CHAPTER 18

Dawowa daga tunanin da ta fada tayi lokacin da taji munira ta zube a jikin ta kamin ta shafa fuskan kanin ta a hankali tana furta kalmar mama na ... mama na har ta tanki jiki ta fadi.
Da sauri yarima ya hanzarta ya dauke ta daidai lokacin Ali da wasu dogarawa sun samo wannan mai magani Wanda ashe sace shi akeso yi.

Da sauri yarima ya handoshi gefen munira sannan yace in ta rayu ka rayu in ta mutu.... sa sauri likitan yace ba sai ka karasa ba kayi min rai kamin cikin dimaucewa ya hau duba munira. Sa'o'i 2 ya dauka yana kokari kamin ya samu numfashin ta ya dawo Dan. Wani ajiyan zuciya ya sauke kamin yayin da yarima ya take ya tsaya gefen gadon da take kwance yace yaushe zata farka?
Baki na rawa mai maganin nan yace daga gobe zata iya farkawa a ko wani lokaci. Sannan ya tattare jakan sa ya fice kamar zai tashi sama. Haka yarima ya zauna yana kula da ita in yaji jikin ta yayi zafi sai ya jika tsumma ya dinga goge Mata goshi har sai ya sauka.

.....

Washe gari da sassafe takarda ya iso daga mahaifin sa cewa ya hanzarta ya dawo ya kamo hanya a take ana bukatar sa a gida. Kallon munira yayi kamin yayi ajiyan zuciya bai ce komai ba ya fita. Kofan dakin sadiya take yaje ya kwankwasa ta bude tare da gaishe shi yace Mata zan koma gida dukda wannan yanayin ba na tafiya bane. Jinjina kai yayi yace ki kula da su... had ya fara tafiya ya juyo yace "kice Mata zan dawo.." kai ta sake daga masa kamin ya kama hanya ya bar garin ko Karin kumallo bai yi ba.

....

Isan su ke da wuya yarima yaga alamun kamar taro za'ayi Dan yanda yaga bayi na shige da fice da alamu dai bikin wani Abu ne ba wai mutuwa akayi ba hakan yasa ya kara sassarfa don ya isa zuwa ga mahaifin sa koda ya shigo cikin fara'a mahaifin sa ya rungume sa yace masa maraba da zuwa Dana. Murmushi yayi ya zauna tare da fadin Abba me ke faruwa aka nemeni cikin hanzari haka bayan mako me zuwa ya kamata na dawo?

Murmushi mai martaba yayi yace gobe zan zabi yarima me jiran gado shiyasa na neme ka. Yarima shiru yayi kamin yace AI ko bana nan zaka iya daura shi abba da an bari ko kwana daya na kara na kintsa amma ko abinci ban sa a baki na ba sai a hanya naci.

Dafa kafadanshi mai martaba yayi yace ke ka huta ka sha hanya kaji ko? Mikewa yayi tare da godiya ya fice yana tunanin yanzu ko munira ta tashi ko bata tashi ba sai Allah. Ali ne ya lura da shi a hanyar su na zuwa bangaren sa Dan haka yace ya shugaba na akwai wani Abu da ke damun ka ne.

Girgiza kai kawai yarima yayi yayinda yake kankace ido alamun nazari domin kuwa lokaci daya tunanin sa ya koma kan abinda mahaifin sa ya fada masa ko dai so ake ace shi za'a bawa yarima me jiran gado bayan yana da yayi har guda biyu? Shi baya so a saka shi cikin wannan daurin da masifa irin na gidan mulki.

Gimbiya hauwa ya hango ta rugo da gudu tana fadin yaya Umar yaya Umar yaushe ka dawo? Rintse ido yayi San yarinyar sam bata masa ba... abinda bai sani ba tafi kayan haushi bayan ta girma dan a lokacin bazata wuce shekaru 7 zuwa 8 ba. Dauke kai yayi yaci gaba da tafiya ta riko hannun shi tana fadin magana nake maka yaya Umar da sauri ya warce yace sake ni da wani kazamin hannun ki kuma kar ki kara ce min yaya. Yana kaiwa nan tayi gaba abinsa.

