CHAPTER 64

Koda suka shigo gidan zaliha na kokarin fita Daga motan luku ya riko hannunta kyam wani yar sukaji amma bai saka ba saima harara daya banka mata. Kiciniyar takeson masa ya mata rikon maza mom Suna fita ya zama saura su biyu ya lafta lock. Wancalar da hannunta yayi yace Menene ma wannan tsiyar hannun naki Kamar muruci? Tsaki taja tareda fadin dalla malam budemin mota na fita.
Banson wulakanci baza'a kwana a gidan naka ba ana dole ne?

Take motar yayi Wanda yayi sanadiyyar da yasa zaliha fasa baki tare da Kwandale kai a window kicin kicin tayi da ido kamin tace kane bala'i na rantse da Girman wallahi Bashi Idan ba saina rama ba me nake.

Daidai lokacin suka iso Dan haka ya fice yana fito kallon part dinsu zaliha ta tsaya yi ba karya ya hadu. Ko nasu minal saide ya Nuna musu girma da tsadan kayan furniture amma saboda hali irin nata tabe Baki tayi tare da fadin saboda wannan tsiyar gidan aka raboni Dana iyayena.

Shrugging yayi yace Aike rayuwarki tsiya tsiya ne iyayenki ne kawai na arziki.

Tsabar tsiya sadakarki aka bani kuma na kawoki matsiyacin gida zaki kare matsiyacin rayuwarki acikinsa tareda matsiyacin mijinki. Ya fadi hakan yana mai mata murmushi.
Iya shaka kam ta shaka kuka ta fara tare da fadin Allah ya isa na nikam an cuceni wallahi da aurenka gara Lauren kolo. Wannanta wuce bazar bazar ta mangajeshi ta fada wani Daki yace jeki dama nanne dakinki. Leka dakin yayi ya ganta kwance kan gado tana kuka yace my wife dagowa tayi tana aiko masa wani harara kiss yayi blowing  Mata tare da cewa kayanki na wardrobe ayi kuka lafiya sannan ya fashe da dariya. Tasowa tayi kamar zakanya. Yayi saurin rufe Mata kofa dadai zai fita daga side dinsu yaga minal tana shirin shigowa hannunta rike da sahir da safwan....

🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀

Su minal suna Shiga gidan su suka labe suna kallon abinda su zaliha keyi dafe kai yazeed yayi yace gosh wai ace bazasu taba yin shiri ba ? Dole ne mu hada kansu. Miko Mata hannu yayi yace plan karba tayi sukayi musabaha tace yes plan.

Daughter! Daughter! Mom ke kwalawa minal Kira tana fadin zoo ki tayani kunce kayana in baki tsarabarki. Zata tafi yazeed yayi saurin rokita kamin tace mom zatazo anjima yanzu ina bukatar matata.

Lekowa tayi ta sama tace iyeeee mai mata manya. Umm Nide kada ka riketa dayawa yafi awa daya Dan yunwa mukeji kuma abincinta mukeso. Zaro ido yayi yace mom bafa haka nake nufi ba magana zamuyi fa sai in danji duminta. Dariya mom tayi tace zama kayi bayani Nide na fada maka.

Sannan ta Koma tana mai jinjina halin rashin kunyan yazeed don atunaninta wani abar za'ayi.

Yazeed ko minal yaja zuwa kitchen wadda duk kunya ya rufeta saboda ganin da mom ke mata.
Fuskar yara ya mata yace babe kiyimana pancake dinki muci please.
Gyada kai tayi ta fara hado abubuwa sai murmushin jin kunya take yazeed ko daya hau kan island ya zauna tareda dauko wayarsa yanata daukar  hotonta tana aiki saide duka fuskarta bai fito ba.

Ajiyan zuciya yake sauke wa yawunshi har tsinkewa yake yace kai nikam ataimaka min na fara cin nawa. Zuba mai tayi ta bashi zata Koma taci gaba da suya ya riko hannunta cikin shagwaba yace ni kibani a baki.

Hannu tasa ta taba goshinsa da wuyarsa ba zafi. Yace yadai tace na dauka bakada lafiya ne naga kana Abu Kamar baby. Yace aini Babyn ki ne kashe gas cooker din tayi ta dawo ta zauna a gefensa bayan ta dauko juice da honey da lemon. Tace da wanne kakeson honey ko lemon yace lemon dinde saboda tsami tsami.

Haka tayi ta bashi sunaci Suna hada plan din yadda zasu hada kan su zaliha da lukman da kuma yadda zasu gudanar da bikin su Abubakar Dan sun dano taragonsu.

Saide kash bansamu Dakar mina  abinda suke Cewa ba saboda ina can ina satar pancake dan  Nasan ko na tamabaya yazeed bazai bani ba tsabar santi Dan naji lokacin dayake Cewa in so samune minal ta bashi duka pancake din sai ta dafawa su mom wani abincin.

Bayan sun gama ci cikin raha da kaunar juna. Yazeed yace kai kullum sai kiyimin irinsa har iya tsawon rayuwar mu. Kuma duk ranan da banci Shiva Toh ko me naci saide inci Dan yunwa. Girkinki na daban ne masoyiya. Hugging dinshi tayi tace Insha Allah kullum zannayi maka girki kuma duk ranan da ban Daga ma abinci da hanuna ba Toh ko wa na dafawa aikin banza ne.

