CHAPTER 86
RECAP
Cikin kakkaurar murya kuma kamar ya gaji da yin maganan yace idan akwai jagwalgwalon da kuke Kira kwalliya a fuskarki toh ki fita ko jarabawar baza'a miki ba idan ko babu to kalli gefenki na dama. Babu musu ta aikata hakan kujerace akai akwai laptop da kuma files guda 10. Yace kalli agogo karfe nawa ne? Tace 11:50 yace mun rasa soft copy na wadannan files da kike gani Dan haka so nake kamin karfe 12:45 ki sake typing duka sannan banason kuskure ko daya idan kuma bazaki iya ba toh KEMA GA HANYA!
CONTINUATION
Kallon files din tayi sannan tayi nazarin lokacin da aka bata indai aikin kwanciyan hankali zatayi toh kana bukatar awa biyu amma a kasa da awa daya akeson ta gama. Zama kawai tayi ba tare da tace mai kala ba, mamaki be ya kamashi da yaji karar keyboard. Ko shi da yakeda saurin aiki yana bukatar awa daya amma mace tayi tunanin zata gama a kasa da minti 55 ? Taurin Kaine kawai na Dan Adam.
Ganin saura mata minti hudu yasa shi yin murmushi faduwa dole. Itako garin sauri ta fice daga wajen Allah ya taimaka tanayi tana saving kokarin komawa tayi dukda ta cire rai saboda akwai file daya a gabanta amma me? Sai taga ga files dinnan gaba daya da me kuskure da Wanda yazeed din ya gyara wato wahalar banza yake basu daga karshe goge aikin zaiyi? Lallai ma mutuminnan. Ai in yasan wata baisan wata ba kaji tsohon nan fa ! Kofar file din tayi sai ta saka kuskure guda 1 daya saboda kar ya gane agogo ta kalla saura Mata second Goma sha biyu ta dannan control-save tace na gama. Yazeed dake Abu cikin wayarsa Dan ya sakankace faduwa zatayi ya kalli lokaci saura second 8. Abu biyu ne suka dira masa a lokaci daya mamaki da kuma kishi, yace karaso ki zauna. Hakan akayi amma me? Yana juyowa suka hada ido take annurin fuskarta ya dauke yayinda a nitse kamar yau ya fara ganinta yace miss mai nasara can you tell me why you want to be my personal assistant? (Ko shin zaki iya fadamin dalilin da yasa kikeso ki zama personal assistant dina?) Tabe baki tayi tace personal assistant na president ba naka ba tunda bansan kai bane president din, amma yanzu da na sani..... mikewa tayi tace kaga tafiya ta gobe zan kawo takardan barin aiki. Har takai bakin kofa yace dakata ms (miss) mainasara! Da alama sanda kika saka hannu a takardan aiki baki karanta ba? Ka'idar mu shine dole mutum yayi aiki damu a kalla na shekara 1 idan ba wani laifi yayi aka koreshi ba. Kinga bisa wannan dole kiyi aiki anan batun mukami kuwa nine me komai anan Dan haka no zan zabi Wanda naga dama ya zama kaza ko kaza. Daga gone office dinki ya dawo nan, banason latti! zaki iya tafiya.
Washe gari lokacin free period sai surutu ake a ajin su zayya kaya kaya yayinda ta turo baki tayi jugum kamar ka dangwaleta tayi kuka.
Halsey da yeonsil ne suka zo sukace zayya wai ba yau bane 1 year anniversary dinku keda saurayinki? Ba yau zaizo ba? Ajiyan zuciya ta sauke tace jiya muka rabu sukace mene? Meyasa?
Kuzarinta ne ya dawo Mata a take tace kai kubar wannan zancen kunsan mota Lexus? Yeonsil tace nidai ban taba shiga cikinta ba amma na taba ji. Zayya tace kina ganin nawa za'a kashe domin a gyara Dan karamin kurjewa a jikinta? Ta fadi hakan tana gwada kankantar da hannun ta?
