CHAPTER 68
Inda mamaki na kashe mutum da yau yazeed ya mutu ganin yadda ya Tatar da matan nasa kasa boye farin cikinsa yayi hakan yasa ya sunbaci goshin s
Duka biyunsu saide ya lura akwai wani Abu a idon zakiyya wadda ya kasa gane alkhairi ne ko tsiya fatansa dai Allah yasa zaman lafiyan ya dore.
Su safwan ne suka rugo a guje Suna fadin daddy saura mu tare da juya masa gefen kumatun nasu. Janye jikinsa yayi Daga na matan nashi kamin ya tsuguna ya rungumesu tare da sumbatarsu. Sallama Mashkur da lukman sukayi hakan yasa minal janyo hijab dinta dake hannun kujera yayin da zakiyya tayi kitchen domin a can tabar hijab dinta. Aiko sai gata da zumbulelen hijabi.
Sakan baki yazeed yayi Dan bai gaskata abinda yake gani ba. Mashkur ne yace uhm su mai iyali manya.
Safwan ne ya lura da gaba daya hankalin shi baya Kansu gashi ya saki baki. Inda yake kalla yaji kamin yayi dariya kasa kasa yasa Hannu ya rufewa yazeed bakin tareda fadin daddy kuda zai Shiga bakin ka. Sai lokacin yazeed ya kallesu tare da Cewa muje muci abinci ko.
A tare su minal suka Shirya Komai yayinda zaliha da lukman Keta rafkawa juna harara. Min ta lura da haka.
Zakiyya ce ta fara zuba abincin. Ta zubawa su sahir da yazeed the next one Mashkur ne minal tace aunty kawo kawai. Zakiyya tace barshi in zuba. Murmushi minal tayi tace ai yanzu ma kinyi kokari kallon yazeed tayi tace kasan Cewa yau aunty zakiyya ce tayi mana girki? Yace haba shiyasa naji kamshin ya chanja. Kuce zakiyyan nawa chef ce. Kallon minal yayi da alamu maganar ta tabata kishin ya motsa yayi da zakiyya ke murmushi minal ko taci gaba da zuba abincin. Taci gaba da cewa nikam ina yiwa Allah godiya daya hada ni da mata Wanda babu yasu ga kyau ga iya girki. Nikam ban Masan wace tafi wacce ba.
Murmushi dukansu biyu su kayi. Abincin yakai baki ba laifi yayi dadi amma yasan babu macen da zata kara da minal dinshi wajen dafa abinci.
Ajiyan zuciya ya sauke yace Ashe haka dama adalcin keda wahala Idan ka yaba daya sai ka yaba dayan? Wannan shine adalci a magana. Hmm Toh faa Gaskiya da aiki a gaba na.
Minal tana isowa kan zaliha dake gefen lukman Wanda Keta dangwalarta Dan ya gano ba abinda ta tsana Kamar tsokana Dan haka ya mayar da ita abin wasa. Tace kash na manta bamu kira mom ba. Bari kawai nakai mata daki zally zuba naki ki zuba na habibin ki.
Wani kallo ta aika mata kallon Idan na kamaki Allah ya jikan ki.
Gwaliyo ta mata kamin ta dale sama abinta. Zubawa zaliha tayi badan ranta yaso ba yayi da lukman ya kashe mata ido. Aiko ta kara cika amma ba yanda ta iya sai yake takeyi.
Yazeed ma ya gano dalilin minal na yin hakan. Cinye abincinsa yayi yayi wa zakiyya alamun ta sameshi a daki.
Bayan mintuna sai gata zaunar da ita yayi a bakin gado yace my zakiyya agaskiya Nayi farincikin yadda na dawo na samu gidana yau gashi kinyi Shiga ta addini kin zama mata ta gari bakisan yadda nakeji a zuciyata ba wallahi. Na rokeki da Allah karki canja halinnan. Matsowa yayi zai sumbaceta ta kauce. Kallon yayi da alaman lafiya? Mikewa tayi tace bana sallah. Kamin ta fice. Jinjina kai yayi yace tooh? Anya kuwa?
Zakiyya ko tana fita dakinta ta fada gado ta soma kuka aranta tana fadin ka yafeni yazeed amma inaso in manta dakai. Inaso in daina sanka shiyasa bazan yarda mu dinga karfafa alakarmu ba ka yafemin. Rayuwar auren mu na Dan wani lokaci ne.
