CHAPTER 58
Saukowa minal tayi cikin navy blue Arabian gown. Murmushi take sakewa yazeed harta iso Inda yake zaune ta tsuguna tareda fadin sannu da zuwa sannan ta dauki office bag dinshi zata juya tana fadin zo muje kasha ruwa ka Shirya ko bak.....? bata karasa Ba yazeed ya finciko ta ta fado jikinsa turo baki tayi tareda fadin kaga ka batamin kwalliyata ko?dariya yadanyi tareda Cewa ina kwalliyar Anan ji yadda kika lafta man baki.
Tace kana nufin banyi kyau Ba?yace wa ni na isa?irin wannan kyau dakikayi ai ko Amarya kawai dai kin tunamin da ranan dana fara ganinki. Turo baki tayi tace shine kukayita min dariya ko? Shafa bayanta yazeed ya fara tareda fadin Kiyi hakuri baby na lokacin ai bansanki Ba.
Kuka ta fara bilhakki da Gaskiya harda shessheka tace shine kuma....kuma ranan da na Shiga motarka...ka..kaci zalina a gidannan har ciwo kaji min. Serious face yasa tare da gyara zama mai kyau sannan itama ya gyarata sosai akan cinyarsa murya kasa kasa abin tausayi Kamar wani maraya yace Kiyi hakuri MINAL dina kinsan kuskure ne da Bacin rai sannan kuma da rashin sani amma Nayi miki alkawari Indai ina cikin haiyaci bazan kara cin zarafinki Ba tace kuma har lebena ka dalle Mun😭 yace na tuba please tareda hada hannaye. Hannun Nasa ta riko tare da turo baki da alamu zata fara shagwaba ne tace to na yafe maka amma da sharadi.
Zaro ido yayi yace yafiyan ma sai an kara min sharadi?yace toh ko bakaso a yafe ne? Yace a ah Ba haka nake nufi Ba inajin wannan sharadin.
Janyo kunnansa tayi tace tashimuje daki ka Shirya sai.......
Yace ehm sai me?gyaggyara tayi ta kwala masa ihun SAI MUJE KACI SINASIR! Sannan ta diba a guje Yazeed har wani zuuut yaji a kunnansa tashi yayi hannunsa daya kan kunnansa yana fadin yau kin Shiga uku a hannuna.
Dakin ya bita ya samu tana hada masa ruwan wanka.
Ban dakin ya Shiga bayan ya ajiye jakankasa aiko tana ganinsa ta bude baki zata kwalla ihu ya hade bakinsu.
Mukut! Ta hadiye ihunta tare dayin lamoo a jikinsa. Murmushi yayi aiko ya fara mata cakulkuli. Dariya take kyalkyalawa tana bashi hakuri shima sai dariya yake mata yana fadin zaki kara min ihu a kunne?tana dariya harda hawaye take fadin ban karawa waiyo Allah cikina,kayi hakuri bazan kara Ba.
Garin shure shure ta bige makunnin shower nan ruwa ya musu sharkaf.
Dakyar yazeed ya lalumo ya kashe saboda karfin ruwan guduwa zatayi ya janyota jikinsa tareda fadin ai baki isa ki shigar min daki a haka Ba. Tace to kaima a jike kake ai yace dama ni wanka zanyi kinga sai mutu tare ko😉?
Girgiza kai tayi tace a ah fa ni iskanci na baikai nan Ba. Yazeed yace hmmm to ai sai ki jira inyi wankan in dauko miki kaya ta Daga kai alamun Toh.
Hannu yasa a ruwan tunda bata tana hada masa Ba yasanyi.
Kallonta yayi yace irin wannan sanyin ruwa haka. Tace to ai ni banga famfon ruwan zafin bane kuma famfo kawai na iya budewa ban iya aiki da sauran abubuwannan ba. Yace zo kigani Toh. Matsowa tayi nan ya gwada mata suka controls din jacuzzi din tare da aiyukansu sannan yace ga Inda zaki dinga ganin temperature din ruwan kuma ni ina wanka a 40°C. Gyara kai tayi yace good yanzu kunna Inda zai dumama ruwanda kika zuba Daga famfo.
Kunnawa tayi tana monitoring temperature din ruwan yana zuwa 40°c ta kashe yace give me five suka tafa yace my baby minal Ashe kanki yanaja. Tace ka dauka ni din wasa ce? Yace ko kadan kayanshi ya fara cirewa minal ta juya fuskannan yayi ja saboda kunya. Murmushi kawai yayi ya Shiga Ba tareda ya rufe glass dinba.
