CHAPTER 79

RECAP

Kwalbar ta raruma ta kwalawa ma wani sannan ta Mike ta fara bin gini aiko ta taka kwalba. Toshe bakin ta tayi tana fita aka kawo wuta hakan yasa suka bita a guje ashe sabi nigga ta kwalawa kwalbar.

Gudu suka dinga yi kamin ta samu ta labe a lungu sai haki take taji an dafa kadar ta juyowa tayi suna hada ido ta zaro ido tare da kwala ihu...

CONTINUATION

Ba kowa bane illa sabi nigga, aiko ya wanka Mata wani jahilin Mari Wanda ya sata faduwa ba tare da bata lokaci ba.
Dariya ya sheke dashi harda rike ciki, hakan ya bata daman rarumar dutse ta tashi a hankali sannan ta kwala masa.
Ihu ya saka yayi da ta fita a guje tana mai tallafo cikinta Wanda ke Mata zafi a halin yanzu.
Sauran yan daban ne sukayi saurin karasawa wajen sabi'u sakamakon ihun sa da sukaji. Tambayan sa suka fara yi lafiya ? Ya nuna musu hanyan da minal tabi. Biyu daga cikin su ne suka bi hanyar yayinda lado ya tsaya, ya tallafa masa ya tashi sannan ya fara kokarin kaishi gida.

Minal gudu ta sharara har sanda kafar ta suka daina gudu kamin ta Sami zauren wani gida ta shiga. Itacen girki ta gani a jibge gefe guda dan haka taje ta jingina a jiki babu bata lokaci tayi bacci dukda ko a jikinta  tanajin akwai abinda ya dace tayi Wanda batayi ba.

🌹🍀

Yazeed bai bude idanun sa ba sai wajajen karfe Goma na dare. Akan fuskar ayush suka fada ta sakar masa wani murmushin munafurci tare da fadin brother sannu da tashuwa. Kallon ta yayi da alamar tambaya yace brother? Tace eh karka damu dama likita yace min zaka iya manta wasu abubuwa so karka damu, San baka dukkanin information da kake bukata. Jinjina kai yayi alamun toh yana kare Mata kallo Dan shi bai ma yarda da ita ba yace wacece ke? Murmushi tayi tare da zama a bakin gadon sa ta riko hannun sa. Dan janyewa yayi tace karka damu ni muharramar ka ce,ni kanwarka ce, your baby sister ka tuna?  sakan jiki kadan yayi yace toh me yasa aka kawo ni nan? Tace saboda tun sanda mahaifin mu ya rasu kake cikin damuwa hakan yasa kake samun wani ciwon kai me tsanani Wanda yakan sumar dakai wani lokaci ko ya sabbaba maka manta wani Abu toh wannan karan da alamu alakarka da mutane ka manta.

Jinjina kai yayi domin maganan ta kama kwakwalwar sa. Yace munada mahaifiya tace eh tana gida yanzu kaga hotanta. Ta fadi hakan tana mai nuna masa wallpaper wayanta. Hoton su ne su hudu, shi da ita da mummy da umma hani. Yace toh ai Mata biyu ne wajen waccece ita? Tace me kwalliyar nanne mana. Wancan kuma umma hani ce nanny din mu. Ajiyan zuciya ya sauke yace bani ruwa insha, Darius tayi kamar shasha tace au na mance na tsaya ina maka surutu.  Murmushi kawai yayi tare da karbar ruwan yasha.

Nan dai taci gaba da masa bayanan karya shi kuwa Allah sarki bai sani ba sai shiga yake tare da rike komai da take fada masa.

🌹🍀

Gidan mahaukata sukasa aka kai mom bayan an haukatar da ita. Mai kawo abin ci ne tazo tana wulla musu hara ta iso dakin mom Wanda yake na karshe. Tana kallon mom taji kamar ta Santa kuma lokaci daya taji mahaukaciyar ta kwanta Mata a ranta. Wulla Mata nata abin cin tayi mom taso ta dauka ta kyalkyale da dariya kamin kuma tace na gode.

Fara co tayi tana yamutsa fuska da ka ganota kasan bata Saba shan wahala ba. Tsayawa kallonta tayi kawai sai taji hankalinta ya kwanta da mahaukaciyar. Bude dakin tayi ta shiga sannan ta rufe, a take mom ta fara ja da baya tana fadin karki matso kusa dani! karki matso kusa dani! Matar tace kwantar da hankalin ki ba abin da zan miki.