Karashe aikinta tayi yazeed ya tayata jera dining table.
Kowa sai Santi yake sahir Dan taurinkai tasowa yayi ya rike hannun yazeed yace daddy I am sorry I called you a bad daddy you are the best daddy because you married the best aunty who can cook the best pancake.(baba kayi hakuri nacema kai ba ubanl na gari bane. Kai din uba na gari ne daya a cikin miliyan saboda auro aunty wacca tafi kowa kuma ta iya soya pancake dayafi ko wanne dadi.) Shafa kanshi yazeed yayi yace is okay my boy. Wajen minal yaje yace aunty will you be my friend?(aunty shin zaki zama kawata?) Daga kai tayi tana murmushi tace yes peck ya mata a kumatu sannan ya hau cinyanta ya zauna bayan ya janyo abincinsa gabanta yace ita zata bashi yazeed yace my boy ka girma fa karka balla min aunty.

Safwan ne ya taso yazo wajen yazeed yana turo baki yace am I not your boy? (Ni ba yaronka bane?) Yazeed yace yes your are my dearest son(eh kai danane da nakeda kusanci dashi). Gwaliyo sahir ya masa. Kallon minal safwan din yayi tace masa karka damu kai amini nane ba abokina bama. Din buro fuska sahir dake cinyanta yayi tace sorry sahir karkayi kuka kaima amininane.

Bayan sun gama cin abincin ne minal tacewa yazeed tanaso taje gidan zaliha yace taje no problem.

Fita tayi yazeed yace ta tsaya a kaita a kafa tace ba damuwa zataje da kafa saboda exercise.

Riko hannun su tayi tiryan tiryan Suna tace Suna hira kankace me sun saba Idan ka gansu zaka dauka ita ta Haifa abin gwanin ban sha'awa. Dukda ko Cewa sahir ya nuna rashin kauna a gareta da farko bata nuna Mara waraiya ba kuma ai ko ba Komai ya nemi yafiya sannan yaro ne shekarunsa 7 ne kawai.

Abakin kofa ta hadu da lukman suka gaisa yake tambayarta ko yazeed yananan tace yananan.
Yace Toh tayi masa alfarma ta lallashi kawarta. A tsorace tace me ya sameta yace sabani Muna samu kamin ya wuce su safwan suka bishi da kallon rashin fahimta. Sahir yace safwan kasan menene ma'anan sabani?girgiza kai yayi yace kai da ka jirmeni ma Baja cani ba balle ni.

Minal ne tace shh bakyau sa ido kunji ? Chocolates ta dauko a jakanta ta basu sannan ta kunna musu TV already an hada tace suyi kallo zata he wajen matar uncle lukman. Zaro ido sahir yayi yace dama aunty baka matar uncle lukman ne? Minal tace aunty baka kuma? Ka dena fadan haka kaji ai baki da fari duk Allah ne yayi mu babu Wanda yafi wani sai Wanda yafi jin tsoransa. Yace Insha bazan kara fadaba amma Gaskiya bakinta dayawa ne ysoro ma take bani. Dariya minal tayi tace karka damu zata Baku sweet. Kaima safwan kaji me nace ko? Yace dama ni bana fada kuma kawatace tun a hospital Dana ganta.

Shiga dakin minal tayi ta sameta tana kuka tace kai zally me haka? Kuka sai kace yarinya ? Idan ma aurenne bakyaso kin kaini ne. Nifa a shashanci na ko mijin ban saniba ma. Dukda banyi nadaman yadda da aurensa ba amma ai sanda na wahalu tukun naji dadi ba gashi yanzu ya wuce ba? Karki damu bari in baki sirrin da zaki sato zuciyarshi da wuri.

Ki tabbata kuna samun body contact koda kuwa kuna fadane hakan ne zaisa ya saba da jikinki yadda duk ranarda baiji dumin fatarki ba zaiji Kamar bayida lafiya Daga nan zaku saba da juna with time har Ku fara lobaiya.
Zaliha tace ni rabu dani waddannan shirmen se ta kaddar Hausa ko film din India. Minal tace yo ke da kike karanta takaddun hausar kenan.

Bari kiji ni shaidace akan wannan ina miki magana ne with experience. Hararar wasa zaliha ta mata tace shegiya kawata nifa banason karyar turanci minal tace dalla tafi can yanzu kin isa ki nunan iya turanci. Zaliha tace Allah baki zanyi tunani akan shawararki. Minal tace ke kikajiyo kinsman dai ba rabuwa zakuyi ba Dan haka gara ki fara action da wuri ko duminsa kidan dinga ji. Dariya suka fashe dashi zaliha kai shegiya kwata kefa yar bara ub*ce da dukum kike ba abinda kika sani ko Dan 10yrs yafi ki sanin harkannan yaushe kika zama yar Hannu ne. Duka minal ta daka mata tace banson ashar ke matsalata dake kenan. Zally tace kinga ni muje muyi yama sunan abin matan manya ? Minal tace me ?zaliha bude ido ta turanci. Dariya minal tayi tace tourism? Zaliha tace shi nake nufi Daga mu dafo abinci. Fita sukayi suka Duba ko ina sunata yaba Kyan gidan suka Duba kitchen akwai Kayan abinci Kamar na sati. Taliya suka daura sannan suka wuce parlour minal tace kawas canjo Maya muyi photon randa kika tare gidanki ko ba haka ba ? dariya zaliha tayi kamin ta wuce zata Shiga zaki minal tace tsafta na kara dankon abin.... Kin gane ai. Zaliha tayi murmushi ta shige tasan love minal kesan Cewa amma saboda su sahir na wajen yasa ta fake.

Bayan ta Shirya cikin Riga da wando hotuna suka sha abinsu sunyi kyau sosai domin minal ma Rolling gyale tayi.

Idan naga comments daya wa Toh za'a sami update dayawa.

Ina kaunarku sosai😘
Takuce karamarsu babbarsu

Don Allah kuyi voting

miss untichlobanty💕

14th January, 2020

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top