Dan karkarwa kadan yaga tanayi yace baby minal?tace na'am yace bude drawer din can ki dauko min turaren wanka na. Toh tace taje Inda ya fada mata ta fara dauko abubuwa tana shinshina har ta sami mai kamshin turare ta dauko ta dawo Inda take dazu sannan ta miko masa.
Yace kinmin nisa ai yana smirking Dan shi yasan me ya Shirya mata. Matsowa ta sakeyi tare da mikowa aiko ya cafkota ya janyota findummm! sai acikin ruwan.
Bata fuska tayi tana hararan yazeed yaja hancinta aiko ta fara dukansa.
Hakuri ya fara bata yana dariya. Batasan me yabi ta manya Ba sai tsintar kanta tayi tana mai core kayanta itama yazama Daga ita sai bra pant.
Ruwa ta fara watsawa yazeed tana fadin tunda so kake Nayi wanka dakai bari in haka ruwa.
Funcikota yayi shi zai bata ruwan tace waiyo Allah kayi hakuri aradu ban iya linkaya Ba. Yace me kuma linkaya?
Tace iya ruwa mana yace kina nufin swimming? Tace nima bansan sunanshi ta turanci Ba yace swimming ne. Oya say swimming tace smimming Jan kumatunta yayi yace swimming Ba smimming ba. Tace swim..ming? Yace hmm swimming. Tace swimming yace clap for your self. Tafawa tayi YAZEED yace kinason ki koyi swimming ta Daga kai yace to zan koya miki kinji ta sake Daga kai.
Nan yazeed ya fara koya mata sunayen abubuwan da yake toilet din. Sanda aka zo kan jacuzzi, kasa fada tayi Daga karshe aka barta akan jazuki.
Koda sukayi wankan yazeed ya dauko musu bathrobe guda biyu ita ya mata burgujeje saboda Ba size dinta bane dariya yazeed ya dinga mata yace muje daki inyi mana ordern couples bathrobe ko?tace menene couple kuma yace mata da miji.
Fitowa sukayi minal ta nufi dakinta ta bude wardrobe dinta tana nazarin wani kaya ya dace tasa sai ga yazeed ya shigo zuwa yayi ya fara hura mata iska a gefen wuyanta ta Dan zabura tare da fadin har kaban tsoro yace maganin mai Baron kofa a bude.
Kamo hannunta yayi ya zaunar da ita sannan ya dibi wasu kaya Daga cikin nata. Wani Riga ya miki mata me hotan lulu Katy yace tasa yana zuwa sannan ya nufi dakinshi kayanta ya jera a gefen nashi na hanging yayi hanging dinsu sannan ya dawo ya Dino Nashan iska da bacci ya zamu harta Shirya tana shirin fesa turare.
Zuwa yayi ya karba shinshina sannan ya ajiye ta kalleshi alamun lafiya girgiza kai yayi tare da fadin karki shaka wannan kisa Wanda kike sawa kullum.
Dan zaro ido tayi tace ya akayi kasan kamshin turarena ? Matsowa yayi yaja hancinta tare da fadin shinshinar ki nakeyi duk sanda kikazo kusa dani😉 gwaliyo tamai tace ai nima Nasan kamshinka yace hmm you are not as innocent as you act tace meh? yace babu.
Shafa turarenda da take shafawa tayi dama innace ta bata. Dakin yazeed suka nufa yace da fatan kin Shirya?tace na me fa? Yace muje zaki gani.
Zaunar da ita yayi a bakin gadonsa sannan yaje gaban madubi ya janyota drawer dozen din 60leaves da kwalin bairo ya dauko ya mikawa minal yana murmushi yace dazu na siyo miki wannan dashi zamu dinga yin karatu.
Karba tayi tana Washe baki tare da jin dadi ta rungume yazeed tana fadin waiyo yazzy baby na na gode yanzu nima zan iya karatu. Sakeshi tayi tare da fara tsalle a tsakiyar gadon tana fadin yay! Nima zanyi ilimi zaliha sai kin iso!zaliha sai kin iso !
Yazeed ne ya rikota tareda da fadin ke madam zaki kara Mani gado bakisan kin girma bane yar lukuta dake. Hararansa ta farayi yayinda dariyar nan ta dauke. Kicin kicin tayi da ido tareda fadin nice yar lukutar? A tsorace yazeed ya girgiza kai Kamar da haske tareda fadin Ba haka nake nufi Ba.
Tunkaroshi ta farayi Kamar zakanya yayinda yake baya yana Daga hannu alamun yayi surrender.
