CHAPTER 20

Fadawan da aka Danka munira a hannun su kuwa dama na marka ne Dan haka sanda suka nufi inda yafi ko ina hatsari a dajin dake wajen gari suka yi cilli da ita kuraje karanta tayi da wani dutse hakan yasa ta dafe da hannun ta. ko da taga sun fara tafiya tashi tayi ta biyo su da sauri amma dayan ya hankade ta zai taka ta da sauri dayan ya hanashi sannan yace masa yayi gaba yana zuwa.

Tsugunwa yayi a kunnan ta yace Mata kiji tsoran duniya karki yarda da kowa musamman mutum kuma kiji tsoran Allah. Sannan ya mika Mata wani sarka rabi yasa Mata a wuyan ta yayin da yasa wani Abu Wanda yake dayan Rabin sarkan ne. Tana hawaye da murmushi da jinjina kai domin kuwa ta sanshi shine abokin wasan a fadawa tafi shiri dashi fiye da kowa Dan shima ba wani shekaru bane da shi da kadan yafi yarima bayan rasuwan mahaifiyar ta ne aka mayar da shi bangaren marka Dan haka a boye yana gadin ta shi da sadiya amma wannan lamarin yafi karfin su domin kuwa linzami yafi karfin bakin kaza.

Gindin wani bishiya ta samu ta zauna tana kuka gashi yunwa take ji ga magariba ya kawo kai a haka har bacci ya dauke ta koda ta tashi wata Mata ta gani a gefe kamar balarabiya yar misisra alokaci daya tayi kama da hindi tana girki da sauri munira ta rarrafa tana kallon abincin da matan ke kwashewa. Kallonta matar tayi tace Mata zaki ci ne? Daga kai tayi matana ta miko Mata saide sai taga ta kasa taba abincin kamar babu.

Shafan kan munira matan tayi tace ashe biladama ce shiyasa kika kasa tabawa. Akwai wani bishiya kwakwa da na sani bari na kawo miki sau biyu munira ta Kira ido har matan ta dawo ta fasa Mata kwakwan. Bayan munira ta fara ci ne matar take ce Mata me ya kawoki nan dajin? Jin Shiruba amsa yasa tace a iya sanina dai ku bil Adam zuwa yanzu ya kamata ki iya magana ko kurma ce girgiza kai munira tayi wani Abu matar tayi tace ko dinga amani a zuciyan ki zanji. Munira tace toh matar tace me yasa kika zo nan? Iya abinda munira ta fahimta ta fadawa matan nan abinda bata fahimta ba kuwa ta barwa Allah...

Aljanar tace Mata toh nide bakuwa ce a dajin nan tafiya muke muka yada zango kuma ni musulma ce Dan Haka bazan cutar da ke ba. Bazan kuma baki komai da sunan taimako ba domin ba mai taimakawa wani sai Allah kuma a wajen sa muke neman taimako saide idan na barki a haka ko gari bazaki waya ba Dan haka in kinaso zan bude miki kunne da harshe zaki iya fahimtar maganar dabbobi sannan suma zasu fahimce ki ko wani yare kika yi.

Murmushi kawai munira ta Mata Dan abinda matar ke fada bai yi Mata ma'ana ba. Anan ne munira ya kasance take iya jin maganar dabbobi inda kullum zata je bakin ruwa tayi hira da kifaye da kwadi ta riki su tsintsaye su Nemo Mata abinda zata ci a haka har auka Saba.  Bayan tayi mako biyu ne ta hadu da dilan ta anan ne ta koma gidan sa kuma kogon da take da zama.

............

CIGABAN LABARI

ajiyan zuciya yarima ya sauke bayan ya gama sauraran tarihi su da ya manta dukda cewa ba komai aka fada musu illa kawai abinda sarkin ya sani. Kallon munira yayi yace Mata dama kece? Kiyi hakuri ban nemeki ba kika sha wahala hakan ya faru ne daga matsalan da na samu amma tunda yanzu naji gaskiya a aura min ke mu koma masaurata na. Kin yadda? Dan turbune baki tayi kamin ta jinjina kai sai de bata farin ciki da faruwan hakan a lokaci guda bata yi farin ciki ba domin kuwa lokacin da abin ya faru a yarinta ne AI bata ma San me so ko ki ba..

Nan aka daura auren ba wani biki bisa umarnin yarima akan zasu bar garin washe gari. Wanka aka taimaka wa munira tayi amma fa wani hanzari ba gudu ba Dan kuwa da aka ajiye Mata dokin ta aka ce za'a saka zul wato dilan ta a kaji tace bata San wanna yaren ba saide bazata iya dada musu hakan ba tunda har yanzu magana bai nuna Mata ba. Ko me akace Dan lallaba ta kalma daya take maimata musu BANACO (banaso) dan kuwa lokacin da kowa ya kita zul ne ya bata makwanci shekara da shekaru Dan haka suna tare dadi ko wahala bazata bari wulakanta shi ba Dan tasan amana da karanci abinda mutane dayawa suka rasa.

.......

Koda yarima ya isa masaukin sa inda aka taba kaishi abaya nan aka dawo dashi Dan haka a hankali ya jingina ajikin gini komai yana dawo masa kamr downloading ake murmushi kawai yake yana tuna shiriritar munira. Da guntun murmushin da dama bai baiyana ba atake ya dauke lokacin da ya tuno da gida ko ya zaiyi da sarauniya Dan yasan za'ayi tashin hanakali koda ta yadda ta karbi munira a matsayin matar sa tunda yar sarki ce bazata taba yadda ya mayar da ita sarauniyar sa ba. Abu daya da ya sani shine ba Wanda ya isa ya masa iko. Wajen karfe takwas bayi suka rako munira zuwa bangaren a hankali ta bude kofa ta shiga ta Ganshi zaune akan gado dagowa yayi ya kalleta kamin ya Mike ya fara takowa inda take. Daf da ita yazo yana kara matso da fuskan sa kusa da nata kasa ta kalla tara da rufe ido.....

AYI HAKURI ZAN BIYA BASHIN JIYA INSHA ALLAH. NAJI RUWAN COMMENTS FA DAN GASKIYA DALILAIN DA YASA NA MANCE BANYI TYPING BA JIYA SHINE BAKU MA YI COMMENT SOSAI BA SAI NA MANCE. DAN IN KUNA COMMENT NE IN NAHAU WHATSAPP NA GANI SAI NA TUNA YA KAMATA NAYI TYPING 👋🏻

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top