CHAPTER 90

DAN ALLAH KARKU MANTA DA FOLLOWING DINA SECOND BIYAR KACAL ZAI DAUKA.

RECAP

Yafe Mata kowa yayi daddy yace batun na aura miki Wanda naso bai taso ba ki naimo miji dai amma kafin nan ya kamata nasani SHIN KIN TABA YIN ZINA A YAWACE YAWACEN KI?

CONTINUATION

Shiru parlourn ya dauka kowa ya tsime yana jiran Ansar da zata bayar girgiza kai tayi hakan yasa kowa ya saki numfashin da basu San sun rike ba.

Alhaji yace toh masha Allah ai abun yazo da sauki. Mikewa tayi zata tafi inna ta kalli bushra tace uwani baki ga baki bane? gaishesu tayi zata fita sabir yace ABBA inada magana.
Daddy yace toh muna jin ka. Yace dama idan babu matsala ni naji na gani inason in aure ta. Kallonsa kowa yakeyi daddy yace ka tabbata ? Yace eh. Daddy yace toh ke kinji kina sonsa? Tace ABBA indai ya maka nima yamin daddy yace toh kai sai ka turo manya ko? Yace ABBA AI banida su yaya mace kadai gareni. Daddy yace toh fa toh yanzu yaushe kake ganin za'a daura auren? Caraf bushra tayi tace yanzu ma yayi. Salati inna ta rafka tace riko sai jalla jalalu. Toh AI shikenan.

Atake a wajen aka daura auren akan Rabin albashin sa wato 10K yazeed ne yace ni kuwa kamar na sanka ko? Yace kwarai kun sanni. Ai nine............

Bayani ya tsara masa yazeed yace Allah sarki Allah ya tsare na gaba ya saka maka. Sabir yace no wonder lokacin da naga yar uwa naji kamar na San ta.

Daddy ne yayi ma mama magana a kunne fuskarta ya Dan canja amma da ta kalli mom sai ta sauke ajiyan zuciya ta gyada kai alamar yarje wa.

Kallon yazeed yati yace Alhaji yazeed idan BAZAKU damu ba naga auren nan gwanin ban sha'awa zan so nima inyi wuf da mahaifiyar ka.

Dariya kowa ya fashe dashi abin kamar a wasa suma a zaman nan aka daure su Alhaji sai washe baki yake yi wai shima a dole ango.

Sahir ne yace toh wai nifa ban gane ba naga sai overtaking akeyi anata aure aure toh kawai ayi namu a huta mana zayya tace kasan dalilin da yasa nake sonka? Girgiza kai tayi tace saboda kanka yana ja sosai. Maketa inna tayi. Akace toh marmarza sahir da safwan ku ciro duk abinda ke aljihun ku ku ajiye. Daga nan aka daura auren daddy yace a Nemo nana da kayai lemo ayi yar karamar shagali.

Inna ke ta kokuwa da cinyar kaza Dan ya Abubakar yace kakus kawai ki hakura da naman nan kin tsufa fa sai kin cire hakori kizo ki hanamu bacci da daddare. Dariya aka yi tace haba mai gida (yaron me sunan baba ne) harda kai ake haduwa aci mini mutunci?
Safwan yace kakus karya kikeso yayi?

Yazeed ne yayi gyaran murya yace inada magana yanzu dai zan bar kowa anan domin banaso ayush tasan cewa mun dawo hankalin mu Dan haka daga ni sai matata sai sahir da safwan da iyalan su ne zamu tafi Jamal kaima zamu tafi tare tunda dama tun da a gidan mu kake amma kar kayi kuskuren nuna kauna ko tausayi ga zakiyya sauran kuma abar mana ni da ita(wato minal).

Sai bayan la'asar sannan suka nufi gida bayan anyi hotuna ran kowa wasai duniya tayi musu dadi.

🌹🍀🌹🍀

Ayush zaune da uwar ta a parlour hankalin su kwance suna kallon film Dan basu da Aiki sai kallon fina finan horror da vampire da BL da GL da sauran su.

Safina ne ta fito taci leshi tana taku jikin nan yana motsawa ta ko ina tace an dai ji kunya. Duk wannan shagali da kuke dazu harda tara kawaye aikin banza ne Dan ko ajikina bari kuji. Kitchen ta shiga ta dauko madara da Kofi.

Sallaman su yazeed yasa hankalin su yayo bakin kofa. Dum dum kirjin su ke bugawa. Cikin tsoro ayush ta hau bari ganin minal biye da yazeed. Mummy ce tayi kokarin cewa son har ka dawo kenan ? Ashe ma tafe kake da amaryar.

Murmushi yayi yace mummy ga inlaw dinki. Ayush ya kallah yace sis ya kika ga matar tawa? Cikin yake tace wow gaskiya tana da kyau. Safina kuwa kasa tsayuwa tayi hakan yasa tayi wuf ta koma daki.

Tana rufewa ta sauke ajiyan zuciya tace kan bala'I wannan AI ta kera ni a komai da alamu ma na fita shekaru, ya zama dole na dage idan ba haka ba da matsala.

