CHAPTER 16

kuyanga sadiya Dan da ke cikin ta ne masha Allah tabarakallah akwai girma ita kuma tana da karancin jini a dinga bata abinci masu kara jini bawai Gina jiki ba. Marka tace mun gode auwalu mai magani yace Allah ya kara lafiya shugaba ta sannan ya fice.
Murmushin mugunta tayi ta kalli asabe tace kin San mai zakiyi. Murmushi asabe tayi sannan tace an gama.

Kamin yamma ba abinda ba'a kawo wa khadija ba daga abinci abin sha kauna sawa kayan marmari duk wani Abu da mutum ke bukata an kawo Mata ahar kayan dskin ta sanda aka canja da sabi. Munira kuwa sai bin masu shiga da fice take a baya. Bakin ta har kunne.

Da gudu ta shigo daki bayan bayin sun watse tace mama kinga kayan da aka kawo mana kuwa? Masu kyau sosai da abinci da nama kala kala har masu aiki ma sanda aka karo mana.

Murmushi kawai khadija tayi munira tace mama bakiji dadi bane? Girgiza kai khadija tayi tace naji amma dai kiyi a hankali kinji ko munira ko da wata rana bana nan kar ki yadda da marka amma kar ki nuna Mata baki yarda da ita ba. Gyada kai munira tayi sannan ta dauki kindai ta zuba abinci a ciki ta tafi kaiwa sadiya tana jin dadi.

Tana shiga taga sadiya da likidiri (bokiti) har ta saka kayan aiki tace yaya sadiya yay sadiya an kawo mana abinci dayawa shine ba kawo miki cikin jin dadi sadiya tace nayi farin ciki da haka ko ba komai bazan yi wahalar banza ba uwar daki na zata ji dadi.

Cin abincin sukayi tare sunata hira abin su. Sai wajen magriba ta bar wajen sadiya ta dawo gida ranta wasai. Wajen sa'a 8 kawai tana kwance ita daya ta Mike ta fita da gudu khadija na kiran ta tace ina zuwa mama.

Bangaren yarima ta fada tana fadin Umar! Umar!! Umar!!! Kokarin rikota fadawa sukayi tabi ta kasan kafar daya ta shige sulut abin ta suka biyo ta da gudu amma gudun tsiya ne da ita.

Tana faduwa taga yarima zaune da wani yaro a gefen sa ya rike hannun sa suna rubutu ko Zane daka ma yarima duka tayi a cinya tace me yasa? Me yasa? Me yasa zaka ki ka bani nayi Zane shi ka koya masa? Waye shi? Sabon aboki kayi shiyasa baka nemeni ba ko?😭 da sauri ya ajiye alkalami da ke hannunsa yace yi hakuri munira sarauniyar Mata bude ido ki kalla sunan sa nake koya masa kuma bawan da na siya ne a kasuwa. Bude ido tayi ta kalla sai ta sake fashewa da kuka tace so kake kace bani da Ilimi ko? (😂kai jama'a )

Yace ni na isa ? Tace AI kasan ban iya karatu sosai ba yance kema sai in koya miki washe baki tayi tana masa marmar da ido tace da gaske? Daga kai yayi sai lokacin fadawa biyun nan suka iso gaiyar asara sai haki suke wai su a dole neman munira suke. Tsawa yarima ya daka musu yace da kashe ni za'a da yanzu gawa na ya fara shan iska.

Cikin rawan jiki suke fadin tuba muke yarima kayi mana rai tuba muke tuba muke kallo ya watsa musu da sauri suka watse. Sunyi sharkab da gumi kai kace wanka sukayi.

Munira tace yarima kasan meye ne? Yau aka kawo mana kaya dayawa abin ci ma dayawa in fada maka ta karashe tana cin farce. Murmushi yayi yace haba? Da ba'a kawo muku ne ? Daga kai tayi tace ba'a kawo mana shine wannan matan sukayi ma yaya sadiya sharri wai ita take sacewa kuma karya ne yawanci ni nake zuwa tambayo wa basa bani saide ma su koreni ko su zage ni idan na Rama sai a fadawa mama babba (sarauniya) tayi min bulala.

