CHAPTER 77

RECAP

Zaune take a kan gadon dakinta yayinda take hango duk abinda ke faruwa a farfajiyan gidan, wani kuna da tafarfasa zuciyar ta keyi kamar tayi hauka haka takeji. Fincike drip din dake hannunta tayi yayinda ta yage riganta jiyoyin kanta sun tashi cikin huci tace nayi regretting aurennan da nayi auren banzan nan da nayi shi ke hannu kusantar ka masoyi na yazeed. Ke kuma sh*giya sai na hallakar dake da wannan tsiyar dake jikin ki sannan ta naushi gini Wanda har jini sanda ya fito daga hannun ta inda ta lashe tare da cewa na rantse da jinin nan nawa sai na kasheki.

CONTINUATION

Jiki na rawa nurse din dake kula da ita tazo ta riko hannun ta dake zubda jini cikin harshen turanci tace ina rokon ki ki barni in koma kasar mu kar wata rana su gane ba a coma kike ba su kasheni dama ance yan ta'adda ne bakaken fata. Mari ta falla Mata tace ki iya bakin ki. Hawaye nurse din ta fara tace maza goge hawayen nan sannan kika sake wani ya gano me ake ciki ni da ke ne. Kamata ma yayi ki ji dadi ana biyan ki ba tare da kinyi aiki ba.

Cikin kuka nurse din tace idan yanzu suka shigo suka ga hannun ki da ciwa ta yaya zan fara bayani? Hankade ta tayi Tate da zama bakin gado tace gyara min hannu na.
Jiki na rawa kamar mazari haka nurse din ta fara dressing hannun nata. Itako tunani take a ranta kamin tace ni ayush nayi alkawari indai bazan samu yazeed ba toh babu mai samun sa kuma wad......

Ringing wayanta ya fara hakan yasa bata karasa maganan ta ba ganin goje love na yawo akan screen din yasa ta jan tsaki tare da dauka cikin murya my zaki tace my love! Ta dayan bangaren goje yace wifey wai yaushe zaki tashi daga jinyan karyan nan ne ? Nayi missing dinki fa.

Murmushi mai sauti tayi tace soon karka damu sai anjima banason su jiyo ni bye zan kashe wayan ne.
Wani tsaki taja tare da fadin kaina aikinka ya kusa karewa. A bangarenshi kuwa tunanin yadda zai kashe ayush ne da tayi taking control ta masa handing over.
Bokanta ta Kira sukayi kus kus Wanda nima banji ba. Tace shikenan ko da akwai wani Abu. Ta dayan bangaren boka mugu yace wannan aikin babba ne dan haka ina bukatar ki samo fatan farjin mace sabon gawa zan miki wani hadi sai kisa a cikin jikinta,ki tabbata kin tura sosai tace zan iya bayarwa ayi? Boka yace ko da wasa, da kanki zakiyi!
Tace naji matsalata dakai ka fiya tsauri, dariya ya sheke dashi tace dadi na fa? Tace aikin ka ba wasa.
Dariya suka sheke dashi mai ban tsoro Wanda yasa cikin nurse kadawa da daukan ruwa dukda cewa batamin yaren tasa ba abin arziki ake kullawa ba.

Ƙwanƙwasa kofan dakin da akayi yasata kwantawa yayinda nurse din ta lillika mata fake drip da sauran su.
Bude kofan tayi zakiyya ce ta shigo ta zauna a bakin gadon tare da shafo kumatun kanwarta tana Mata kallon so, kamar kullum yauma sanda ta tamabayeta yaushe zaki tashi? Hawaye ne suka dinga zirya a idanunta.

Bayan aani lokaci tace ma nurse din zata tafi nurse dai nata gyada kai ne Dan banda film bata taba ganin irin wannan mugunta ba.
Ayush kam tunani ta lula bayan zakiyya ta fita. Juyi tayi tare da tuno sanda ta fara haduwa da goje.

