CHAPTER 25

An daura auren minal da yazeed akan sadaki naira dubu 50,Yan uwa da abokan arziki NATA taya murna makiya ma na hassada

Allah ka barmana makiyanmu kodan su zama dalilin da zamuyi nasara. Imagine life without munafukai 'Allah barmana Ku Yan wuta😂'

Mom ta aiko da kayan abinci da abubuwan da za'ayi walimah Dan babu wani event da za'ayi. saboda abin yazo a kurarren lokaci ko mai wa'azi ba'a sami daman kira Ba.

Bayan la'asar akayi da mom Cewa za'a daukan minal around 5 pm inji ango(mom anya wannan magana kuwa zan yarda da ita?).

Hakan yasa aka fara shirya Amarya around 3:50 bayan Anyi sallar la'asar.

Liffaya mai kyau tasa wadda aka siyo mata awajen reemah's collection. Wani sarkan gold akasa mata Wanda yake na inna ne family necklace dinsu. Babbar ya ake bawa in za'a kaita dakin miji. Kuma ba'ayarda ka siyar Ba amma zaka iya upgrading.

Kyansa yananan Dan haka ba'amayi upgrading din Ba.

Dayawa daga cikin Yan makarantansu sunyi attending, ciki kuwa harda heedaya Muhammad da ma'ani yerima Wanda suke mutunci sosai.

Yan matan ne adakin minal yayinda aketa tsokananta itako sai cika take tana batsewa wai ita batason adinga zancen batsa a gefenta.

Hidaya ce tace Nide sake fuskannaki in gama kwalliyan yayinda ma'ani ke Cewa nikam yau sai na cika camera ta da hotuna, inajin ma inna sami dama zanje in karanta photography😉

Heedaya ne tace oh mude zamuzo muji ya aka Kare a Daren farko.

Harara minal ta ballo mata,aka fashe mata da dariya Ashe ta shaka, minal tace ko ma dai menene ni kar a tura ma kowa hoto na cikin kayan nan tunda kunga dai gashi na da wasu bangaren jiki na a bude.

zaliha tace kai Ku rabu da ita bari ayi Daren farkon wannan Cuno bakin da take duk zata dena saide muga mutumiyar ka an zama miji dadi

Alamun zatayi kuka muryanta yayi tana Cewa wallahi zaliha karki bari na kamaki shegiya yar.....

Innace ta shigo tace inkika karasa sainaci ubanki.

Tunda ake hirar bansa baki Ba ina zaune a gefe ina typing a wattpad dina saboda kar ace na fiya rashin kunya sai alokacin na sako baki nace "assha!inna kin bata goma boyar bata gyaru ba in ita batayiba aike kinyi"

Dakuwa tayimin tace ingo naki yar jakan uban yarinya da baki cau cau Kamar babba kodan kinganki cikin Yan mata shiyasa kika falle ko?kinsa niqabi kamar da gaske ashe dai.......shegiya Da I damu Kamar na Yan chaina

Kafin ta karashe nayi Sauri nace wallahi Nide Ba yar China bace ina turo baki,aiko inna tayi kaina na fita a 360 har inacin karo da mutum Ashe ma sakina ce da habiba (from the nemesis of sakina)yi hakuri kawai nace kamin na buya a zaure ina haki sannan na sauke niqabi na,na saka gilashi na.

Ciki su sakina suka Shiga aka gaggaisa kamin suka wuce domin mazajensu na jiransu.

Kanwar dad din yazeed aunty nafeesa da Umma habiba wadda take step paternal grandma ga yazeed sai kuma aunty nina Kanwarka mom Wanda suka iso yau da safe sune sukazo daukan Amarya tare da motoci 3 kacal saboda basuso bidi'an tayi yawa

Aiko nan aka fara tashin hankali minal fa da taga da gaske tafiya za'ayi da ita kirjinta ya fara lugude duk dadin da takeji taji babu shi ya tafi kawai sai ta fara hawaye wiwi Ba magana nanfa wattpad fans dinta sukayi CAA anata bata hakuri amma ina kukan karuwa yake tunba sanda sukayi sallama dasu inna Ba dasu baba da ya abubakar.