Zama tayi a gefenta kawai sai mom ta fashe da kuka. Matar me suna senior hauwa tace me aka miki kike kuka? Mom tace ɗa na, zasu cutar min dashi! Senior hauwa tace ina yake kuma yaya sunan shi? Shiruuuu mom tayi kamin tace nima ban sani ba, na manta sannan ta sake fashewa da kuka.

Rarrashin ta senior hauwa tayi haka sukayi hirar su dukda cewa wani lokacin mom din takan Mata hauka amma dukda haka tana zargin wani Abu tana ganin haukan mom din ba haka kawai bane.

🍀🌹

Washe gari da safe aka sallamo yazeed kuma har wannan lokacin ayush tana like dashi, mummy ne tazo tayi musu oyoyo, taci ado ta kashe saurin dankwalin shaddar nan, gwala-gwalai ta ko ina abin nema ya samu.

Daidai lokacin wayan ta yayi ringing hakan yasa tayi excusing kanta kamin ta haura sama. Goje ne ke kiran ta, tace baby ya akayi ne? Yace lafiya kalau wifey dama so nake mu hadu tace okay no problem ka sameni a Sheraton hotel, royal suit daki na uku yace ba matsala sai mun hadu.

Motar luku ne suka ta iso suka fito suna cewa ina president? Wai attack dinka ya tashi ko? Nan sukayi masa jaje domin suma an juyar da kwakwalwar su sannan suka koma side dinsu, kuma a daidai lokacin ne su zakiyya suka shigo ita da Jamal. Yazeed yayi shaking hannun Jamal yace gou are Jamal ko? Jamal yace yup ashe baka manta ba. Dariya yazeed yayi yace ai little sis ta fadamin tace idan naga balarabe toh shine cousin Dina jamal. Jamal yace tabbas kuwa amma ka daina damun kanka, uncle ya tafi babu abinda yake bukata sai addu'ar mu. Mummy ta fara share kwalla kamar da gaske.

A halin yanzu dai abinda suka nuna ma duniya shine baban yazeed ne ya hada jini da larabawa saboda kimanin yazeed da kuma Jamal idan ba haka ba ai mummy yar najeriya ce futuk dan haka basuda explanation shi yasa suka hado wannan karyar tunda dai a zahirin gaskiya mom ce balarabiya kuma sun batar da ita.

🌹🍀🌹🍀

Koda su lado suka karaso layin su godiya sabi'u yayi masa tare da cewa ya tafi gida shima zai wuce haka suka rabu suna shirya yadda zasuyi mugun sabawa minal idan suka sameta.

Yana raba hanya haka ya shigo har ya wuce sai yaga kamar akwai wani Abu da bai Saba gani ba a gefen itacen mahaifiyar sa. Rakani kashin sa (Nokia) ya ciro ya haska sai ya tuna ashe gari ma ya waye kalla yayi dakyau yaga minal kwance tana bacci hankali kwance. Yace daidai kenan wato kin tagaiyara ni  shine ke kuma zaki kwanta kiyi bacci ko? Toh gashinan Allah ya kawomin ke har gida. Dariya ya fashe dashi Wanda yayi sanadiyyar farkawar ta babu shiri ta fada cikin gidan daidai lokacin ummu amina ta sauke kunun sayarwar ta tana kokarin dauko su mukubur din ta na tuyar kosai taga mutum ya fadi Mata gida salati ta rafka yayinda minal ta buya a bayanta. Daidai lokacin sabi ya fado cikin gidan yana fadin ina take ? Ina ta shiga? Ummu amina tace lafiya zaka biyo yar mutane ku fadomin cikin gida da sanyin safiya? Yace kalli, ummu kalli goshina. Wannan yar iskar ce taji min.

Kallon ta ummu amina tayi tace a ah yar nan Dama kece? Sabi yace kin Santa ne? Tace ai jiya da muka fita nemanku ni da uwani, sai aka fara ruwa anan muka hadu da ita.
Kai miko min kujerar can ta zauna, yace  tashin hankali ai indai ni zan dauko kujera ta zauna saide ta mutu a tsaye. Ba rantse da wallahi idan na shiga na fito bata bar gidan nan ba, zan muku hauka. Yana fadin haka ya banka dakin sa ya shiga. Ummu amina tace dadin abun nice uwar ba kai ba, daga nan ta shigar da minal daki ta zaunar da ita ta bata kunun sannan tace Mata ta shirya su tafi kasuwar gwanjo ta siyo Mata kaya, ta daga kai alamun toh nan dai ummu amina ta gane cewa minal bata iya magana.