FLASH BACK

Kamar yadda kuka sani zakiyya ta kasance me kokari,makaranta daya suke zuwa har ayush toh saide zakiyya tafi ayush da aji daya.
Ayush a rayuwanta babu Wanda take mutuwan so kamar Farouk saurayin zakiyya hakan yasa take Mata hassada, gashi ta fita kokari tana karban kyaututtuka.
Yau ta kasance ranan rufe makaranta kamar kullum zakiyya ce tazo na daya, yan ajin su ayush din suke ta tsokanan ta wai itace dakikiyar family din baki daya shiyasa ko turanci bata iya ba lokacin. Da gudu ta fice tana kuka bata ganin inda take tafiya. Cin karo tayi da marka mai goro da Sigari tayi Mata bari nan fa marka tace ta biyata, ita kuma batada kudi. Hayani ne ya kaure, karkashin wani rumfa goje yace ke marka wai me kike ta daga makokoro ne? Tace wannan banziyar kwailar ce ta yi mini bari, karki ga kinje makaranta ki nemi ki kawomin ranin hankali ta karashe tana cin kwalar ayush.

Sauri ayush ta kara tana mai kara tsanan duniyannan saboda azzalumai sunyi yawa a cikinta.
Lokacin shekarun goje 20, wulla ma ta kudin yayi  tare da riko hannu ayush har cikin rumfan suka zauna. Yace yan Mata ya sunanki? Tace Aisha yace wow! Kina da saurayi ta girgiza kai. Yace me yasa kike kuka toh? Abinka da shashasha nan tazauna ta tsara masa bayani shikam sai binta yake da ido. Sigari ya bata yace ta zuka aiko ta kware sai tari take yace ta sake gwadawa a haka har ta zuke daya tuni ta fara jin ta a sama duk damuwan ta sun tafi.

Tun daga ranan suke ture turen letter domin a garinsu take hutu. Wasa wasa ta fara son shi hakan yasa lokacin da ya baiyana Mata soyaiya ta Amince kai tsaye. A haka ya dinga Mata kalamai inda ya nuna Mata yana son jasancewa da ita amma ba'ayi musu aure ba a gida dan haka sukayi aure a boye. Hakan yasa koda tace zata zauna gidan yazeed baiso ba amma tunda kudin yake bukata ai shikenan.

END OF FLASH BACK

Hawaye ta goge tare da ci gaba da tunaninta sannan taji haushin kanta na yin soyaiya da lukman kawai Dan ta kusanci yazeed.
Message din plan dinta tayi ma goje kamin ta fara shirye shiryen fita.

Zakiyya kuwa tana fita daga dakin ayush dakin ta taje ta shirya sannan ta nufi dakin minal domin ta kaita antenatal kamar yadda suka Saba. Taimaka Mata tayi ta shirya sannan suka nufi dakin mom sukayi Mata sallama.

Ayush kuwa direct gidan goje taje ta karbo shantun da bokan yace a bata Wanda tayi mai text ya karbo sannan suka tafi operation area. Text bokan ya Mata na yadda zatayi domin bukata ta biya.
Zakiyya tana cikin kuka mota kayansu yayi faci fitowa tayi domin taga me ya faru aka doke Mata kai wani powder aka hurawa minal daga nan bata kara ganin komai ba.

Ahankali zakiyya ta fara bude idon ta amma me ganinta tayi daure a kujera likimo tayi Dan taga Wanda ya kamosu. Aiko ayush da goje suka shigo suna dariya ko a jikinsu. Tashinsu sukayi zakiyya tama kasa magana saboda tsananin mamaki kawai kuka takeyi.

Tsk.tsk.tsktsk shine abinda ayush ta maimata kamin tace my darling sister are you surprised? Zakiyya tace me muka miki ? Idan na miki wani Abu ne me yasa zaki azabtar da mai ciki? Fuskar tunani tayi kamin tace may be me cikin da cikin suma sun min laifi ne.

  Tunda muka taso kike samun duk abin da kike so, ni fa? Banida komai. Iyayenki sunfi nawa kudi kin fini Ilimi, malamai suna sonki, Kin Sami farouq,kin Sami yazeed,kin Sami kudi,nayi kokarin rushe farin cikinki amma a banza.