Har dare yana ta nazarin yadda zai samu ya gudu daga kujeran mulki yayin da lokaci zuwa lokaci yakan yi tunanin ko shin munira ta farka ko kuwa ya ake ciki. Abinka da shekarun baya masu yawa babu wayar salula a kasar saide a aika sako shima sai mutum yana da hali.

Washe gari da sassafe Ali yazo ya tashi yarima Umar. Juyawa yarima yayi ba tare da ya bude ido ba. Bafade Ali yace shugaba na ka tashi safiya tayi kana bukatan ka shirya saboda taron da za'a gabatar. Kara Jan bargo yarima yayi yace idan nayi latti de baza'a kashe ni ba ko? Ali yace wa ya isa? Yace toh ba yanzu zani ba ka san cewa bana son tashin safiya.

Ali yace amma kamin ya guda yarima yace umm? Da sauri Ali ya fice yana fadin tuba nake uban gida na. Sanda yarima ya Shari bacci kusan na Rabin sa'a kamin ya tashi shiryawa yayi sannan ya hau dokin da aka shirya masa suka nufi fada.

Koda yarima ya isa su kabir suj rigashi isowa bakin kabir har kunne za'a yi nadin sarauta shi wai Dan ma ba sarki zai zama ba. Koda suka hada ido da Umar miko masa hannu Umar din yayi domin suyi musabaha saide kabir din kamar bai ma Ganshi ba yayi gaba abinsa yayinda jabir ke binsa a baya.

Kamin kace me al'umma sun cika fada kamar za'ayi tashin duniya wasu yan kazafi har sun fara taya kabir murna saide mutane dayawa sunshade jinin jikin su lokacin da aka nada yarima Umar a matsayin yarima mai jiran gado wato crown prince inda mutane kalilan sukayi farin ciki yayinda mafi akasari suke bakin ciki bawai Dan kabir suke so ba saide suna ganin kamar yarima Umar zalinci zaiyi domin kuwa kamin ka samu Wanda zaice ya taba ganin dariyan sa  toh ka hadu da aiki hakan yasa suka ganin bashida tausayi balle imani dukda ko a lokacin matashi ne ma.

Godiya yarima Umar yayi yace nagode da wannan karramawa ya mahaifi zanyi iya kokari na wajen ganin na kare al'umma na. Sarki yace nasan mutane dayawa bazasuyi farin ciki da wannan Abu da nayi ba tunda kuwa a bisa ka'idar musulunci ba'a bada gadon mulki saide a zabi masu gaskiya da amana a cikin al'umma su duba suga waye yafi cancanta ya zama shugaba bawai Dan sarki ya gaji sarki ba. Saide shekaru dari da ya wuce an fara kafa masarautun gargajiya inda abin ya zamto Dan sarki shi zai gaji sarki idan mutum ba jini sarauta ba bazai iya zama sarki ba a kasar nan tamu da ma kasashe dayawa na duniya.

Hakan yasa na fahimci indan na mutu bazaku yi aiki da ka'ida na usili ba acikin yara na zaku zabi daya toh me zai hana na duba Wanda yafi nazarta a ciki na zaba muku? Cikin hada baki sukace lallai sarkin mu mai hikima ne. Yace na sallame ku. Sankira yace an gama kowa na iya watsewa da izinin Allah.
Bayan kowa ya fita maimartaba ya bukaci yarima ya tsaya domin yanada abinda zai tattauna da shi. Zama yayi sarki yace dalilin da yasa na zabeka tun kana da karancin shekaru shine inaso zam turaka zuwa nahiyar yahudawa ka Nemo Ilimi dago kai da sauri yarima yayi tare da bude baki...

FATAN KUNA CIKIN KOSHIN LAFIYA ? AN KUSA AZO ASALIN WAJEN FA DAN KUWA TUNA BAYA YA KUSA KAREWA YANZU NE MA ZA'A SOMA USULIN LABARIN FATAN ZA'AYI MIN UZIRI A YAFE MIN RASHIN UPDATE DINA AKAN  LOKACI MAKARANTA NE YA BOYE NI😌

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top