Ganin ta hayaiyako ta iyo kansa yasa ya arce a guje. Nan fa suka fara nuna fasaha da kwarewa wajen iya gudu. Sanda suka wargaza dakin kaf kamin minal can ta tsaya tana haki tareda fadin na hakura ka tsaya.
Zuwa wajenta yazeed yayi shima yana haki. Ruwa ya dauko musu a fridge din dakinshi sannan yace ai sai mu gyara dakin ko?minal tace Toh tana kokarin saita numfashinta.
Bayan sun gyara minal ta dauko takarda daya da bairo daya sannan ta ajiye sauran. Zama yazeed yayi tareda Cewa mu fara ko?murmushi take sake masa yace hajiya lafiya dai ko?ko bakyason karatunne?
Pillown da take boyewa a bayan ta ta fara dukan yazeed dashi tana fadin ancema na hakura ne? zaka kama ka kirani yar lukuta?dauko pillow shima yayi nan suka cigaba da jifan Muna da pillow kamin ta fara yiwa yazeed cakulkuli tana Cewa ya kaji abun? Dariya yazeed yake yana Cewa Kiyi hakuri,na tuba,bazan kara Ba,waiyo cikina,cikina fitsari nakeji.
Dariya ta fashe dashi shima yazeed din dariya yaci gaba dayi. Sanda dariyan ya lafa yazeed yace maza ki matso muyi karatu. Tace fitsarin fa? Tana dariya kasa kasa yace ai na fada ne Dan Nayi escape.
Matsowa tayi tace amma fa yunwa nakeji yace muje muci Toh Dan nima yunwan nakeji.
Abincin sukaje sukaci yazeed sai Santi yakeyi Anan yake ce mata ai bai taba cin abincin dayake mai dadi Kamar nata Ba. Sannan Gobe tayi abinci dayawa Dan su mom da Dr Mashkur zasuzo. Dadi ta dinga ji har yazeed yana mamakin yaushe suka saba har haka.
(Dan wasu matan da ance surukarsu zatazo Kamar ance mutuwanta zaizo. Wasu ma ko auren mutum basayi Idan uwarshi tana Raye sai kaji Suna "da fatan dai bashida hawan jini" Wai sirikarce hawan jini! Allah dai ya kyauta ya ganar damu amma lamarinku akwai gyara.)
Jinshi kawai takeyi Dan tasan yana cikin sinasir ne kawai. Wai bai tabacin abinci mai dadin shi Ba.
Tace yazzy baby, yace umm? Dan bakinshi ya cika da abinci. Tace wani abinci kafiso ne yace eh Toh ada dai pancake ne amma a yanzu tuwo ne.
Dariya tayi tace aiko kaci sa'a na iya pancake Dan aunty fauziyya tana sonshi sosai.
Yazeed yace Toh kimin gobe. Ma'ke kafada tayi yace please tace nope yace pleeaase! Ta sake Cewa nooo turo baki yayi Kamar zaiyi kuka tace fine zanyi. Murmushi yayi yace iye my baby kin lura da Cewa kin fara sirka English word acikin Hausa kuwa?dadi ta fara ji ya miki mata hannun hagu suka gaisa yana fadin congratulations baby! Murmushi tayi tace thank you, yace you are welcome. Shiru tayi yace my pleasure zakice ta gyada kai.
Abincinsu suka cinye cikin jin dadi sannan suka Koma daki.....
Kinga sister murmushi ya isa haka kar bakinki yayi ciwo😜
Yau no dogon surutu kawai I love you wujiga wujiga. Duk wacce batayi commenting da voting kuma ta karanta itace ma'kiyiyar su yazeed dinnan. Thank goodness its not my handwriting😶
One more thing; NEXT UPDATE BA CHAPTER BANE QUESTIONS AND ANSWERS NE. ZAKU TAMBAYI CHARACTERS DIN TAMBAYOYI A COMMENT SECTION SAI IN ANSWER MUKU A NEXT UPDATE HOPE KUN GANE ABINDA NAKE NUFI? SANNAN ZAKU IYA TAMBAYANSU KOME KUKESO.
CHARACTERS DA ZAKU TAMBAYA SUNE KAMAR HAKA:
1. Yazeed
2. Minal
3.zakiyya
4.zaliha
5.lukman
6.mom
7.inna da baba
8.dijeh
9.ya abubakar
10.Laila
11. Jamal
12.Mashkur
13. Unknown makiyiya
Da fatan zaku tambayesu ?
Takuce karamarsu babbarsu,karamar tsuntsu me babban gida.
Miss untichlobanty💕
18 December, 2019
IDAN AN SAMI TAMBAYA BIYAR YAU TO ZASU ANSWER YAU IDAN BA HAKA BA SAI GOBE
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top