Koda minal ta dawo bata kalli Inda su zally suke ba Dan tasan sakamakon. Dakin yazeed ta nufa har ta tura kofar sai wani tunani yazo mata what if yana tare da zakiyya ne. Memakon tayi knocking Dan rashin wayo sai ta leka ganinshi tayi yana shan magani hakan yasa ta Shiga tare da warcewa da Sauri. Duba sunan maganin tayi taga bata gane ba hakan yasa ta fara karanta uses dinsa kokarin kwacewa yazeed yayi amma ya makara domin ta karanta kuma ta gane Cewa maganin rage karfin libido ne. Ranta ne ya back idonta ya kada yayi ja. Cillo masa maganin tayi tare da fadin me wannan? Kace maka me wannan ? Tuni hawaye ya fara zubowa tace haba ya yazeed me kake shirin wulla mu ciki yanzu da ace mom ne taga wannan me zata dauka? Ace kanada mata biyu amma kanashan maganin rage sha'awa. Ka taba zuwa wurina na hanaka hakkinka ne? Daga murya tayi tace NACE KA TABA ZUWA WAJENA KA NUNA KANADA BUKATA NA HANAKA? Me kakeso ka nunawa duniya yakai mijina? Shin bamukai ka kusancemu bane? abin tausayi yazeed ya Koma dan yaji kunya yadda kasan da uwarsa na masa fada. Ya matso ya riko hannunta idanunsa sun cicciko yace ba haka bane na dauka bakisan wannan abin bane ni kuma banason na kawo miki shi lokaci daya kar Nayi gaggawa. Harararsa tayi tace a da ba amma banda yanzu domin kan mage ya wa.....
Bata karashe ba yazeed ya cafkota ya hade......... Su take ta tsorata saboda yadda yake mata Dan ita batasan yadda akayi ta zake haka ba Daga zaliha ta daurata a network din yadda abin yake ko gama koya mata batayi ba sai tayi azarbabi?
Tsoro sosai taji ganin yadda yazeed ya Koma ba sai kafarta ya fara rawa ba take ta fara kukan Neman agaji sakanta yazeed yayi yace you see! Kingani ba? Ba aje ko ina ba kin tsure. Tsitstsilla ido ta fara tare da Cewa ban Shirya bane cikin in ina.
Yazeed yace okay kawai ya Shiga ban daki da gudu ta fice kirjinta na lugude cabdi anya kuwa zata iya yadda taji ance idan bakayi wasa ba in akayi first night wasu har dinki ake musu. Amma ita har yanzu abinda bata gane ba shine me takeyi har yake causing dinkin? Cabdi bari dai ta nemi shawarar zaliha. Koda ta fito a wargaje hijab a yamutse ta samu lukman na jawa zaliha kumatu yayinda take bige hannunshi. Ganin minal ta dawo yasa yayi pecking kuma tun zaliha yace Toh honey na wuce harara ta aika masa tare da fadin da na rike ka ne. Fice wa yayi yanajin dadin yadda yake tsokalarta ko ba Komai hakan ma yayi masa dadi.
Tunani ya fara yi Kamar yadda ya saba na yanda zai Sauri ayush tun sanda aka makala masa zaliha amma yau Allah da ikonsa kawai sai yaji ransa na baci. Bayason ko tunaninta yayi.
Murmushi ya saka tunowa da irin kallon da zaliha ke binshi dashi lokacin daya fito yace Gaskiya yarinyace. Kai amma fa auren yaran ma da dadi. Shege yazeed Ashe chilling yake shiyasa kullum zaka ganshi makale da matarsa.
Daki minal taja zaliha ta mata highlight akan abinda ya fara bawai dalla Dalla ba sannan ta tambayi ya zatayi? Janyo kunnanta zaliha tayi ta rada mata wani Abu zaro ido minal tayi tace anya zan iya? Zally tace Ras ma kuwa saide in baki gwada ba.
Hararta minal tayi tace shegiya sai Sanin sirrin kula da miki amma ba'a aiki dashi. Kinyi asara, ni ba wannan bama Wai a ina like Sanin abubuwan nan ne? Zaliha tace mutum da salularsa a WhatsApp mana a irin groups hakannan kinsan sai kaga dama zakayi misusing phone. Kinsman wasu su suke jawa Kansu duk abinda ya samesu. Minal tayi ajiyan zuciya tare da Cewa hakane Nide ki hada lambata a lintsima ni Dan baza'ayi babu ni ba. Zaliha tace angama matar oga. Dariya su kayi kamin suka shige wata hirar.
Yazeed ko wanka yayi ya fito ya rasa yadda zaiyi da ransa rana zafi inuwa kuna.
Bayan sallar isha'i zakiyya ta hada golden morn tana sha yazeed ya Shigo. Ajiyewa tayi agun ta haura sama abinta shikam kallo ma yake binta dashi. Dakinshi ya wuce abinsa koda yaje Abu yagani cikin bargonsa karasawa yayi yaga minal ce ke bacci tabe baki yayi yace uhm matsoraciya kawai.