Haka suka tafi kasuwa ta zabo Mata kala 5 masu arha da rahusa sannan suka dawo gida. Koda suka dawo sabi bayanan dan haka ummu amina tace ma minal tayi wanka ta shirya sai tazo ta karbi kosai a kofan gida.

🌹🍀

Yazeed yana zaune a dakin sa, ayush tana hada masa shayi yace little sis banida Mata ne? Ajiyan zuciya ta sauke tace Allah tayi Mata rasuwa bayan ta haifi safwan. Shiru yazeed yayi kamin yace safwan din ɗana ne? Ayush tace eh shi da yayan sa safwan. Murmushi yazeed yayi yace no wonder nakeji kamar ina missing wata ashe marigayiyar Mata ta ce. Ina yaran suke? Tace sun tafi school is already 8am fah. Yace kikace nine president na jeedmar group ko? Tace ofcourse bro Yace toh gobe zan cigaba da fita aiki. Tace okay but bro kasan ban Dade da dawowa daga karatu ba and you said zaka bani GM kace zaka shirya papers din kuma sai wannan abin ya faru. Yace no problem tomorrow zaki iya fara fita kece general manager na advertisement department. Tsalle ta daka tare da rungume shi tace thank you brother, ya shafa kanta yace you are welcome sweetheart.  Kanshi ne ya Sara jin kalmar sweetheart hakan yasa ya rike kansa. Tace bro lafiya yace nothing ki turomin sahir da safwan din idan sun sawo in gansu. Dariya tayi tace kaji ka fa bro wai ka gansu. Sai kace irin an siyosunnan yace toh ai na manta shiyasa. Dariya kawai tayi ta fice, tana fita daga side dinsa ta daka tsalle tare da fadin yes! Komai yana tafiya yadda nake so.

.......

Ummu amina tana cikin tuya minal ta fito ta zauna a gefen ta, Murmushi ta Mata tace har kin fito kenan? Minal ta daga kai kosai ta zuba Mata ta fara ci tana Mata hiran yadda takeson Allah ya bata diya mace. Tace sai gashi Allah ya bani ke, kinason ki zama diyata? Minal ta daka kanta.

Abinda basu sani ba yan anguwa duk sun taru, labari ya ratsa ko ina akwai sabuwar budurwa kyakkyawa a gidan ummu Amina kuma tana da ciki. Saurayi dake siyan kosan ne yace ummu amina wai a ina kika samo wannan kyakkyawar budurwar? Ummu amina tace kai banason maganar banza diyar nan tawa ce da na Dade ina rokon Allah ya bani ya kawo minaita har gida, kuma harma ina sa ran samun jikoki. Sunan ta Amina.
Kallon minal yayi yace wow nide minal baby zan dinga kiranta sannan yayi kokarin riko hannun minal din. Wani irin kallo ta banka masa tare da Jan dogon tsaki tana mai yin kicin kicin da idanu.
Yace tofah, ummu ai baki sanar dani cewa amina taki batada kunya ba ashe uwar tsiwa ce. Wani kallo minal ta aika masa ta ajiye kosan a gefe ta dafa kasa ta Mike. Wato za'ayi cakwakiya kenan, daidata tsayuwarta tayi ta dunƙule hannu wata Mata dake keken abinda ke faruwa ta window tace tooo, ashe aminar ba ta arziki bace wannan aminatun yar jagwal ce.
Take kan minal ya Sara 'aminatu yar jagwal' ke Mata yawo akai kamin ta yanki jiki ta fadi.

Nan fa...nan fa...nan fah. Au ashe ruwan biro na ya kare shiyasa na kasa ci gaba da labarin😁

Karku manta ku latsa tauraron dake kasa sannan kuyi COMMENTING hakan ne zai nuna min tsananin kaunar da kuke wa littafin nan da ma mai littafin da kanta.

Follow me on miss_untichlobanty

One love 💋 from your KARAMARSU  BABBARSU

Miss Untichlobanty 💕

30th March,2020

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top