CHAPTER 84
OH WAI YANZU COMMENT DIN MA AN DENA.
RECAP
Ido cikin ido suka fara nufo juna gaba daya daliban da suka taru suna kallo baya baya suka fara yi Dan sunsan yau za'ayi world war na 3.....
CONTINUATION
Naushi ya kawo Mata ta kauce, caraf tayi ta riko shi tare da basa one blow seven die. Haka dai ta hadesu duka su goman ta basu kashi.
Principal ne yazo kanshi ya bata sammacinta lokacin da aka dawo daga wasa.
Cikin takunta na maza ta shigo dakin taron Dan malamai gaba daya sun taru, cikin harshen turanci tace malamai sannunku sannan ta dauke kai.
Ajiyan zuciya principal Solomon ya sauke tare dacewa zayyana meyasa? Meyasa bakyajin magana ko kadan? Ke wace irin matamaza(tomboy) ce? Mun baki hutun hukunci (suspension) yadi Akirga,hukuncin Karin lokacin tashi (detention) kuwa yana cikin jadawalinki. Kinsani a Bisa ka'idar makarantan nan ba'a duka tunda international school ne Dan haka mun yanke shawara zamu mayar dake dayan branch dinmu Wanda babu musulmai,babu hausawa, babu yan kasarnan saide yan wata kasa.
Tunda principal din ya fara magana ta saka earpiece a kunnenta dan haka koda ya gama godiya tayi ta karbi paper da ya bata sannan tayi ficewarta aji ta koma ta zauna a kujerarta Wanda ke karshen aji sannan ta fara shirgar baccinta. Girgiza kai malamin yayi kamin yaci gaba da bada darasi.
Koda aka tashi sanda sukayi fada da shameela akan ta bata musu lokaci zayya bata ce kala ba sanda shameela ta gama zayya tace bana taba Mata saboda ragwaye ne sannan ta wuce abinta.
Suna dawowa suka samu kowa da kowa a parlour barka da zuwa aka musu mama na zaune a gefen daddy wato Alhaji mansur mainasara, yayinda aunty jalila ke hararan kanwar shameela wato nana saboda tayi roko.
Bushra aka tisa a gaba akewa fada akan yadda ta rufe ido Sam wai ita sai mai kudi zata aura. Ga yadda take wulakanta talakawa kuma hakan matsala ke haifar musu ita da minal.
Ko ina idan minal taje neman aiki sai ace ba ita bace tayi wulakanci a waje kaza ? Sai a koreta komin rantsuwar da zatayi, yayinda ita kuma bushra ake cewa an ganta a waje kaza da shiga ta mutanen arziki. Shiyasa kullum sai sunyi fada.
Daidai lokacin minal ta sauko tana sauri tace bye bye everyone (kowa da kowa ) ni na fita inada interview Alhaji mansur ne yace haba minal ni zakibi ta tawa da kin bari na miki hanya kin samu aikinnnan cikin sauki. Girgiza kai tayi tace no daddy nafiso insha wahala in Nemo da kaina zanfi daraja aikin. Murmushi yayi yace kuma hakane kinci wannan yar uwar taki ita ba aikin za'a nema Mata ba ko yi Mata za'ayi bazata karba ba nide nayi asarar kudin karatu . Mikewa bushra tayi tana fadin haba dady tunda wannan imposter (me satan kamannin wani) tazo gidan nan ka dena sona komai akayi minal, minal, minal,minal.
Dariya yayi yace yaro man kaza ai sai ki yi aure ko kinga ba sai kinganta ba balle ta baki haushi. Kema.. ya fadi hakan yana kallon minal ya kamata ki samu miji ki sake aure tunda dai a asibiti ance babu abinda ya samu kwakwalwar ki malamai ma sun duba ki ance ba komai ko akwai abinda kikeji. Tace a ah kawai de idan suna duba ni sai in fara ji na tuna komai da sungama kuma sai na sake mantawa gashi kuma ko nayi kokarin fada kasawa nake.
