CHAPTER 88

RECAP

Washe gari tana shigowa floor dinsu taci karo dasu yazeed secretary dinshi ne yace ms mina da alamu hiran jiya yayi dadi tunda birthday din saurayin ki ne. Kwal....datseshi tayi ta hanyar cewa rike zancenka, ko ganin fuskarsa banyi ba. Sannan tabi bayan yazeed tana mai murkutsa baki.

CONTINUATION

A gidan mai nasara kuwa maman su ne tare zaune suna hira da bushra take cewa bushra ya kamata kema fa ki fara aikinnan kinga yar uwar ki minal....
Bata karashe ba sanadin bata rai da minal tayi tace ba yar uwata bace.

Maman tace munji kinga dai yanzu a jeedmar take aiki ya kamata kema ki nemi aiki. Zama tayi tace mom jeedmar kikace fa. Tace eh shi mana. Tsaki taja tace dama nasan ba'a sona ya za'ayi a nema Mata aiki anan ni a hanani ? Mama tace kinaji tace uta Zata Nemo aikinta yanzu zakice an nema Mata.

Tace babu yadda za'ayi ta samu aiki saide in jikinta ta bayar. Sahla yar biyun zayya tace AI uwar mu ba irin su oo bane. Cikin mamaki dukansu biyu suka kalleta. Bushra ta Mike zata daketa tana fadin keda ko usili bakuda shi sahla tace kina duka na zan fada ma daddy duk abinda kika ce akan ummi na, wallahi karkiganni shiru shiru banda kyau Dan haka bazan juri zagin uwata ba daganan ta shige daki.

Sallama aunty jalila tayi shameela na biye da ita. Tace yar karamar kanwata lafiya kike haki haka. Mama ne tace ma shameela taje wajen feena a daki zasuyi magana da mamanta. Amma kun Santa da gulma Dan haka labewa tayi.

Sahla ce ta bude kofa ta hangota Dan haka ta Nemo zare a hankali tasa Mata a jiki. Ihu ta kwalla kowa ya fashe da dariya ashe suna sane da ita.

Aunty jalila tace mummy ga me aikina fa shekarar 5 muna tare sai yau kuka hadu. Sai a lokacin umma ta lura da kyakkyawar matar dake tsaye a baya tana kalle kalle yayinda take zubda kwalla. Mama tace baiwar Allah shigo mana lafiya kike kuka? Zauna anan gefena.

Zama matar tayi suka gaisa umma tace lafiya dai ko? Matar tace kawai gidanku ya tunamin ra rayuwata ne. Nann ta labarta musu rayuwar ta amma ta kasa fadan family name dinta. Yin duniya akayi ta kasa fada ko ymta kwatanta inda za'a samesu.  Matar nan ba kowa bace illa MOM mahaifiyar yazeed. Security dinnan ce ta taimaka Mata ta fitar da ita daga gidan mahaukata.

🌹🍀🌹🍀

Ya Abubakar zaune da matar sa laila  da yaransu guda biyu a parlourn su inna sun kawo musu ziyara.
Tunda dama ta rasa kowa nata tun kamin su mance komai yanzu a nasu tunanin ita Marai niyace gaba da baya domin ko sun mance da wani Dan uwanta goje Wanda ya kasance miji ga ayush idan Baku manta ba.

...........

Direct company ya nufa wajen baban sa ya samu minal da yazeed da secretary sunata aiki. Shigowa yayi babu knocking suna hada ido da minal yaji kamar akwai alaka mai karfi a tsanin su. Baisan yadda akayi ya gaishe ta ba.

Yazeed yace kai secretary taba min goshin sa ko bayida lafiya ne? Dariya yayi yace lafiya nake. Secretary tace ms minal wannan shine sahir, future president wato babban Dan yazeed.  Murmushi tayi masa tace nayi farin cikin ganinka zama yayi a gefenta yace na fiki farin cikin ganinki. Yazeed yace kai banson shirme tayi kama da sa'ar la ne. Wato dama abinda ake fada min gaskiya ne ? Muje. Sahir yace ina zamu? Yazeed yace gidan ka.

Wani kulululu yaji a cikin sa, take yayi kokarin kawar da maganan amma yazeed yace Sam kallon minal yayi yace muje ko? Sahir kuwa Message ya turawa zayya akan ko bata gama ba tabar gidan,Amma me rana can tana shirme.

A cikin mota sahir ya matso jikin yazeed cikin kunne yace daddy dama PA dinka ce matar ka. Yace me kakeso kace ? banason kwane kwane. Yace dadi na dakai saurin gano ni so nake ka AURETA. Mangare shi kadan yazeed yayi Yace hmm yaro man kaza kaida kakeda mummy safina me zakayi da sabuwar mahaifiya? Kaga dai safina.. hannu sahir ya daga masa yace bana bukatar ji. Dariya yazeed yayi yace wai me yasa bakason safina ne? Duk maganar nan da suke minal bataji.

