CHAPTER 24
Munira tace wanne zan fara amsawa ? Maman ta ne tayi yake tace kinga yar uwar taki ta sha gajiya ki barta ta koma ta huta. Sunkuyar da kai tayi tace toh sanna ta rike hannun munira tace anjima zanzo muyi hira murmushi muniran ma tayi ta koma dakin ta bayan ta tafi maman laila tayi yake tace a dinga yi a hankali kinji ko? Ta amsa da toh Dan kuwa ta gane gargadi take Mata da ta kiyayeta ka tayi wani Abu ma yarta laila wacce taje munira.
Tashi tayi itama ta koma dakin ta tabar maman laila zaune a lambu tana rufe dakin ta tayi murmushin nan nata mai dauke ido tare da fadin SANNU DA DAWOWA LAILA.
(NOTE: Na manta sunan da naso na Kira yayar laila Dan haka zan Kira ta da nabila)
Zama nabila tayi a bakin gado ta bude wani akwati tare da cigaba da kera takalmin da take karawa tana cigaba da murmushin ta. Nide jikina yayi sanyi.
Ko da muka sake komawa bangaren yarima bai tashi ba sai bayan kwana uku lokacin mai martaba ya kawo masa ziyara. A hankali ya bude idon sa kamin ya sake rufewa da hannu mai martaba yayi wa mai magani alamun yazo da sauri ya karaso tare da rike hannun yarima.
A hankali yace yarima don ya gwada kwakwalwar tasa. Bude idon sa ya sake yi yana kokarin tashi suka taimaka masa ya tashi. Bin kallon kowa yake da ido suma suna binshi da ido suna jiran yayi magana shima yana jiran suyi magana. Suna jiran ya motsa gudu zaisa ko duka zai kai shima jira yake su motsa yankashi zasuyi ko yaya?
Mai martaba ne ya kalleshi yace masa Umar yace na'am yace ka sanni? Shiru yarima yayi kamin yace na dai ji zuciyata tana son ka. Yace nine mahaifin ka. Yarima yace na yadda. Sarki yace kai waye toh? Yace mutum mai muhimmanci dukda bansan waye ni ba. Mai martaba yace ni sarki ne kuma kai yarima ne. Jinjina kai yayi yace na yadda. Wani numfashi da kowa bai San yana rike da shi ba ya sauke tunda dai bai haukace ba toh Anyi sa'a kamar yadda mai maganin yace Dan haka ko me aka ga ya sameshi tunda sai bai haukace ba agode wa Allah.
Kallon mai magani sarki yayi yace yaya ake ciki Yusuf? Mai magani yace bazan dai iya cewa komai ba amma bisa abinda nake gani bai manta abubuwa ba amma jinin da ya cire a kansa ya tare masa abubuwa Dan haka zan iya cewa (nace idan zan iya tunawa sakan biyu da suka wuce cewa kayi bazaka ce komai ba😂) yace kwakwalwar sa ta manta mutane amma alakar dake tsakanin su bai tsinke masa ba. Yana iya jinta a zuciyar sa saide kamar yadda nace zuciyar sa tana cikin hatsari domin kuwa zata iya rikidewa taki Wanda yakeso kiyaiya me tsanani ko yaso Wanda yake ki ko kuma kiyaiyar da soyaiyar su iya janyo masa ciwo mai tsanani ko wanne ne ya faru saide ayi ta addu'a na kwakwalwar nasa zance nayi nazari da yan uwa na muga yadda zamu taimaka.
Shafa gemu mai martaba yayi yace Allah ya bada iko. Daga nan aka raka mai maganin bayan an masa kyauta me yawa. Kokarin mikewa yarima yayi sarki yace masa zauna zauna zauna.
Shiru be ya biyo baya kamin yarima yace me ya same ni sarki yace ni ya kamata na maka tambayan saide nasan bazaka tuna ba. Shiyasa nayi shiru.
Bafaden yarima aliyu ne ya shigo tare da samun waje ya zauna domin kuwa ba halal bane ka tsaya Dan wani mai girma yana zaune ko Dan yana tsaye kaki zama da sunan girmamawa.
Kallon shi yarima yayi kamin ya kalli gefe mai martaba yace wannan bafaden ka ne ismuhu aliyu and he is your confidante (amincaccen ka ne) gyada kai kawai yarima yayi.
Bayan mai martaba ya fita ne aliyu ya matso kusa yace shugaba na. Yarima bai kalle sa ba saima Ayabar sa da ya karasa cinye wa. Daukan wani aliyu yayi ya baya masa tare da mika masa. Kallon shi yarima yayi fuskar nan kai kace yaji warin tusa sai bata rai yake kamar an masa laifi yace fadamin komai da ka sani a kaina.
Rairairai aliyu ya fada masa komai da ya sani harda munira a ciki amma bai fada masa alkawarin aurensu na yarinta ko kwaron da taci ba saboda shima aliyun baya nan a lokacin haka yanzu ma baisan auren su ba saboda ba tare sukayi tafiyar ba. Toh ko tunda haka ne bai wani bata lokaci akan munira ba kawai de ya fada masa yadda tayi musu daru sanda aka siyo aliyu tace yarima yana so ya canja ta ne.
Hannu yarima ya daga masa yana hade gira ya tabe baki yace banason jin kayan takaici wuce ta. Yace sai akwai gimbiya hauwa Wanda ake son a aura mata yace itama wuce ta. Kusan awa 2 ya dauka yana fada masa komai da yake da muhimmanci. Saide fa da kaga yanda ya sha kunu kasan jiya iyau rashin sake fuska ya karu Dan idan zamu tuna a farkon labarin kafin yayi tafiyan zagaye don ganin yanda al'umma suke ciki baya sakan fuska inda dai anan ne yayi hatsari ya fada ruwa har ya hadu da munira harde ta kaisu da jin tarihi aka yi musu aure a dawowan su suka sake haduwa da wani iftila'in.
Bangaren su munira kuwa nazari take wannan wani irin al'ada ne a garin? Ya za'ayi a dinga daukan yara masu gata da yanci a yaudari sarki da sunan bayi ne a cika musu form din bayi karkashin Wanda zasu zama kuyangu kwai Dan su zama jinin sarauta. Dan kuwa matan sarki da kuyangun sa ahalin sarki ne.
Toh fa lalle akwai kura dole ta gudu daga gidan nan saide ko tayi kokarin gudun ma AI bata lokaci ne Dan kuwa ansa Mata tsaro mai tsauri. Amma kuma AI idan ta shiga fada sai ta buya saboda kar a zabe ta shikenan in ta hadu da yarima sai yayi ma kowa bayani. Jinjina kai tayi alamar yadda da shawaran da tayi da kanta ba tare da ta sani ba. Nana ne tace uwar daki na tunanin me kike yi. A rada nana tace uwar daki karde guduwa zaki sake..... da sauri munira ta rufe Mata baki tace ki rufa min asiri.
Zaunar da ita tayi tace "kewan ki". Nana tace kar ki damu AI nima an cika min saide ni ba na kuyanga za'a saka ni ba. A mai bauta za'a sa ni kinga idan aka zabe ni sai kice kina so in zama jakadiyar ki. Munira a ranta tace AI tun kamin a zabe ni zan zabe ki dan ni da aure na.
KAR A MANTA WAJEN SAMBADO MIN COMMENTS TARE DA VOTING.
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO.
Miss untichlobanty 💕
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top