Ba kashe farouq,na tabaki da yazeed, na koma boutiques dinki,nayi abubuwa da yawa aciki harda hatsarin yazeed amma me yanzu ma kin samu wani miji ga kina rike da mukamin da nakeso kinga dole ne na salwantar dake. Idan har bazan Sami abu ba toh babu Wanda ya isa ya samu.

Ke kuma, ta naushi bakin minal sai jini, kece dadi miji ko? Kowani lokaci kiuita like masa toh yau ne na karshe. Doke kan minal tayi da sanda take ta sume sannan ta dauko garin dake cikin shantun ta raba biyu kamar yadda boka mugu ya umarce ta.

Rabi ta zuba a tulun yayinda ta barbarda Rabin a tsakiyar kan minal Rabin kuma ta zuba a shantun ta jijjiga sai ta fasa. Sannan ta taka da kafar hagu. Kallon zakiyya tayi tace bakiyi mamaki ba Dana barki kike gani? Nayi haka ne domin kisan abinda ke wakana saide bazaki iya yin komai akai ba, Wannan shine hukuncin ki.

Yanzu haka your dearest mom tabi duniya don yanda na fasa shantun nan haka kwakwalwarta ta rushe sannan kishiyarki zata manta komai, zata dawo kamar yanzu aka haifeta. Kowa zai manta da ita banda ke da ni da mijina da boka na da.........

Kofa ne ya bude sai ga mummy (maman zakiyya) ta shigo, zaro ido zakiyya tayi hawayen dake zubowa a idon ta suka tsaya cak tace mummy dama baki mutu ba, colin samun Kwarin guiwa tace mummy help us ayush ta haukace,ni ban San wannan ba mummy ba ayush din my bace. Zama mummy tayi yayinda ayush ta rungume ta tana fadin mummy saura kiris kiyi missing kuwa.

Bakin zakiyya na rawa tace tare kuke aiki ? Mummy tace what do you expect?look young lady idan ma baki sani ba ki sani ayush ce kadai yata ke da yayarki a gidan marayu na dauko ku meaning  maman su safwan ma is not your biological sister that is you are all alone.

Zakiyya tace mummy me yasa zakiyi min haka? Mummy zakiyyan ki ne fa! Mummy...... yatsa mummy ta daura Mata a baki tace ya isa please no complaints. Riko hannun ayush tayi tace baby go ahead. Wani allura suka soka Mata a take ta zama paralyzed.

Mummy tace dont forget after three three months zakina yin wani okay? Tace okay mummy. Ya batun gidan anyi settling komai ? Tace yes nasa anyi photoshopping pictures din the guy is an American so ya iya aikinshi sannan umma hani ma bazata iya musa duk wani Abu da zamu ce ba tunda boka yayi mana maganin bakin ta.

Ayush tace wow mama na you are too great wallahi,naga pictures din. Nuna Mata tayi tace wow bazaka tana cewa hada hotunannan akayi ba. Tunba wannan da muke yara ba. Let's hurry up mu kama hanyan Abuja nasan yazeed ma I mean bro yazeed ya suma already muje kamin ya tashi.

Dariya mommy tayi tace sh*giyar yarinya wai bro yazeed kamar da gaske, suka fashe da dariya. Zakiyya tana gani kuma tana ji amma banda ƙyafta ido babu abinda zata iya yi.
Ko hawaye saide idonta su ciko. Wheel chair suka daura ta goje ya turata ya fitar da ita. Sannan suka fitar da minal ma.
Dadai maraba gaban karo international market suka yarda minal suka barta kwance Shabe shabe kamar macacciya..........

IS ANOTHER UPDATE

KOWACCE TA TOFA ALBARKACIN BAKINTA.

KUN TABA TSAMMANIN AYUSH CE MUNAFUKAR?

YA ZATA KAYA NE WAI? INA TSIMAYIN COMMENTS DINKU.

KARKU MANTA KUYI VOTING SHARING SANNAN KUYI FOLLOWING DINA miss_untichlobanty

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU

Miss Untichlobanty 💕

14th March,2020

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top