CHAPTER 76

RECAP

Back up na 20 cars aka aiko ma yan sanda yayinda sojoji ma suka karo back up, kaucewa mutane suka fara yi Dan sunga fadan yafi karfinsu. Shugaban yansanda na lokacin ne ya zo shima sai ga shugaban sojoji ma .
Cikin isa shugaban yan sanda yazo ya danko hannun yazeed wai zai wullashi a mota minal tayi kukan kura ta raba hannun su tare da cin kwalarsa ta yarfa masa Mari 3 masu kyau. Sama yan sanda suka harba tare da saita ta da bindigogi amma ko gezau batayi ba sojoji ma suka harbi sama suka saita shugaban yan sandan sukace ana taba minal sunanshi sorry.

Huci minal keyi tare da kara matse damkar da tayi masa har yana ƙaƙarin amai , kawai wani Dan sanda mai rawan kai ya saita ta tauuuuu! Kakeji.

CONTINUATION

Shiru wajen yayi tsit kowa yana register din abinda ya faru.
Faduwa minal tayi akan guiwanta tare da rike hannunta da aka harba. AI nan kakejin dau!dau! An sakewa Dan sandan nan bullet biyu a hannu.

Nan fa shugaban nafdac ya fara hadiya yawu tare da kokarin zamewa ya gudu, wabi cacuma sojoji suka masa sukace ko ya fadi gaskiya ko yaji ba kyau. Tsilli tsilli yayi da ido Dan yaga mutuwa a gabansa. Nan fa ya fara in ina,wani soja me zafin rai me suna musa ya gwabje sa da bindiga atake ya soma bayani cewa kudi aka biyasa ya fadi hakan.
Akace wa ya biyasa yace Alhaji tukur gadon kaya ne. Nan take ya basu registration number tare da bada hakuri yazeed yace ai dole a tsigeshi nan fa ido ya Rena fata m, haka ya dinga bada hakuri yana nuna nadamar da yayi sanda yazeed ya tabbata ya wahala yace yaji ya tafi zaiyi tunani amma fa hakan batayi wa Musa dadi ba Dan haka yasa shi lungu ya dan jijjibgesa ya sauya masa halitta kamin ya barsa.

Asibiti aka kai minal da Dan sandan nan jina jina nanfa magana ta lafa, chief of police din yace a masa afuwa ba laifinsa bane na yan NAFDAC ne da sukayi musu karya kuma munafiki harda shi a ciki.

Haka dai magana ta watse aka sasanta toh anan ne mutane suka sake tada kayar baya akan a sakewa yazeed dukiyarsa.
Shugaban yan sanda yana zaune a office gadon kaya ya kirashi yace asan yadda za'ayi da mutanen nan dake zanga zanga. Nan ya Kira yan sanda 3 yace a saki teargas a wajen zanga zanga. Daya daga cikin su mai suna lieutenant sabir murya kasa kasa cikin girmamawa yace :sir! This is totally dishonest and unfair, some police are the cause of the negative views people have on us. If not for dishonesty  these people did nothing wrong, they did not temper with government property neither did they go against the law. They are just practicing a peaceful riot. To tell the truth me and my people will not participate in this (yallabai wannan fa rashin gaskiya da rashin adalci ne, wasu yan sandan su ke jawa wasu bacin suna,idan ba rashin gaskiya ba mutanen nan basu taba kayan gwamnati ba basu yi wani Abu da ya Saba doka ba, peaceful riot sukeyi Dan haka shi bazai sa yaranshi suyi ba.)

Mari chef of police din ya wankawa lieutenant sabir kuma yace yaje shi bayan kwana 3 ya dawo ya karbo dismiss letter. Yace shidai da ayi aikin rashin gaskiya dashi gara ya rasa aikinsa.

A bangaren su yazeed kuwa bayan an cirewa minal bullet din ta farfado yazeed yana bata shayi sukaji hayaniya a hall din asibiti,saukowa minal ke kokarin yi daga bed dinta yazeed ya kwantar da ita kuka ta fara masa wai tanason ta gani dan haka ya dauketa suka fito Dan sandan nanne suke cakwakiya da sojoji zasu tafi dashi Dan ya harbi matar oga yayinda yake kuka yana fadin bashi ya harbeta ba. Yazeed yace a dakata. Tsit kowa ya yi yazeed ya iso gaban shi yace :kace ba kai ka harbeta ba? Da sauri gyada kai yazeed yace idan na gano kai ka harbeta wani hukunci zan maka yace a tsire ni.

Yazeed yace a kai bullet din da aka harbeta da kuma bullet din bingigarsa a duba su shi kuma kar a tafi dashi a mayar dashi daki aci gaba da kula dashi.
Koda aka Dubo bullet din ba na bindigar sa bane nan yazeed ya fara tunanin yadda zai gano na waye tunda yan sanda ke duba wannan kuma yan sandan ba mutuwa dashi sukeyi ba.

A kwana a tashi minal ta warke yau aka sallamo su kuma basu fadawa kowa abinda ya faru ba especially mom saboda kar hankalin ta ya tashi.
Marhaba umma hani tayi musu tare da sauran masu aikin inda sukayi musu jaje. Su nason minal sosai saboda kirkin ta.
Washe gari zabe  dan haka yazeed yace wannan shekara bazasuyi Zane ba saboda tsaro kar a kuma kawo musu hari. Sabon president yana zuwa ba tare da bata lokaci ba yasa akayi dismissing case din saboda ya gano rashin gaskiya kawai akeyi. Anan ne yazeed yayi resigning.