Ajiyan zuciya yayi yace Allah dai ta kyauta. Fitowa tayi sabir na labe domin ya tabbatar ba bushra bace Dan batason ko ganinsa tayi acewarta.
Ganin ya tabbatar minal ne yasa yazo suka gaggaisa sannan ta fice bayan ya Mata addu'ar Allah ya bada sa'a.
Ba'a Dan Jima ba sai ga bushra ta fito itama buya yayi a bayan flower zuciyarsa na lugude.
Tuka motan ta take tanata sauri Dan tayi latti motan dake gabanta ne ya tsaya ba tare da bada alama ba aiko sukaci karo kau.
Iska ta furzar tare da saukowa ta cika tayi fam. Shima (yazeed) fitowa yayi kannensa dauke da bluetooth tare da fadin zan kiraka ta harshen larabci sannan ya kashe.
Masifa ta fara yi masa baka ganine? Ya zakayi muna cikin tafiya ka tsaya? Ba tare da ya ce komai ba ya nuna Mata traffic light. Rufe ido tayi tare da shafa fiskanta tace kayi hakuri ban lura bane na..... datseta yayi ta hanyar cewa banida lokacin wannan ki bani business card dinki cikin harshen larabci Dan shi ya manta domin waya yake da Jamal lokacin da abin ya faru.
Tace mene? Ya sake cewa nace ki bani katin kasuwancin ki ko bakyajin larabci ne ? Sarai taji abinda yace amma tasan rainin wayo ne kawai irin na mai kudi yana Nigeria yace bai iya hausa ba? sai tace la ban iya ba, banaji, ka gane me nace, la Arabic, la okay? Mota ya koma ya dauko wayarsa tare da daukan hotonta sannan ya karbi wayan hannunta yasa numbarsa ya Kira. Tace kai dalla malam ka bani wayata ko bakaji ne? Nace ka bani wayata ko? Mika Mata yayi still ta larabci yace yanzu inada hotonki inada numbarki zan kiraki mu tattauna kudin gyaran. Purse dinta ta dauko ta ciro passport dinta ta bashi tace ga hoto na maza goge hoton da ka dauka. Karba yayi yasa acikin suit dinsa sannan ya shige mota kan tayi magana yaja abinda saboda an basu hannu. Tace kai, kazo ka goge hotonnan wallahi. Tsaki taja ta shige motar ta duba madubi tayi Dan ta gyara wuyan hijabinta sai taga ashe man bakin ta ne ya baci. Naushin steering tayi tare da cewa Allah ya hadamu kaga ikon Allah sannan ta wuce.
Aiko taci interview kuma ta samu aiki a jeedmar group a department din ayush....
Da yamma da ta dawo gida ta samu an taru a parlour kowa yayi jungum jungum an kafe zayya da ido zama tayi tana me fadin lafiya? Letter da aka bawa zayya aka miko Mata ta karanta abinda ke ciki kamar haka.
"Letar sauya makaranta
Duba da yadda daliba zayya mainasara ta addabi makaranta saboda rashin jin ta, da yadda take fada da maza. Hukumar makaranta ta yanke shawaran mayar da ita dayan cibiyar mu Wanda ke wajen gari kuma makarantar kwana la Alla zatayi hankali.
Idan har iyayenta basu yarda da wannan hukunci ba toh saide a gafarcemu domin bamuda wata zabi da ya wuce mu koreta .
