata itama tayi ta saka ta fito da sauri jin ihun a tunanin ta abin da take jira ya faru hakan yasa tayi saurin saide me ashe mahaifiyar laila ne ta biyo muniran akan dole ta cire takalmin Dan ba yadda za'a yi nabila ta nufe ta da alkhairi ita kuwa sai dariya take hakan ne ya faranta wa bayin dake aiki suka fara kiran sunan ta suna bata karfin guiwa kar ta bari a kamata.
Tunani nabila ta fara ya akayi har yanzu bata fadi tayi targade ba saide tunaninta ne ya tsaya lokacin da kasan takalmin kafanta da saman suka rabe. Ras kake ji a kasa ta gurje hannu da guiwa hakan yasa ta saki kara Dan haka hankalin kowa ya koma kanta. Murmushi munira bai gama daukewa ba Dan tasan za'ayi haka...
KU BIYO NI A NEXT CHAPTER DAN JIN YADDA AKAYI NABILA TA FADI BA MUNIRA BA DA KUMA YADDA ZAI KAYA A RANAN DA ZASU SHIGA FADA.
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top