CHAPTER 11
Jinjina kai yayi yace ina MUNIRA? yanda Kira sunan kawai kasan kashin munira ya bushe. Cikin sanyi jiki khadija tace tayi bacci Dan ta kare ta domin kuwa bata yi bacci ba. Kara bata rai yayi yace mutuniyar banza ta lalata rayuwar wasu shine zata kwanta bacci? A taso min ita.
Bude baki khadija zata rikewa akan yayi alfarma ya yafewa munira ko zuwa gobe ne tunda yanzu tayi bacci ya daga Mata hannu yace babau ruwanki khadijatu, ki kula da abinda ke jikin ki kawai.
Sadiya ce tayi sauri ta shiga daki munira ta samu lungu ta rakabe sai kuka take sharba Dan bata taba ganin ran mahaifin ta ya baci haka ba. Sadiya ne tace kina zuwa ki fara bada hakuri kinji ko? Girgiza kai munira take tana fadin duka na za'a yi yaya sadiya duka na za'ayi yanzu idan na mutu wa zai Kula da mama ta?
Muryan sarki sukaji yana fadin in Baku fito da wannan makirar ba zan shigo da kaina da sassarfa sadiya ta janyo munira dake kafewa tana kokarin saka burburwa. Sadiya ta mika ta tare da ja baya. Munira fuska shabe shabe da hawaye tace ya kai mahaifi na ka tausayamin ka sanni ka San hali na bazan taba yin wani Abu dan na Saba maka ko na tozarta gidan nan.
Kaine shaida yadda dazu nayi wasan mashi kawai Dan na rike mana mutuncin mu. Murmushi yayi tunowa da yadda sukaci kamin ya sake daure fuska yace toh munji tunda kinyi min zakin baki da bulala 30 zansa a miki amma yanzu na canja shawara bisa adalci da tausayi na da kuma ganin kankantan ki da kishin gidan nan da kike yi na rage miki zuwa bulala 10 Wanda za'a miki gobe da safe sannan kiyi bayin duka bishiyoyin da ke gidan nan.
Dafe zuciya khadija tayi tace mijina ka tausaya mana ka duba yarinya ce fa bulala 10 in ta mutu fa. Yace toh naji ni matsalata da ke kin fiya abun tausayi khadija nayi sassauci ayi Mata bulala 3 khadija tace amma..... sumbatan goshinta yayi yace Dare yayi jekiyi bacci karki damu kanki da shiririta yarinyar nan. Kinsan shi ice tun yana danye ake lankwasa shi.
Idonta cike da hawaye tayi murmushi tace haka ne Allah yayi wa zuri'a albarka. Saida safe yace saida safe sannan ya tafi bangare sarauniyar sa.
Khadija tace kin gani ko? Kin gani ko munira kullum ina fada miki kar kiyi fice kar kiyi fice amma kinki ji yanzu gashinan bularki 3 zaki karba.
Fashewa munira ta sake yi da kuka ta kwanta a cinyan maman ta tana shafa cikin tace kanina kaga abinda ake min ko? Idan ka girma ka zama gwarzo duk Wanda zai taba ni ka fasa masa hanci. Dariya sadiya tayi tace kaji babbar banza kanin ki ne zai kare ki? Tashi tayi taje ta kwanta.
Da hantsi sarki yasa a kamo masa munira bayan kamar minti 5 bafaden da aka aika yace mahaifiyar ta tace tun asuba ana neman ta ba'a ganta ba an aika dogarai sun duba gidan gaba daya basu ganta ba. Da sauri ya Mike ya fito farfajiyan gidan sa yace a Kira masa Wanda sukayi gadi jiya.
Da gudu suka zo su 15 aka ce shin a cikin su akwai Wanda yaga gittawan munira ? Kowa yace gaskiya bakiga fitan ta ba haka yasa a take ya bada umarni a zana kamannin ta a lika cewa ana neman ta. Wata me aiki ce taji ana zancen tace Allah ya ja zamani nidai jiya tsakar dare na fito na ga gittawan ta ta nufi yamma amma ban San ita bace sai na dauka bacci ne yasa naga hakan.