Murmushi me kyau halsey tayi tace ke gajiya me kika aikata? Cikin San yarda magana tana wasa da yatsarta tace bani bace kawata ce. Halsey tace a kudin kasarku akalla dubu dari! Zayya tace haa ? Yeonsil tace zaifi sauki ka biya jikinka.
NA YEONSIL
Kifawa zayya tayi cikin harshen hausa tace na banu na lalace. Bayan an tashi akayi assembly na karshen sati Wanda yayi daidai da karshen wata kuma bisa al'ada duk karshen wata dukan fito bakin makaranta susha iska na minti talatin yayinda za'a tabbatar an kewaye waje da masu tsaro saboda masu guduwa. Yauma dai hakan akayi cikin jindadi su zayya suka fito suna yar hirarsu yeonsil tace la kyautar cupcake ake bayarwa acan naga an taru? Kafin ta sugmfe baki zayya tayi nisa AI suma gudun suka saka domin baza su ki bati ba.
Isarsu keda wuya suka kutsa taro sukaga an lillika fefofi ne rubuce a jiki ba komai bane sai: ZAYYANA MAINASARA KI FITO YANZUNNAN! Yagewa ra fara yi rana fadin wani Dan iskan ne yayi wannan?
A gefenta taji muryasa da bazata manta ba yace manyan Mata yaushe gamo? Kinyi kyau fa. Tsaye yake a jikin gini yayinda ta jingina kafarsa daya ya shafa bakin gashin dake kwace a kansa tare da sake Mata wani munafikin murmushi.
Murmushin yake tayi masa rare da cewa hi wato sannu. Gaba daya yan matan ne suka fara "awwn!" "Kyakkyawa!" "Waiyo dama yace yana sona" da maka mantansu. Abinka da Wanda yayi karatu a turai sankamarta yayi ya daura kafada nan yan Mata suka fashe da ihun hakan yasa hankalin securities yayi kansu Wanda ya bashi daman sata a mota yayinda tabar yar Mata suna zubda yawu aminanta kuwa suna mamaki.
Tafiya suke tana tunanin zuci "wai ina zai kaini ne?" Taji yace what a beautiful (kai yau rana mai kyau ce) ba karamin kyau zaiyi ba idan akaje ofishin yan sanda ko makabarta. Farce ta fara ci cikin abin tausayi kamar marayan bera tace Dan Allah karka kasheni. Yar budurwar dariya yayi yace bazan kasheki ba abinda zakiyi kawai ki bani $10,000 ko kuma mu karasa. Maganar yeonsil ce ta fado Mata, cab wallahi babu yadda za'ayi ta biya da jikinta.
Yadda kasan marayan Dan akuya haka muryatta ya koma tace nifa talaka ce yar makarantar secondary ne ajin manya. Banida kudi. Yace hmm! Da alamu dai nafa bakida hanyar biyan kudin barnar da kikayi ko? Kirjinta ne yace dam amma ta gyada kai murmushi yayi yace ba matsala.
Restaurant ya kaisu tare da ajiye Mata wani paper a gabanta yayinda ya bararraje kamar a parlourn gidansu.
Yace sign it ( saka hannu aciki ). Tace menene wannan din? Yace karanta mana, dala dari ko wace Rana Dan haka zaki gama biya a kwana 100. Kinga 100×100=10,000.
Lekawa tayi taga an rubuta ENSLAVEMENT AGREEMENT wato yarjejeniyar bauta turo baki tayi tace wannan rashin adalci ne fa. Yace rashin adalci? Toh shikenan sai in karbi kudin daga waje mamanki. Ya fadi hakan yana zaro wayarsa tace barshi barshi zan saka hannu.