A waje kuwa ayush ne ta riko hannun minal ta zaunar da ita yayinda take lura sosai da yanayin yazeed amma taga babu sauyi. Sahir ne yace aunty my baki ga amaren mu bane?

Dariya tayi amma da ka ganta kasan a firgice take tace kuma karde auren aka daura yau ? A ah ya naga safwan ma da wata me kama da matarka? Yazeed ne yayi caraf yace AI kinsan dama yar matan tawa zai aura kuma yan biyu ne yaranta sannan itama tanada twin sister(ya fadi hakan ne domin ya kawar musu da shakku tunda yanzu akwai bushra ko suna tunanin minal ne zasu daina)

Mummy tace masha Allah kace kawai ruwan jikoki yan biyu za'a dinga min? Murmushi yayi irin yaji kunyannan.
Ayush tace sis ya sunanki cikin duniyar da kai minal tace nana. Ayush tace masha Allah nana sannunku da zuwa family din mu.

Yazeed yace toh mummy bari mu shiga daga ciki tace toh ba matsala Dan albarka.
Suna wucewa ayush ta rugo da gudu har tana Tuntube ta zauna a gefen mummy tace mummy minal ce fa. Djngure Mata kai tayi tace kiji banziya ba mugu yace daga ta aure shi zai tuna komai ba ? Ke banda shashanci bakiji yan biyu bace ba ma? Kuma yaran nan nata ai sunyi shekara 18 (su zayyan sunada girman jiki hakan ne ya cika musu ido)

Ke kinsan tabar gazar da mukayi musu bazasu yi mana da sauki ba da sun tuna ayush tace wannan gaskiya ne. Amma dai zan sa musu ido sosai.

Umma hani ce ta fito tana fadin naji hayaniya karde har sun iso ina bayi? Ayush tace toh sannu munafuka sun iso sai akayi yaya? Umma hani tace Allah huci zuciyar ki shugaba ta tambaya kawai nakeyi.

Mummy tace dallah ki koma daki ganin ki kadai yana sa ni inji kamar zanyi amai.
Simul sumul ta koma tana shiga tace ma zakiyya sun iso fa kuma ina ji a jikina wahalar mu ya kare.

A dakin su yazeed kuwa suna rufe kofa ya kara rungume ta. Kawai sai ya sake Mata kuka cikin mamaki tace haba kai kuwa da girmanka? Yace kewarki nayi sosai.

Murmushi tayi tace in fada maka wani Abu kallon ta yayi yace me ? Jan hannunshi tayi ta zaunar dashi a bakin gado ta kwantar da kanta kirjin sa tace "YAZZY BABY" wannan karan ita ta fara hawaye shi kuwa cewa yake sake fada inji tace yazzy baby yace banji ba Dan Allah maimai ta. Tace yazzy baby Kankameta yayi yace Allah ya isar mini da aka rabamu.

Kuka take masa harda majina yace toh sarkin shagwaba kin girman ma baki canja ba ko? Ni dagani in cire babbar rigan nan. Tace indai ins tare da kai toh bazan taba girma ba kuma har mu mutu kai yazzy baby na ne. Sumbatar goshinta yayi yace me ya samu zakiyya? Hawayen fuskar ta goge kamin ta zayyano masa abinda ya samu zakiyya take ya Kira mashkur ya fada masa shi kuwa yace AI wannan me sauki kaza zaku siya ku canja Wanda akeyi Mata dashi shikenan zata warke yazeed yace toh mun gode sosai yaushe zaka zo? Yace gaskiya ba rana saide ku ganni kawai.

........

A dakin su sahir kuwa suna shiga ko ina kayan sa ne da ya watsar yau da safe fara tattare dakin zayya tayi tana babatu tace kaide wallahi anyi kazami, la duba dakinka kamar bola sai an.......

Finciko ta yayi ta fado jikinsa yana kallon bakin ta yace waye kazamin? Turo baki tayi tace toh ba kai bane kake..... kasa karashe tayi sanadiyyar peck da ya Mata a lebe. Zaro ido tayi tace dama halsey ta fada min ashe gaskiya ne ? Cikin rudewa yace me? Tace wallahi shocking naji. Tsaki yaja ya raba jikinsa da nata sannan ya fada ban daki tace kai ka jiyo bani yadda muyi Abunnan har sai nayi shekara 18. Batasan ya jita ba Dan haka yace mu zuba mu gani.

..........

A dakin su sahla kuwa ashe kunya kunya nan a fili ne amma tafi zayya sanin me takeyi dukda ko itace usaina. Safwan kawai daga Dan tabata kadan ganin yarinya ne yanaso ya daga Mata kafa kawai ta kama masa wasu irin salo da badan ya dage ya kwaci kansa ba da ya rasa sallah magrib.

Bayan Isha'I kowa da kowa zaune a dining room, mummy ta kwala ma umma gani Kira fitowa tayi da sauri minal ta kafe da ido tana mamaki ko itace ko ba ita bace. Murmushi ta Mata wanda ya tabbatar Mata da itace.

Minal tace sannu baba umma hani tace yauwa sannu sunana umma hani. Murmushi minal ta sake yi mata. Mummy tace kicewa masu aikinnan su kawo mana abincin....