Cikin daga murya kuma hawaye na zuba a idonsa yace saboda bata son mu, ta tsanemu ra wahalar damu.....nan ya fadi duk abinda ke cikinsa rungume sa kawai yazeed yayi. Ashe kangin da yaransa suka shiga kenan ? Toh lallai zaiyi maganin safina. Zaiyi maganin ta ne ta kasa kasa yadda tayi masa zalinci kasa kasa.
Hakan kawai minal taji kamar ta rungumeshi dukda cewa bata San shi ba.
Daidai lokacin suka iso gidan suna bude kofa sukaci karo da zayya tana wakar hauka tana rawa da mop. Yazeed ne ya kalli sahir yace me yarinyar nan take a gidan ka? Yace daddy aiki takemin.

Ita dai minal idan ba kuskure tayi ba toh bayan yarinyar yayi Mata kama Dana yarta zayya.
Murda kunnenshi yazeed yayi yace aikin kaniyar ka? Zukekiyar buduwa ce zata maka aiki? Hmm daidai kenan fadamin address dinta gobe goben nan zamuje gidan su. Yace me kake nufi dad? Yazeed yace auren ta zakayi kuma dole ne ba shawara nake baka ba. Sahir yace zan AURETA da sharadin zaka auri PA dinka. Minal kallon bakada wayo tayi ma sahir shi kuma ya Mata abin tausayi.

Shiru yazeed yayi tunda sun sha wahala a baya ya kamata ya auri wadda suke so wata kila zaiji sauki sauki. Kuma ai ms mina ma ba laifi tana burgesa. Wani lokacin ma dariya take basa.

Yace naji amma naku za'a fara sahir yace ina ? Naku dai ai cikin satinnan nakeso ayi. Minal tace nace na yarda ne? Gefe yazeed ya jata yace nasan kinji abin da yace dazu? Na Dan wani lokaci ne kawai tai maka min zakiyi in koya ma safina hankali zan biyaki.

Hararsa tayi tace banason kudin ka saboda sahir zanyi Dan karamin dariya yayi yace fadi gaskiya dama na Dade da gane kina crushing murmushi kawai tayi ta girgiza kai. Ashe dama mr yazeed yanada kirki? Cabdi za'ayi ruwa da kankara.

Wajen sa suka dawo sukace mun yarda ihun dadi ya sake Wanda yasa zayya juyowa tana fadin waiyo barawo!barawo! Bara.... bata karashe ba sanadin hada ido da tayi da minal. Tace um... ummi? Minal tace zayya?a tare suka tambayi juna me kikeyi anan?

Yazeed da sahir ma suka hada bakin wajen cewa kunsan juna ne? A tare suka sake cewa yata ce da kuma mamata ce.

Yazeed da sahir suka kalli juna kawai sai suka sa dariya. Maganar ido sukayi irin mutumi na a gida daya zamuyi aure fa.

Zayya ne ta kalli yazeed tace uncle? Kallonta yayi na Dan sakanni yace idan ba kuskure nayi ba boss lady ce ko? Tace uncle ashe baka mantani ba? Yace ina fa?
Wannan karan minal da sahir ne sukace kunsan juna ne? Nan zayya ta fada Mata ai shine Wanda ya taimaka musu lokacin nan godiya minal tamai. Haka kawai taji hankalinta ya kwanta da auren shi da zata yi koda zasu rabu batada asara dukda cewa babu rabuwa a lamarin ta ma.

Zayya kuwa tanajin cewa sahir Dan uncle ne ta yarda zata auri sahir ko ba komai zata bawa shameela haushi.

Haka sukaje bayan kwana uku suka nemi aure kuma cikin sa'a aka basu. Feena sai dadi takeji yayinda shameela da bushra kamar zasu fashe.

.......
Suna shigowa yazeed yace kowa da kowa ya taru a parlour akwai babban albishir. Cikin jin dadi kowa yazo umma hani ma haka ta turo zakiyya ta fito da ita Dan yanzu ta daina kokarin fadan gaskiya Dan bazata iya ba.

Maman ayush kamar da gaske tace son ya akayi ne naga kanata jin dadi ? Murmushin sa ne ya fadada haka kawai gaban safina ke lugude.

Ayush tace brother na kagu yi sauri ka fada mana mana yace da farko dai sahir zaiyi aure. Murmushi ne ya fadada a fuskar kowa safina kuwa cikin ranta tace toh sai akayi uwar yaya? A baiyane kuwa yake tayi tace finally Dana ya girma,Ko ba kai bafa. Murmushi yazeed ya Mata aranshi kuwa yace zaki San kin taba ni.