Mun gode ~~
Saka hannun makaranta
Mikewa minal tayi tare da riko hannunta suka shiga daki,dadi ne ya kama shameela yau za'a daki zayya yayinda cikin daki kuwa minal tace zayya na fahimceki domin nima nayi abinda kikeyi yanzu haka, yau dinnan ma naso in daki wani amma yanzu na girma, bawai ina karfafa miki guiwa bane saide banason ki dinga taro fada, amma kuma karki zauna a cuceki kinji? Kuka ta fara yi tace mummy ni gaskiya a cireni daga makarantar banason rabuwa dake, minal tace karki damu ni inaji a jikina ALKHAIRI ne kuma zan dinga kawo miki ziyara duk karshen wata sannan zan canja miki sabuwa waya ma, washe baki tayi tace da gaske? Minal tace sosai ma kuwa na samu aiki yau. Ihun dadi ta sake shameela dake kasa tace yes a kara Mata Alhaji mansur yace je banson shashanci fa. Zayya ne ta sauko tana fadin grandpa mummy ta samu aiki! mummy ta samu aiki! Murna aka taya minal yayinda da aunty feena da aminiyarta deena suka ja minal daki cikin kaguwa sukace sis a wani company ne tace a jeedmar ne sukace what?! Mene? A jeedmar? Deena tace wow! Naji ance president din kyakkyawa ne, feena tace dama nice saide abinda na karanta idan na samu aikin dakyar idan zan dinga ganinsa. Minal tace nima sai akace muku ganinsa zanyi ko Dan shi naje yin aikin? Dariya suka kyalkyale dashi sunata bata labarin yazeed.
Bayan Sato biyu
Zayya ne rike da akwatinta tsaye a bakin makarantan su tana kare masa kallo kai amma an rena wa bakaken fata, wato shine su akayi musu nasu local amma dubi wannan branch din kamar a turai, itakam rashin ji yayi Mata rana. Bude kofofin hancinta tayi ta shaki iska tana sakan murmushi kamin ta shiga. Bawa idonta abinci take sosai Dan jinta take kamar a kasar waje. Gaba daya yan makarantan ke binta da kallo abinka da turawa da yan China su Korea ne, Italia ne Thailand ne yan turkiya dukdai gasunan suna al'ajabi domin sunsan ba'a kawo bakar fata makarantan su.
Cikin harshen turanci suke magana dan haka tace menene kuka kafa min ido? wata baturiya me suna halsey tazo cikin zumudi ta rungume zayya tace bakuwa a makarantar mu, sannunki da zuwa sunana halsey kuma zanso mu zama aminai, nasan ma kin yarda Dan haka mu aminai ne zo muje. Ta fadi haka tana janta.
A wani hostel kike? Wani daki?
HALSEY
Zayya tace dakata mana, da farko dai yaushe nace na yarda mu zama kawaye? Abin tausayi tayi tace bakyasona ne? Dariyar zayya tayi tace dalla gyara fuskarki ni ki rakani wajen principal. Zayya tace yay naji daidai muje..... rike hannu sukayi suka nufi office din principal. Knocking sukayi suka shiga suka samu principal dinsu yar kasar Australia. Murmushi tayi musu tace ku shigo mana sannan ta kalli zayya tace da alamu kece zayyana mainasara ko? Tace nice ma. Wani paper ta bata. Photo copy ne na student information tare da su hostel ajujuwan da zata dinga shiga da sauransu. Godiya tayi principal din ta bata uniform tana fadin principal Solomon ya ce bakida tarbiyya sai an miki tsauri ni banga alamun haka ba. Halsey tace kwarai kuwa principal, kawata tanada mugun kirki ga hankali sosai ma kuwa, mun gode, muje ko ? Ta fada tare da janta suka fice.
Halsey tace menene wannan wai a kanki, zayya tace shi aje Kira hijab, halsey tace me aikinsa to? Tace saboda rufe kyawun mu domin shine mutunci (modesty) bakyajin zafi? Zayya tace kin fiya tambaya gaskiya zan amsa miki rakani daki.
Halsey tace muga paper din, ihu ta kwalla lokacin da taga cewa dakinsu daya tace dakin mu daya muje! muje! muje! Unpacking kayan zayya sukayi halsey na fada Mata duk wani information da ya dace ta sani da yar iskar makarantar tasu.
Wayanta halsey ta dauko suka dauki selfies. Daddare zayya ta dauko diary dinta ta fara rubutu:
MONDAY– 6 JUNE
Yau nazo sabon makaranta na kuma wallahi kyau gareshi gashi nayi kawa mai suna halsey saide akwai wata banziya wai ita vanessa amma zanyi maganinta idan ta shiga sabga ta.
Don't forget to VOTE, comment and share love you all.
Miss Untichlobanty 💕
15th April, 2020.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top