CHAPTER 1
MASARAUTAR UNTO
Mai martaba kayi min afuwa kayi min rai karka kashe ni. Cikin izza sarki da kansa ya sauko zai falla Mata mari yana fadin mutuwa ta wajabta a gareki maciyiya amanar sarki.
Kabir ne ne ya rike hannun sa yace mai martaba kazantar ta yafi karfin ka daura hannun ka a kanta. Najasa ce!
Da kafa kabir ya hankadeta tare da fadin dogarawa ku kamata ku daure ta kar a bata ruwa na awa talatin sannan a dinga Mata bulala 10 bayan awa daya bayan awa 30 din ku daba mata mashi a ciki ku tabbata ta soki mahaifarta ya fito a zubar da shegen da ke cikin jikinta a tabbatar ta fadi waye ubana idan ba haka ba a dinga yankan naman jikin ta har sai ta fita daga haiyacin ta!
Kamin ya rufe baki yaji an dauke shi da wani zazzafan Mari Wanda yasa har sanda ya rufe idon sa. Cikin kururuwa yarima Umar yace naga Wanda ya isa ya taba ta. Wannan cikin nawa ne kuma banga Wanda ya isa ya taba min jini ba!
Shiru wajen ya dauka domin kowa ya sha jinin jikinsa cikin rawar baki mai martaba yace kai Umar me kace? Yarima yace Allah ya kafarta wa ABBA wannan cikin nawa ne. Zaman dabas mai martaba yayi tare da sauke kai. Bayan wasu dakinku cikin wani kururuwa yace SHIMA KU KASHE SHI!
🍁yadda abin ya kasance🍁
GARIN BANTY
Ruwan wanke wanken da aka watso masa ya sa ya mike tare da gyara zaman tarkacen da ke jikin sa, da kaga fuskan sa kasan ba haushin abin da akayi masa yaji ba kawai de ya gaji ne da irin abinda ake masa cikin garin.
Matar da ta watsa masa ruwan ne tayi masa nuni da kofa tare da fadin abar min kofan gida na gaiyar tsiya kawai. Tare da rufo kofar ta da karfi.
Kamar ya bude ya fada Mata bakaken magan ganu amma sai ya Share kawai ya fice daga zauren yana gyara rawanin dake kansa Wanda ya rufe har fuskan sa.
Ruwa ake zabgawa garin ya yi baki hakan ne ma yasa ya shiga gidan domin ya samu mafaka. Waigawa yayi gabas da yamma kudu da arewa amma ba mahaluki ko daya.
Hakan yasa ba tare da damuwa ba ya cire rawanin da ke kansa domin ya fara yi masa nauyi. Gashin da na gani ya sauko zuwa kafadan sa yasa na fara tunanin ko daga irin su Sudan yake?
Amma da na kalli fuskar da yanzu bata dauke da rawanin da ya rufeta sai naga ashe mace ce. Mikewan da tayi yasa rigan ta ya Dan kama jikin ta ya kara tabbatar min da mace ce saide Sam in bakada lura bazaka fahimta ba.
Haka taci gaba da tafiya bayan tayi gyale da rawanin nata har ta dangana zuwa wani shagon me shayi.
Gefen rumfan ta samu ta rakabe Dan ta San duk yadda zata roke sa da kyar ne ya barta ta samu mafaka.
Daya daga cikin masu shan shayi a wajen ne yace habu taimakawa baiwar Allah nan mana kaga ruwa sai duka yake Mata. Habu na kallon ta ya ganeta yace wannan tsiyar zan taimakawa? Masifa ce fa ni yanzu haka da ta zo gefen shagona kar ta janyo min abun da yafi karfi na.
Wani daga cikin Wanda sukayi mafaka a shagon ne yace haba habu kasan de mutane da karyar banza ni fa ban yarda da abinda ake fada a kanta ba kawai ace Dan mutum na raban Abu sai masifa ta fada kan abin?
Gaskiya da.... kamin ya karashe zancen sa wani katako dake saman sa yana reto ya fado masa, 'kusan da ke jiki ta yagi gefen fuskan sa. Salati kowa ya saka habu yace toh ai gashi ka gani yayin da yake yago wata tsimma.
Mutumin da kansa ya Mike ya fita zuwa inda yarinyar take yace ke tashi , tashi ki bar nan shegiya har ina tausaya miki ashe ke alkaba'i ne bar nan wajen ya jefeta da takalmi. Mikewa tayi ta tabe baki Dan ita a wajen ta ba faru bane saboda tunda ta tashi haka ake Mata dan haka bata daukeshi a matsayin wani matsala ba.
Kawai juyawa tayi tace " ta kare a kanku." Sanda tsikan jikin sa ya tashi saboda jin muryar ta da yayi. Sai tayi sati kalma 1 bata hadata da mutum ba Dan haka mutane kalilan ne suka taba jin muryar ta a garin.
Irin mutanen nan ne masu murya kamar ta yar tsana mai ban haushin nan. Wanda yawanci suna da cakwaikwaiwa su cika wa mutane kunnen su da zance.
Komawa rumfan mutumin yayi yana sa kafarsa kawai wuta ya kama teburin akayi akayi a kashe wutan nan amma kamar rura ta ake ga ruwan sama da ake zabgawa ma ya isa ya kashe wutan amma wutan nan bai mutu ba sanda ya cinye komai a wajen nan Abun ka karare.