Zakiyya ma dadi takeji cikin ranta harda tsalle amma bazata iyayi a zahiri ba.
Yazeed yace na biyu kuma nima zanyi aure! Tsit parlour yayi ko allura ne ya fadi za'a ji karar ta. Safina tace kan bala'I toh ba a gidannan ba. Na rantse da Allah baka isa kayi aure ba harni za'a wulakanta? Ni safina. Cabdi! Hawaye ne ya zubo a idon zakiyya domin tunawa da yadda tayi wa yazeed lokacin da zai auri minal har yau tana nadama.

Yazeed yace ke a suwa? Mummy da ayush ne sukace fada Mata dai. Mummy tace aure dole bari kiji da na dole ya kara aure. Tafawa ita da ayush sukayi suna nuna kiyaiya karara. Yazeed ko mikewa yayi yana fadin asabar me zuwa daurin auren bayan wata daya za'ayi na sahir lokacin ana hutun makarantar su yarinyar. Kallan safwan yayi yace toh Alhaji saura kai ni da sahir munyi namu.

Sama ya haura sahir yabi bayansa safwan yace kai ku jira ni mana shima ya haura aguje yana tambayar Dan uwan sa sanda suka fara soyaiya bai sani ba.

Safina kuwa wani fadan suka kafa a kasa yayinda umma hani da zakiyya sukejin ransu wasai.

Koda suka shiga daki umma hani tace zakiyya naji dadi sosai da shugaba zai kara aure kefa kinji dadi? Kyafta ido tayi. Umma hani tace nasan kema kinsan gaskiya shiyasa ke daya nake iya tattauna wannan maganar ba tare da wani Abu ya sameni ba shiyasa na nayi nazari sai nake tunanin kodai lamarin nan akwai sihiri? Kyafta ido ta sake yi tace to indai haka ne zan Nemo ma shugaba magani. Shin kema sihiri aka miki ? Zakiyya bata kyafta ido ba tace ba sihiri aka miki ba? Ta kyafta ido tace ikon Allah.

Yau ta kama asabar ranan daurin aure kuma tun daga ranan da su yazeed sukayi tambaya minal bata sake fita aiki ba shirye shirye kawai ake dukda cewa ba wani shagali za'ayi ba.

Sahla ne ta shigo ta zauna a gefen minal da zayya tace ummi wai aure zakiyi ki barni anan ? Minal tace nima banaso in barki amma karki damu zan tambayi miji na idan ya yarda sai kizo mu zauna tare ko? Zayya tace AI ni akafi cuta ranan Monday fa zan koma makaranta.

A bangaren ango kuwa yasha shaddar sa ruwan madara sai kamshi take sha dukda ya haura shekara 40 hakan baisa kyawunsa ya dishe ba idan ma baka lura ba toh zaka dauka har yanzu Dan talatin da wani Abu ne.

Kirari aketa zuba masa yana ta kara kudi kamar bayaso. Yaransa na biye dashi gefensa kuwa Jamal ne sai ma'aikatansa Wanda suke shiri kamar su ya Abubakar. Luku kuwa bai samu zuwa ba saboda shi ke kula da company dinsu dake Cairo dan haka shida matar sa zaliha suna can saide kash gaba daya sun manta da minal. Akan sadaki dubu 100 aka daura auren saide ana gamawa kan yazeed ya Sara salati ya fara yana ganin dishi dishi sannan ya tuna komai da komai kamin ya fadi kasa a sume. Kamin kace tak, Jamal da safwan da sahir da duk wani Wanda aka yi masa tsafin sun zube a kasa hankalin jama'a ya tashi. Nan akayi ciki dasu aka kaisu part din daddy Dan nanne babu mutane.

Mom kuwa kamar yar gida haka ake Mata taci leshinta fess sannan ba'a wani sata aiki sosai. Suna zaune a dakin mama ana hira irin ta manyan Mata mom tace wai ni kam WANENE angon ne naji ana an daura auren Amma banji sunan sa ba. Mama cikin fadada murmushi tace yazeed ABDULMAJEED Umar ne atake mom ta Mike tana fadin shine wallahi shine. Akace shine me? Tace Dana shine Dana. Daidai lokacin bushra ta shigo dakin tana fadin mama ayiwa kawayen wannan yar rainin hankalin magana su fita a daki na. Yau kwanana biyar bana nan daga dawowa za'a bata min rai? Mom tace minal me kikeyi anan? INA YAZEED?

DON'T FORGET TO VOTE,FOLLOW,SHARE AND COMMENT YOUR THOUGHTS

LOVE YOU ALL💋

miss Untichlobanty 💕

20th April, 2020.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top