Mr. President yayi bakin ciki na rashin jami'i mai gaskiya da amana Dan haka ya hada masa taron bankwana a wajen taron ne aka Kira yazeed domin yayi jawabi cikin jawabin Nasa ne yake cewa zai koma ya kula da hard work din mahaifin sa kuma insha Allah  daga ranan har tashin kiyama baya fatan shi ko wani a zuri'arsa su kara involving kansu da government business kawai zasuyi kuma individually zasu dinga taimakon kasarsu ba sai sun tsunduma kansu a cikin ba idan an nemi gudun muwarsu toh zasu bayar. Idan sunga ana Abu da ya Saba doka toh zasu yi magana.

Kuka jama'a keyi wiwi! Anan taron ne akayi presenting award of excellence ma yazeed as the BEST MILITARY PERSONNEL of the year. It was a heart touching moment,box daya na tissue paper na karad saboda kuka anan ne nima aka bani award Dina as THE BEST FICTION WRITER of the year. Muka ci abinci muka sha sannan muka watse ana ma juna fatan ALKHAIRI.

Washe gari da safe suka lulu suka dawo Kaduna domin yazeed yayi shirin fara aiki as JEEMAR GROUP PRESIDENT yayinda minal taga cewa ya kamata su ciyar da almajirai domin godiya ga Allah Dan haka asabar din data kewayo ta Nemo tsofi 20 aka fara girki. Manya manyan tukunya fiye da lamba hamsin guda 20 aka daura kenan ko wacce tsohuwa 1 tukunya 1, yayinda aka biya ko wacce dubu hamsin kuma anyi haka ne Dan a taimaka ma tsofin ma.
inspection minal tazo yi yayinda take testing ana bude tukunya farfesun kaji ta hau kakarin amai. Dannewa tayi ta dandana ai take ta fara amai ba sassauci nan hankalin tsohuwa ya tashi itakam kashinta ya bushe.

Kowa ya rude ya rikice aka samo likita ta dubata tace yuzu dai she can't say amma tana suspecting ciki ne da ita dan haka aka bata pregnancy test tube aikuwa positive. Nan shagali ya karu murnane ba'a cewa komai, tun daga ranan minal batada aiki sai cin gurasa da zogale.

BAYAN WATA 7

Minal zaune akan gado ta mimmike kafa bakin nan cike da gurasa da zogale yazeed shigo ya zauna a gefenta,daura kafafun nata yayi a cinyan sa yana Mata tausa saboda sun Dan kumbura yace mummy gurasa na shirya sai tafiya turo baki tayi tace daddy zogale ka tafi dani Dan Allah yace a hakan? AI idan na kaiki can zaki wahala ne gara nan akwai mom kuma ai bakuyi hutu ba karki damu yanzu zakiga weekend din ya kewayo na sake dawowa kinji? Tace Tom shikenan Allah ya tsare ya kuma kare yace ameen.

Saukowa tayi dakyar tare da kanka kwanta me kwabon zogale yazeed ya ja kumatun ta yace nikam Allah ya tunamin ranan haihuwar ki, irin wannan ci da kike yi zaki rakanin ma kina cin zogale cikin mamul mamul da baki tace babu ruwanka. 

Fitowa sukayi tibi tibi suna dariya har ya shige mota bayan sunyi sallama ya sauko ya rungume  ta tare da kissing gurasa da zogale (cikinta) yace bye bye my little babies da big baby dariya suka fashe dashi kamin ya shige motan suka wuce yayinda minal ta koma cikin gida.

.........................

Zaune take a kan gadon dakinta yayinda take hango duk abinda ke faruwa a farfajiyan gidan, aani Luna da tafarfasa zuciyar ta keyi kamar tayi hauka haka takeji. Fincike drip din dake hannunta tayi yayinda ta yage riganta jiyoyin kanta sun tashi cikin huci tace nayi regretting aurennan da nayi auren banzan nan da nayi shi ke hannu kusantar ka masoyi na yazeed. Ke kuma sh*giya sai na hallakar dake da wannan tsiyar dake jikin ki sannan ta naushi gini Wanda har jini sanda ya fito daga hannun ta inda ta lashe tare da cewa na rantse da jinin nan sai na kasheki.

WA IYAZU BILLAH!

Toh masoyana Rabin raina, a halin yanzu dai ba baku satan amsan wacece ita. Shin a ganinku wacece ita? Duk Wanda ta canka zanyi dedicating Mata next chapter.

Me Kuke ganin zai faru a gaba?idan kika canka zan miki kyautar chapters guda 3 a jere.

Shin labarin nan yazo karshe ko da saura?

Ina tsimayi amsoshin ku. Domin inyi muku wani update yau ina bukatar 30 comments 50 votes.

Karku manta kuyi tagging kawayenku domin su karanta sannan kuyi sharing lungu da sako domin wani ma ya samu.

Karku manta kuyi following Dina @miss_untichlobanty ta haka ne zan gane masoya na, na gaskiya.

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU wato

Miss_untichlobanty 💕

11th march,2020

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top