Sarki yace bangaren mutane biyu ne a yamma. Inda yarima yake sai bangaren marka Wanda sunce basu ganta ba. An duba bangaren yarima ? Suka girgiza kai yace muje. Shiga sukayi bangaren yarima yana zaune jingine da gini Wanda ya bokare bayan sa da bargo.
Gaisawa sukayi da baban munira yace masa ya jikin yace Alhamdulillah ya ji sauki kawai de bayida kwarin jiki ne. Sarki yace toh masha Allah dama wannan yarinyar ce nace ko ta shigo nana saboda bamu ganta ba kasan halin yaro. Yarima Umar gyara zana yayi ya sake jingina da bangon sosai yace wacce kenan ? Sarki yace Allah yasa ka gane ta yarima, munira muke nufi. Yarima yace wacece munira? Sarki yace wacce ta baka kwaron nan.
Yarima yace ai mace me kamar maza kenan AI ni rabona da ita tun lokacin ace Mata tazo ta dubani ba sai taji tsoro ba abzwn Mata komai ba AI da hannuna naci kwaron. Cikin washe baki sarki yarima ka fiye kirki tuba Mike a dai kara hakurin abinda ya faru. Gyada kai yayi yace ni zan koma in kwanta ko.
Da sauri sarki yace kai maza kuje kar mu dami yarima toh yarima Allah ya kara lafiya. Kwanciya yayi suna fita da yaji ya daina jin motsi su ya Mike da sauri ya bankada bargon ya bude. Ga munira nan tayi tsuru tsuru da ido duk ta hada gumi. Fashewa sukayi da dariya da sauri ta sauko ta dauko kujera da ke gefe ta ajiye tare da zama.
Abincin da aka kawo masa ta bude suka fara ci yace wai me ya faru ne ake neman ki? Me yasa kuma kika gudu nan? Turo baki tayi tace ni karka dameni da tambaya yunwa nake ji tana shirin daukan nama. Daukewa yayi yace in baki fada min ba baza ki ci ba ta ce to naci zan fada maka.
Jiya ne baba na yaje dakin mu wai sai anyi min duka 10 da kyar ya tsaya a kan za'ayi min 3 Dan haka tun cikin dare bayan mama na ta yi bacci ni da yaya sadiya muka yanke shawara zam gudu da asuba saboda in aka rasa ni za'a nemeni amma tasan bangaren ka ne baza'a zurfafa bincike ba saide mama na tun da asuba bata koma bacci ba. Kuma idan tasan zan gudu baza ta yarda ba.
Jin takun dogarai domin su kamo ni yasa ta mike don ta rufe jikin ta anan ne ni kuma na Sami dama na fita da gudu daganan dai nasan yadda mukayi da yaya sadiya haka ta fada musu Dan munyi idan na gudu zata ce tun dare basu ganni ba. Sannan zatayi kokari ta hana mama ta yin magana.
Bayan an tafi sai ta fada Mata cewa ina cikin koshin lafiya kar ta damu ni kuma lokacin ne na gudu na shigo dakin ka kafin nayi maka bayani muka jiyo shigowar su shine nace ka taimaka min ka biye ni kuma ka boye ni a inda baza'a taba nema na ba kaga yanzu in zaka tafi sai ka tafi da ni AI babu Wanda zai hana ka ko? Ajiyan zuciya ya sauke yace aiki ja ba dai surutu ba. Ni in kinaso in tafi da ke sai kin rage surutu. Tace toh na yarda yanzu dai zaka iya bani nama na ko sai nayi kuka?
Yace shikenan sai su tafi da ke ba ni kuma...... kofar da aka turo yasa suka jiyo lokaci daya suka zaro ido naman da ke hannun munira ma sanda ya fadi.
TASHIN HANKALI AN GUDU BA'A TSIRA BA KENAN. DUK WANNA SAKA TA MUNIRA KAR DE AN WARE SHI? ME ZAI FARU A GABA?
NASAN KOWA YAYI FISHI AMMA YA NA IYA MURA CE TA KAMANI TA SAUKE MIN ZAZZABI SAI YAU NA DAN JI SAUKI ALHMDLLH NACE TOH BARI KO BA YAWA A SAMBADO MUKU.
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top