CHAPTER 13

Sarauniya tace wa jakadiya a Nemo mata takwabi yayin da ta kalli tami tace SAI ME KUMA KUKA AIKATA KE DA UWAR DAKIN TAKI?

Baki na rawa tace tuba nake ranki shi Dade wallahi babu wani abinda muka aikata da yake ni ina da aljanu wani zubin sukan sa nayi Abu kamar zaucacciya a yi min uziri a yafe min tuba nake tashi sarauniya tayi tare da fara dodo ta sai ga marks ta fado da gudu munafuka cikin kuka ta durkusa gaban sarauniya tanan fadin Dan Allah ayi wa jakadiya ta rai walli yare muka girma a taimaka kar a kashe ta. Sarauniya tace ku kama su dukan su biyu ku daure su.

Sannan a kawo min hatimin yarjejeniyar bautan su zan siyar da su yanzunnan munafuka dama haushin ki nake ji kin tsaya min a kofar hanci. Bayi ne suka fara cewa Allah ya huci ran sarauniya. Allah ya huci ranki mahaifiya  kuma jagora a garemu, hukuncin ki adalci ne.

Sako sarki ya aiko cewa yaji me ke faruwa ya baro fada yana bangaren sa kowa yazo farfajiyan sa. Hakak ko akayi sarauniya ta zauna a gefen sa. Cikin bacin rai da daga murya yace me kuka mayar da ni a gidan nan be? Abin wasa ? Diya ta bamu ganta ba bamu San ko makiya ne suka dauketa ba amma ko a jikin ku shine kuke hayaniya a gida na?

Da sauri suka fara bada hakuri sarki yace a yi wa marka da kuyangan ta bulala 15 ko wacce su. Marka fuskan abin tausayi ta saka tace tuba muke mai martaba amma kasan aljanu gareta duk abin da ta fadi cikin dimuwa ne amma ni ba wai nace kayi min rashin adalci bane idan haka shi kaga yafi toh a hada nawa da ba jakadiya ta ayi min 30 domin kuwa ni ya kamata na kareta Dan a karkashi na suke.

Usilin markan kenan ita bazata nemi afuwa a haka sai de ta karbi laifin ta da Wanda ba nata ba hakan shi ke sanyaya zuciyan sarki yayin da abin ke yi wa sarauniya ciwo saboda yadda marka ke taka kowa kuma ta zauna lafiya.

Jinjina kai sarki yayi ya kalli sarauniya kamin ma yayi magana tace ni ban yadda ba.  Kasa kasa tace toh amma batun siyar wan a fasa kinji? Haba mata na ni daya. Hade rai tayi ta dauke kai. Yasan idan tayi haka toh tanannufin kai ka sani, kayi duk abinda zakayi don zaka hadu da ni.

Dan haka yasa cewa zasu yi aiki a kitchen kullum tare da sauran bayi har sai munira ta fito. In bata fito nan da wata daya ba an dauke musu aikin. Daga nan aka sallame su.
Munira kuwa zaman kadaici ya isheta Dan haka wajajen la'asar ta leko da kanta waje. A zaune ta kalli yarima yana Zane da yake bakin cau cau tace me kake yi? Dagowa yayi yace na jiki shiru na dauka bacci kike yi ai.

Girgiza kai tayi alamun ba bacci takeyi ba yace Zane nake yi. Katakau ta fito da sassarfa kamar zata kofa tace da gaske? mu gani nuna min. Wa ya koya maka? Tun yaushe ka iya? Yace wani tambaya zan fara amsawa? Tace zaka koya min? Yace me yasa zan koya miki? Yace saboda ina son yin Zane.
Yace toh AI kinyi karama, hararar sa tayi tace sai kace kai din ba karami bane abinda har a wasan mashi ma na fika?

Murmushi yayi yace ai dan na rainaki ne ban tsammaci kin iya sosai ba. Tace toh zancen ma kaga ka rena ni shiyasa bazaka bani ba. Yace toh tsaya bari na gama wannan zan baki. Girgiza kai tayi tace ban yarda ba yanzu zaka bani. Yace ki dai bari na gama nawa sai na baki hannu ta kai zata amshi alkalami da sauri ya daga sama.

Daddare ta fara amma yana zaune ma ya Mata tsayi Dan haka ta fara raruma hannunsa tana janyo wa kasa tashi yayi ya fara gudu a daki tana binshi ita a dole sai ya bata tayi Zane. Saboda rashin kuzari da ke tattare da shi ba  don ya so ba ya zauna yana dariya da sauri ta wacce itama tana dariya tace gashinan na kwace.

Yace AI yanzu zamu ga jagwalgwalon da kika iya bari inyi magana a kawo min Karin alli ki buya a bayan gado. Har yana shirin fita ta riko shi caraf kamar Wanda in ya fita za'a kashe shi yace me? Dan har ta bashi tsoro ganin yanda tayi tsurutsuru tace kar ka fita.

Yace me yasa ? Tace saboda akwai kamshi na a jikin ka. Dan Sosa kai tayi kamar zatayi kuka tace sanda yayabsadita ta yi min gargadi mantawa nayi kuma ni bana so a yi min hukuncin. Tausayi ta basa yace kar ki damu baza su ji kamshin naki a jiki na ba. Tace me yasa ? Yace saboda kamshi na yafi naki karfi kinga ni za'a iya jin kamshi na a jikin ki.

Kana hannunshi tayi ta shinshina tace haka ne kuwa kamshin ka yafi nawa da na mama na ma. Shi duk a surutun yaro ya dauki abin saide fa abinda bai sani ba shine its da gaske kamshin mutane kowa da nasa haka takeji Dan ta saka abin a kanta.

Dariya yayi ya boyeta kamin ya lekawa sauri wani bafade yazo Wanda abin ya bada mamaki Dan a sanin sa babu dogarai a bakin dakin shi amma ya zu ya gansu rututu. Abin da zasu kawo masa ya fada kamin ya koma. Munira da ke tsaye a bayan gado ya leka yace yanzu yaushe zaki koma wajen maman ki? Ko bakya kewan ta ? Turo baki tayi ttana shirin kuka tace inayi amma ina fitowa za'a dake ni.

Yarima yace karki damu gobe zan fitar da ke sai in fita sai mu dawo tare sai in nuna kamar sace ki akayi na taimaka miki. Tace toh AI baza'a fasa dukan ba. Yace zance kar su dake ki, tace da gaske? Ya daga kai washe masa baki tayi tana mikewa mai kawo tawada ya shigo hakan yasa yarima ya danna kanta kasa kamin ya kalli bafaden yace kamin ka shigo sakin mutum ka nemi izini. Bafaden yace an gama. Yana fita ya rufe kofa yaji Muryan munira tana cewa toh ni ka ban nima nayi zanen da sauri ya sa aka rufe dakin yarima sannan ya nufi fada sai haki yake... 

SALAM YAN UWA BARKA DA WANNAN LOKACIN INA JIRAN COMMENTS DINKU.
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top