CHAPTER 14

Yana fita ya rufe kofa yaji Muryan munira tana cewa toh ni ka ban nima nayi zanen da sauri ya sa aka rufe dakin yarima sannan ya nufi fada sai haki yake... 

Gaban sarki ya fadi tare da fadin ranka shi Dade munnn....munira yana nuna kofa da yatsa sarki yace an same ta ne? Ya daga kai da sauri da hannu sarki yayi alamun dogarai su Nemo ta Dan shi can ya manta ma da zai Mata hukunci tunda aka neme ta aka rasa.

Bafaden nan aka saka a gaba zulum zulum zulum ya nufi bangaren yarima. Daya daga cikin dogaren ne yace nan fa hanyar bangaren yarima ne. Bafaden nan bai kula su ba sanda suka isa ya karbi mukulli ya bude. Dakin yarima suka shiga ya dago kai a Tanake yace ina tawadan da nake nema?

Bafaden yace munira muke nema. Da hannu yarima yayi musu alamun bismillah sannan yaci gaba da zanen sa. Duba ko ina sukayi kaf amma babu alamun munira idon bafaden nan ya Rena fata. Cacuman sa sukayi aka mayar da shi gaban sarki tare da neman ayi masa hukunci na bata musu lokaci da yayi saide fa bafaden nan shima ba kyal bane.

Tattaro kwalla yayi ya fara sadakar su yana fadin ayi min rai ya mai martaba tsananin ganin tashin hankalin da ka shiga yasa nake ta Allah Allah a samu gimbiya munira shiyasa na fara gani da jin alamun ta a ko ina saboda kowa ya sani akwai ta da tsalle tsalle.

Jin jina kai sarki yayi yace duba da cewa bisa damuwa da ni yasa kayi haka an yafe maka amma dai a kiyaye  na gaba. Wannan bafade yace godiya nake ranka shi Dade.

A kwana a tashi har kwana 3 da faruwan wannan al'amari saide munira shiru ba ita ba labarinta. Yayinda bangarenta fa duniya ta Mata dadi bata aiki saide tayi ta surutu ko wasa da yarima ko kuma suyi Zane Zane. Wani lokacin takan yi kuka tace tanan son ta koma wajen maman ta da kanin ta amma yarima yace ta bari tukunna sai sun shirya dabara.

Washe gari yarima ya warware baki daya Dan haka ya fita yace yana so a rakashi kasuwa Dan ya Dade a daki zama waje daya ya damesa. Sarki yace masa akwai hatsari yayinda ya dage cewa shide shi daya zai fita kuma zai 'badda kama ba sai sun damu ba.

Ba Dan ran sarki ya so ba aka barshi ya fita. Shagon Dan kunne ya gani na gold kundai San kirar da Dan haka ba wani kyau bane ba ma da shi kamar manne de haka ya siya ma munira guda dankunen. Hayaniya ya gani a gaba Dan haka ya karasa Dan jin me ke wakana a wajen wani bawa ya gani Wanda da kyar idan ya kai shekara Goma an dake sa har ya fita a haiyacin sa.

Abin ya bashi tausayi ya kuma bata masa rai Dan haka cikin tsawatar wa yace waye wannan? Wani mutumi rike da bulala yace kai yaro waye kai ? Ba taee da yarima ya kulashi ba ya sake nuna bawan yace waye wannan? Wata Mata ce tace bawa ne yayi sata shine uban gidan sa ya dake sa.

Yarima yace ina ubana gidan nasa? Nuna wannan mutumin da ke rike da bulala akayi yarima yace zan siye shi. Dariya mutumin yayi yace da fari dai kai matshi ne karami, sannan menene marabarka da bawan da zaka siya murmushi kashin ka ya bushe yarima yayi yace a juri zuwa rafi sannan ya jefa ma wannan mutumin makudan kudi (azirfa) fiye da kudin bawan.

Dauka mutumin yayi ba kunya ba tsoron Allah yace an rabani da alakakai barawon banza da wofi kawai. Anan ne farkon haduwan yarima da jakadan sa Ali. Goyan shi a Kan dokin sa yaci gaba da tafiya...

A gida kuwa sadiya na zaune a kasa tana yi wa khadija wato maman munira tausa tace sadiya kin hada min ruwan wankan ko ? Sadiya ta amsa da eh tare da Karin saide naji jikin ki da dumi sosai uwar daki na ya kamata ki sha magani. Mikewa khadija tayi tana fadin karki damu ki hada min in na fito daga wanka zan sha...

saide tana karashe wannan kalmar ta yanki jiki ta fadi labari ya karada ta ko ina. AI khadija zata haihu a wannan jita jiran ne munira ta jiyo wasu fadawa da iron nasu labarin wai AI khadija ta kasa haihuwa ta mutu.

Munira bata san yadda akayi bam kawai ta tsinci kanta ne tana gudu zuwa dakin mahaifiyar ta. Saide shigan ta ke da wuya tayi kicibus da sarki ba tare da ta kula ba ta fada jikin mahaifiyar ta Wanda zazzabi ne fa ya sa ta yanki jiki ta fadi.

Sarki ne yace munira? Kece? Daga kai kawai tayi tare da juyowa ta rike hannun mahaifiyar ta tace mama me ya same ki? Murmushi tayi tace na warke ai, sarki ne yace munira je ki ayi miki wanka sai ki dawo kinji zazzabi ne yake damun maman ki. Da sauri munira ta tashi ta kalli maman nata tana bata rai tace mama kin sake kwana ba gawayi ko? Girgiza kai tayi tace je ki yi wanka.

Make kafada munira ta Lara yi ranta ya baci tace karya ne ga dakin nan da sanyi me yasa baki fada ma yaya sadiya ta karbi ba idan sun hana.. bige Mata baki khadija tayi tare da yi Mata tsawa tace ki fita! Ba sanda nace miki kar ki kuskura... taro ne ya sarke ta ba Dan ta so ba tayi shiru munira kuwa tsuguna tayi gaban sarki tace baba ka nema mana hakkin mu me yasa aka maidamu kaman ba iyalin la ba.

Ba a bamu abinci yanda ya wadata ba'a bamu gawayi sutura ma namu bai kai na saura kwari ba kullum idan inaso in fada maka sai mama na ta dinga hanani wai nayi hakuri idan baka son mu ne sai mu bar maka gidan ka. Wannan karan Mari khadija ta sauke ma munira dukda ko ji take kamar kanta ta mara saboda yadda take son tar nata tace ki fice da ga dakin nan.

Sarki ne yace ba inda zata. Zama yayi a gefen khadija yace me yasa kuma shan irin wannan azaban kuka yi shiru? Murmushi khadija tayi a ranta fadi take idan har nayi magana lallai za'a cutar min da munira na Dan haka wannan wahalar ba komai bane a fili kuwa cewa tayi ranka shi naga harkokin mutanen gari ma kadai ya ishe la ba sai mun kara maka da namu ba.

Mikewa yayi yace ta tabbata kenan.... waye a wajen? Bafadu biyu ne suka amsa da Allah ya kara ma sarki lafiya. Yace a je a kawo min marka yan zunnan!

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top