Kananu da ido yarima yayi domin irin wautar da sarkin garin nan yake yi dole ne a fige sa idan bazai iya kula da Iyalin sa ba ya batun gari kacokam? Haka de suka cigaba da hira anan munira tayi bacci. Har yarima yace wa aliyu ya goyeta ya kaita gida sai kuma de wata zuciyar kawai tace ya kai da kanshi baisan halin aliyun ba dukda lokacin su bai baci kamar namu ba.

Lokacin da ya iso gaba daya hankalin khadija ya tashi ko dai guduwa ta sake yi ? Dan ta aika a tambayi sadiya tace AI ta Dade da barin wajen ta. Godiya tayi ma yarima a karo na farko da suka hadu kenan haka kawai yaji ta kwanta masa matan akwai nutsuwa dukda shekarunta 27 a lokacin babba ce a wajen sa. Gashi kaman su daya da munira kawai yarinta da manyanta ne ya banbance su.

Cikin da ke jikin ta ne ya fado masa a ran shi yace kai masha Allah wannan girma haka kode takwaye zata Haifa yana lissafe lissafen sa har ya koma dakin sa. Nan ya saka aliyu a gaba yana masa tambayar kwakwaf yanda akayi ya zama bawa nan ya sanar da shi yaki akayi a garin su aka dauko shi kuma shi Dan Senegal ne.

......

A kwana a tashi rayuwa ta warware wa su munira kamar ba su ba har kwana biyar shiru marka bata yi wani Abu ba hakan ba karamin tsoro yake  bawa khadija ba Dan tasan na kasa na kasa. Munira de ba ruwan ta banda guje guje kaga ta shigo ta fita ta shiga ta fita ita haka take yini zubran. Ga wani Dan iskan dariya da ta koya me wani shegen kara in ta fara ko baka San me yasa ta dariya ba kaima sai kayi.

Wajen karfe 8 munira tana zaune yarima yace Mata neera? Gira ta daga ba tare da ta kalle sa ba ta sake dangwalo tawada tana zana bishiya. Yace gobe ba karki zo da rana kinji? Gyara hannun Riga tayi yadda ta maida hankali kai kace professor ke research tace me yasa ? Tana zana ganyaiyaki a jikin bishiyan. Yace zan fita kasuwa ne kinsan na ku sa komawa gida tunda na warke. Tace toh amma da ni zaka tafi ko?

Yace ah ah sai kin girma zanzonwata rana na dauke ki. Tace kayi alkawari? Yace nayi. Tace tohm shikenan sannan ta dauki yadin da take zanen a kai ta fita da gudu tana fadin sai gobe. Zan nuna wa mahaifiya ta Zane na.

.....

Washe gari da hantsi nakuda ya kama khadija. Mai karban haihuwa aka Nemo yanzu ne anjima ne shiru sai dibo ruwa ake kar amma in za'a fitar jazir da jini. Munira kuwa anyi anyi ta bar kofan dakin tace Sam dukda an hana ta shiga ciki toh ba inda zata. Mai karban haihuwan ne ta fito marka cikin nuna damuwan munafurci tace yaya dai har yanzu shiru.

Jiki na rawa mai karban haihuwan tace bayin da na aika su Nemo ruwan zafi ne shiru basu dawo ba shine zanje karbowa. Da sauri munira ta riko ta tace AI ba aikin ki bane karbo ruwan zafi idan kika bar mama na wa zai kula da ita.

Mai karban haihuwan tace ke yarinya da ke me kika sani ruwan yana da muhimmanci ne sake ni. Kuka munira ta sake fashe wa dashi zata fada dakin aka riko ta fadi take a barni naga mama na a barni naga mama na amma aka Mata rikon huhun goro.

Wata baiwa ce tazo da gudu tana haki ta durkusa gaban marka tace ranki shi Dade mai amsan haihuwa ta gudu. Kowa yace mene? Ta sake cewa TA GUDU.....

TASHIN HANKALI KAKA KARA KAKA DIN KENAN KAI JAMA'A WAI YA ZA'A KASANCE NE WANNAN HAIHUWA NA TANGARE GARE

KU BIYO NI CHAPTER NA GABA DAN JIN YANDA ZAI KAYA GASHI AN KUSA A FARA SHIGA WAJE ME SIGARI.

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top