Wanka yayi abinsa ya Shirya kamin ya kunna game yana bugawa abinsa. Tashi juyi tayi hakan yasa bargon yadan zame taga Ashe bra ne ajikinta take ya juya kai tare da Cewa kul yazeed barta tadan huta zuwa ka dawo Daga mission dinka wata zuciyar tace amma kai sai ka cutu ? Yana cikin wannan zazzafar muhawara da zuciyarsa minal ta bude ido gashi tayi ta zauna kawai ta ganta ba kaya ihu ta kwalla ai super daya yayi yasa Hannu ya toshe mata baki yace ke lafiyarki kuwa? Zazzare ido tayi ganin Daga shi sai boxers itama kusan yanayi daya suke amma Idan zata tuna ai da kaya ta Shiga dakinnan kamin bacci ya kwasheta kallon window tayi taga duhu hakan yasa ta fincike hannun yazeed tayi saurin dauka tare da fadin waiyo banyi sallah ba. Kunya ne ya kamata tayi saurin shigewa toilet tare da yin dahara sannan tayi alwala. Bath robe ta saka kamin ta fito domin ta gano na kowa ya sheka mata tsiyarnan ba illa zaliha kuma zata rama.
Kayanta ta dauka ta Shirya kamin tayi sallah. Koda ta idar kin hada ido tayi da yazeed. Murmushi yayi ya rufe laptop din Nasa kamin yazo ya tsuguna a gabanta. Sunkuyar dakai kasa tayi ya dago da fuskarta yace me na sunkuyar dakai Dan tureshi tayi a wasa tace ni kunya kake sani ki kasaka kaya.
Dariya ya kyalkale dashi yace Idan wani ya ganki zai dauka wata salihar baiwa ce nanko wani abin dakika sani koni ban sani ba.
Kwanciya tayi akirjinsa tana rufe ido da hannun ta Dan dariya yakeyi mata yana shafa kanta. Cikin shagwaba tace Dan Allah ka dena ni kunya kake sani ji. Cakulkuli ya fara mata tun tana nokewa har ta fara dariya. Cakulkulin itama ta masa kamin ta mike da gudu nanfa suka fara guje guje pillow ta dauko tana kwala mai tare da Cewa banaso aiko kaimi ya kara wajen yi mata cakulkuli tana fading waiyo zanyi fitsari cikina. Shikam dariya yaketa yi. Dukansa ta fara yi dakyau da pillown shima ya dauko wani Daga nan aka Koma pillow fight abin dai gwanin ban sha'awa sanda suka faffasa pillown gaba daya dama guda 4 ne yazeed daya kalli dakin yaga yadda ya wargaje saboda wayo yace uhm bari inje in yin kallon mikewa yayi zai gudu tayi saurin cafko wandonsa ta janyosa tare da saurin rude koda tace babu Inda zaka sai Mun gyara dakinnan. Fuskar abin tausayi yayi mata taja hancinsa tace oga babu wannan maganar fa. Nanfa suka dukufa ka'in dana'in suka gyara dakin. Sai haki suke yazeed ya baje a gado. Minal ta dauko takarda ita ma ta fada gado jagab. Miko masa takaddar tayi yace haba uwar karatu ai ma huta na yau ko bakiga yadda Muka gaji bane. Jinjina kai minal tayi alamar yadda Dan itama dama ta gaji tace ya batun tausar fa yace barshi kawai shima. Murmushi tamai ta rungumesa kamin ta kwanta a wurinta. Tace Saida safe yazzy baby. Matsowa yayi yace ke madam tashi.
Zama tayi yace akwai matsala tace name fa? Yace ni bana iya bacci Idan babu pillow tace Toh bari in dauko ma a daki na ta fadi hakan tana kokarin sauka Dan ta dauka da gaske yake. Riko hannunta yayi yana mata wani munafikin murmushi yace haba mutuniyata ace duk aikinnan da kikayi kuma sai na baki wahalan dauko mina pillow? Zo ki kwanta abinki tace Toh ya zakayi kayi Baccin? Yace kwanta kede ki gani tana kwanciya ya kwanta a kirjinta dariya tayi tace zama kayi bayani. Da ka fadi kanka tsaye kace kanaso ka kwanta a jikina ba ka tsaya noke noke ba. Murmushi kawai yayi Kamin yace Allah ya miki albarka tace Ameen da alamu bacci na Neman saceta. Hannunsa ya daura a cikinta yace my minal inama ace yanzu haka akwai Dan Babyn mu acikinki mu rayu dukanmu harda su auntynki cikin farin ciki Dan dariya yayi idonsa fal da kwalla domin yana matukar son ya samu haihuwa yace ace Ku haihu rana daya kuma Ku haifi Yan uku uku. Jin shiru bata kwafso masa wani kwaba ba yasa ya kalli fuskarta yaga ai tana wani duniyan sumbatar ta yayi kamin ya kwanta bayan ya musu addu'a yana Rokan Allah ubangiji ya azurtashi da yaransa na kansa.
Kiyi hakuri nace zan muku update jiya kuka mini shiru afwan banida lafiya ne Kamar yadda wasunku suka sani amma yanzu dai na samu sauki kuma da izinin Allah jibi zan muku update.
Longest chapter ever Dan haka nima inason sweetest comments
Don't forget to vote as well.
Love you all😘
Miss untichlobanty💕
22 January, 2020
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top