Juyawa tayi tana tafiya tana waige hakan yasa minal ta kashe Mata ido alamun ita ne bayan ta isar da sakon hajiya wajen zakiyya taje ta fada Mata. Hawayen jin dadi zakiyya ta fara dukda basu tabbatar da cewa minal bace Dan da ita ne da tabbas za'ayi tashin hankali.

Wajajen karfe Goma yazeed yace ma minal uwar yanzu ayush ke fitowa shan shayin dare daga nan sai tayi kallo Dan haka kiyi naki bangaren plan din. Sannan part dinnan da mutum ya doso shi ake alerting Dina..... haka ya faf fada Mata sabon tsare tsaren gidan sannan ta fita ta zuba mai a kofan side din zakiyya da mummy domin ko wani side part biyu ne dashi.

Wato side daya asali na mom da late ABDULMAJEED ne kuma shine mummy da ayush ke ciki. Sai na sahir da safwan sai kuma na minal da yazeed sai na guest har guda biyu.

Komawa tayi daki suka kunna CCTV footage din suna kallah.

Ayush kuwa fito wa tayi da niyar tasha shayi tayi leken asiri sannan tayi yanda zatayi ta hanasu yin wani Abu. Saide me ji tayi wani Abu ya kwashe ta sannan ya adana da kasa. 

A daki kuwa gani sukayi ayush ta fito cikin satin rigar bacci tana latsa waya. Suu mai ya kwasheta ya direta a gefe ihu ta fara waiyo kwankwaso na brother! mummy! Ku taimakeni haihuwa tazo min babu ciki.

Dariya su minal suka fara minal tace gaskiya mu fita Dan inga plan b ido da ido camera dinnan ba dadi. Yace duk abinda kikeso shine burina masoyiya ta.

Fitowa sukayi kowa da kowa ana fadin lafiya ? Itako sai fadi take ku tayani gani kwankwaso na yananan? Kokarin dagata mummy da minal sukayi amma ta like da floor. Yin duniya akayi a dagata Abu yace Sam mummy tace saide mu Nemo wuka sai a yaga pant dinki sai ki tashi shikenan.

Kuka ta fara wiwi  tana fadin waiyo Allah na mummy na shigesu! Mummy tace menene? Tace bazaki gane ba mummy! Tace toh menene? Tace shikenan tawa ta kare waiyo!waiyo!waiyo Allah na yasin banida Dan kamfai (pant)mummy tace na shiga uku ni salamatu yau za'ayi tonon salala.

Yazeed yace ma su sabir su koma daki zayya da sahla kuma su tsaya. Bayan sun shiga dakin yazeed yace sis kajama kawai za'ayi miki a cireki idan ba haka ba kuma toh saide ki kwana anan gobe likitoci suzo da karafuna a banbareki. (Yace karafuna ne Dan ya bata tsoro)

Tace wa ? ni shegiya inji Dan daudu kawai ku cireni. Zayya da sahla ne auka rike hannu yayinda mummy da minal suka rike kafa akayi sama da ita a lokaci daya.

Tace la ha'ila ha illallahu shikenan! Kun kun kasheni. Waiyo Allah sun kwaye min mazaunai.
Umma na sun kwaile min mazaunai naaaaa😭😭😭

OKAY BARI NA DAN DARA KADAN NE😁😁🤣🤣  DA FATAN KUN MURMUSA KUMA KUNYI DARIYA A WANNAN CHAPTER?

INA FATAN DUK SANDA KUKA TUNA KUYI MURMUSHI HAR BAYAN RAMADAN INDA ZAMU CIGABA DA GASAWA AYUSH GYADAA A TSAKIYAR KA YAYINDA MU KUMA ZAMU DARA DOMIN MU KARE LITTAFIN MUNA MASU ANNASHUWA DA FARIN CIKI.

INNA TANA MIKO MUKU GAISUWA TA MUSSAMAN TARE DA WASHE BAKINTA DA HAKWARA SUKA SOMA ZUBEWA😁😁

KUYI VOTING  DA COMMENTING SANNAN KUYI SHARING DOMIN WASU MA SU DARA.

KAUNATA GAREKU BUHU BUHU❤❤

Miss Untichlobanty 💕

DUBA SABON LABARI NA MAI  SUNA YARINYAR CE TAYI MIN FYADE

WANNAN GAJERAN LABARI NE DAYA FARU A GASKE. BAN CANJA SHEKARUN YARINYAR BA KO ALAKA BA,AMMA NA CANJA SUNA, GARI DA KUMA ANGUWA.

LUBABATU YARINYACE YAR SHEKARU 5 KACAL WADDA TA FARA DA TABA MA BABBAN SAURAYI DAN SHEKARU 27 JIKI KAMAR DA WASA ABU YA GIRMAMA. SHIN WAI ME ZAI FARU NE? KO ALJANU NE DA YARINYAR? BUKATAR DA NAMIJI A SHEKARU BIYAR BA ABINDA MUKA SABA JI BANE. SAIDE AYI AIKIN KARFA KARFA TOH FA ANAN ITACE TAYI.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top