Ta daura bairo kenan tace kodai kokari kake ka.... sai ta shiga tunanin ya siyar da ita a gidan giya wani kurma ya ceto ta ya aure ta. Saurin girgiza kai tayi tace bakida lafiya yan Mata ko kyau ma bakida shi bari in fada miki. Tace anji dai! Yace ni kiyi sauri yunwa nakeji. Signing tayi ya karba ya ninke ya ajiye kamin yace student ID card dinki kuma sai mun gama yarjejeniyar tukunna zan baki dai lokacin abincin su ya iso dadi ta fara ji cikinta har sauti yake bayarwa sai taga an jerasu baki daya a gaban sa turbune fuska tayi yayinda yaci koma biyu a jere kamin yace banacin abinci da bayi na. Wullo Mata atm yayi yace kije wani shagon kusa ki nemi Dan abin ci da ruwa saura kici dayawa ki gani.
Wani restaurant ta shiga tayi ordern abinci kala kala Wanda yakai mutane Goma suci su koshi.
...........
Washe gari minal ta rubuta Letar daukan hutun kwana 3 wai za'ayi Mata tiyata na appendix. A gaske kuwa so take ta shirya kanta yanda zata iya danne bacin ranta ta huce idan taga yazeed.
Zayya kam titsiyeta yeonsil, halsey da sauran aji sukayi, a ina kika samo hadaddan gayen? Gashi da kudi ga kyau da alama yanada Ilimi cewan halsey. Yeonsil tace kode mafarkin ki ne ya zama gaskiya? Zayya tace to AI shi ba yarima bane da alamu dai kyakkyawa ne kuma yanada kirki.
Ihu yan ajin suka sake kamin ruwan tambayoyi ya fara zuwa kamar haka, tun yaushe kuke tare? A ina kika hadu? Wani makaranta yake zuwa? Inane gidansa? Me da me kukayi?
Murmushi tayi tare da gyara zama tace restaurant ya kaini ya siya min icecream har yace zai zama bawa na, sai mukayi yawo a Lexus dinsa sai yakaini gida ta karashe maganar tana murmushi kamar da gaske. Halsey ne tace kinada message. Karba tayi taga sahir ne.
Bandaki ta shiga tana rufewa gabadaya yan ajin suka lika kunne a kofa. Kiranshi tayi kamar yadda ya umurta yace ba nace kina ganin kirana ki dauka ba? Tace yanzu na fito daga aji. Yace naji maza kizo gidana yanzu tace mene? Yace abinda kikaji. Tace ina da sauran aji daya fa kamin a tashi bai amsata ba yace Gidana yana kallon makarantar ku ta gefen dama. Tace Anya kai musulmi ne kuwa? Kizo yanzu kawai yace kamin ya kashe wayarsa. Tace hello! Hello ! Ihu ta kwalla kamin ta naushi kofar ji kake ruuuu! Gajab gaba dayan su dake bayan kofar suka zube. Tafiyan maza ta fara Su halsey suka biyota sunajin dadi cikin ƙaguwa sukace zayya! Ke zayya wai cewa yayi kije gidansa? Halsey tace lokacin yayi! Riko hannunta sukayi cikin bada karfin guiwa sukace zayya mu zaki iya kinji? Yarfesu tayi tace ka dalla ku matsamin ni bansan me kuke magana akai ba.
Cikin tsohon dakin ajiya ta shiga ta window akwai inda ya fashe dama ta nan take fita kuma akwai tsani (ladder) dan haka ta fice.
KAKA KARA KAKA CABDI HMM DA FATAN DAI KUNA NISHA DAN TUWA ? WANI HANZARI BA GUDU BA ZAN CANJA SUNAN LITTAFIN DAGA KURUCIYAR MINAL ZUWA (WAI KOWANI AURE IRIN NAWA NE?) YAYI KO BAIYI BA ? IDAN KUNADA WANI SUNA A ZUCIYARKU TOH KU SANAR DANI ZANYI FARIN CIKI.
DON'T FORGET TO VOTE, COMMENT, SHARE AND FOLLOW ME miss_untichlobanty LOVE YOU ALL
Miss Untichlobanty 💕
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top