A kasa mai shayin ya kwanta yana burburwa kamar zararre yana yin Mata Allah ya isa da gudu ya matsa lokacin da iska yayi majaujawa da wani gungumin itace. Wannan mutumin da ya kore ta ne yayi saurin rufe masa baki yace yi shiru habu naji ance ba'a yi Mata allah ya isa masifa ce take fadawa mutum fiye da Wanda ya same shi.
Ita kuwa bata ma San anayi ba Dan tayi gaba abin ta, ko da tabi ta gaban gidan da aka kore ta dazu samu tayi ruwa ya ture musu gini ya fada kan yaro.
Sauya hanya tayi abin ta tana Dan sautin ta tana tafiya domin karasawa gidan ta kuma inda take rayuwa ba tare da an shiga hancin ta ba.
Ruwa ya fara tsagaitawa hakan yasa jama'a suka fara Dan firfitowa. Wasu yara da aka aika su sayo itace tayi karo da su yayan yana ganin ta ya gane ta hakan yasa ya rike kanin sa suka fara sassarfa.
Kanin ne yaci birki yace Mata yaya babba wannan kwari da baka ne a jikin ki? Daga kai tayi cikin jin dadi yace kina da gwafa? Sake daga kanta tayi. Yayan sa ne ya ja hannun sa yayin yaron ke cijewa yana fadi yaya me gwafa zaki ara min kwari da bakan ki?
Sake daga kai tayi yayan sa ya make keyarsa yace ba ka da hankali ko wannan in ka bari kuka kara hada hanya sai ka mutu. Tana taba mutum yake mutuwa karka kara Mata magana. Kanin yace amma ni ina son ta. Ban taba ganin ta ba, kodan ni yaro ne shiyasa bana yawo balle na kalle ta.
Tabe baki kawai tayi taci gaba da tafiyar ta yaron yana fada Mata yaya kizo gidan mu wata rana muyi wasa. Basuyi wani tafiya mai nisa ba yayan ya ji sa cikin wani rami lintsum yasha ruwa kuwa sosai. Da kyar aka ciro shi lokacin har ya fita daga haiyacin sa.
.......
Lokacin da ta isa wajen gari wani murmushi tayi ga iska me kamshin kasa da take shaka wani zomo ta dauka tace nanne kinyi kewata ko? Yau kinga ban dawo da wuri ba in fada miki ruwan nan ne ya tsare ni a hanya. Mutanen cikin gari suka dinga yi min wulakan ci ban San sanda nace tsiya ta kare a kansu ba.
Tsintsaye ne suka fara saukowa jikin ta suna bin ta. Tace abokai na sannun ku fa muje gida naga me kuka kawo min toh.
Ci gaba tayi da basu labarin abubuwan da ta gamu da shi daidai lokacin da ta shige cikin kogon ta sannan ta zauna tana fadin in takaice muku yanzu haka ana ambaliyan ruwa a garin.
Ko wani dabba kukan sa yayi Wanda ke nufin suna dariya ajiye zuciya tayi tace yau da na shiga kunga abin da na samu.
Yanzu zan iya girki cikin sauki. Bude buhun ta tayi Wanda ba na leda bane irin na kaban nan ne ta ciro tukunyan kasa.
Duk dabbobin matsowa kusa sukayi kowa yana kallon tukunyan masu hannu suna tattabawa. Dilan ta ne yazo ya kwanta a cinyan ta. Shafa jikin sa tayi tace zul ka tashi daga bacci? Hamma yayi tare da kallon tukunyan ita ma ya kalleta.
Tace nasan dama kowa tambaya ta zaiyi. Naji ance sunan abin nan tukunya kuma abin ci ake dafawa dashi ba yadda muke ci danye ba. Kallon ta suka cigaba da yi alamun basu gane inda ta dosa ba tace mu hada wuta ku gani sanda nake karama na San shi amma na manta sai yanzu na sake gani
Bayan kowa ya watse an tafi hado itace tace ma zul wato dilan ta "yau abinci dayawa aka kawo?" Yace Mata eh amma kamin ya dauko yana so ya tambaye ta. Yace ta koyi maganan mutane ne da har ta iya cewa wannan mutumin tsiya ta kare a kansu? Dan shi a sanin sa TOH kawai ta iya fada. Tace ah ah kawai suna yawan fada Mata hakan yasa itama ta fada musu dukda ta Dan fara koyan magana.
Zul yace yanzu kam tana gane duk abinda suke cewa ko? Tace eh. Kuma na gano wani Abu ashe dalilin da yasa kowa baya son na shine ina da.....
ALHMADULILLAH ! CHAPTER 1 YA ISO TOH FA KU BIYO NI DAN JIN DALILIN DA YASA BA'A SON TA DUKDA DAI KUN GANI TOH AMMA ME YASA DUK ABIN DA TA RABA IN BAI MATA BA SAI YA SAMI MATSALA?
KU RIKE HANNUNA KYAM DAN JIN ME YASA TAKE RAYUWA CIKIN DABBOBI KO DE ALJANA CE? SHIN KUN TABA JIN LABARI IRIN WANNAN? MENENE HALAKAR TA DA SARKI DA YARIMA DA YASA NA SAKOTA A FARKON LABARIN NAN?
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top