Inna da baba hawaye suke hankali kwance yayinda idanun yaya abubakar suka ciko da kwalla deeje Kam an jika gaban riga ma da hawaye da majina sai alokacin na lura da kwalliyar da tayi kominta yayi matching da kayanta hatta Jan baki da eye-shadow, da brows din duka blue ne. Abin dai sai kun gani. Nikam share kwallan da zai zubo min Nayi domin tausayi. Rabuwansu was heart touching haka aka kwashemu mu 10 aka kaimu gidan amarya.

Tundaga kofa akayi mana maraba,kai Mun sami tarba me kyau dakin zakiyya aka nuna mana muka kai minal Dan bada amana mu Yan mata 8 da tsofi 2.

Ba yabo ba fallasa ta karbemu. Amma ni dai hankalina bai kwanta ba kuma naga alamun hakan a fiskan wasu daga cikin mu amma dai sai Nayi shiru. Kar aji mutuwan sarki a bakina.

nuna mana dakin minal akayi Wanda yake part din baki ne na sama kuma acikin sashin zakiyya yake ada amma an daba kuma an gyarashi kai ya hadu. Allah dai ya kyauta ya Kare Daga sharrin makiya

Aikuwa hidaya ta cika alkawari Dan photo kam gida yashashi har minal dinma sanda akayi mata pic amma sanda ta sake ado tukunnan.


Haka dai har dare yayi munata shewa da tadi kamin aunty Nina ta shigo tace mana motocin tafiya najiran mu haka Muka tattari kafufun muka tafi minal Kam kukanta ta bude sabon shafi Dan ta manta da Cewa ita daya zamu bari(saima ankai mutum kabari zai San kadaici. Allah dai yasa muyi dariya a kaburburanmu.).

Hmm ai batamasan gidan wa aka kawota Ba saboda kanta na cikin gyale har muka kaita daki kuma ai batasan yazeed Nada mata Ba kuma bata tbna Shiga side din zakiyya Ba Dan haka bata gano ba.
Lokacin ko da akayi musu maraba kuka take ga hayaniya Dan haka bata gane muryan mom ba.

Aunty nafeesa da mom ne suka shigo,mom tayi Sauri taje wajen minal yayinda ta dago chin dinta tana mai Cewa " 'yata me ya sameki?"
Kuka minal ta kara fashewa dashi ta rungume mom Dan ta dauka mom tayi attending bikin ne

Tace "mom Ashe an gayyaceki?mom Dan Allah karki tafi ki barni kamar yadda su zaliha da untichlobanty da ma'ani da nasreen da hidaya da..."

Ya isa bazan tafi in barki ba mom ta fada hakan tana me daurewan kai ?kode batasan wa ta aura ba?kai maybe de tsoro takeji saboda first encounter dinta da yazeed wasn't good.

Shafa bayanta mom tayi tana bata soothing words har tayi shiru tana shessheka (sobs).

Kinyi sallahn Isha'i ? mom ta tambayeta tace a ah. Mom tace to tashi kije Kiyi kinji
Shiga toilet din tayi taga irin na wannan dakin da aka kaita ne sansadowa tayi kamar barauniya Wai Dan kar fanfo din yaji motsinta ya bachi da gangan har zatakai hannu ta bude saide ta fasa

Fanfon dake jikin toilet irin na tsarkinnan tace ta matsa tayi alwalanta Dan akwai irinsa a gidan aunty fauxy so ta iya aiki dashi har wani smiling take irin itama ta Waye dinnan.

After tayi alwalan bata mayar da dankwalinta ba ta fito Dan ta manta da cewa ma su mom sunanan

Smiling suka mata ta miyar musu kafin mom tayi introducing mata aunty nafeesa sannan ta tada sallah

Aunty nafeesa Kam yaba Kyan minal take tunba gashinba shi yafi dauke mata ido.

After ta idar mom ta zaunar da ita ta mata wa'azi ya tsumata sosai.

Abinda ta fada last ne yasa minal shock.

"Daughter Dan Allah ki rikemin Dana dakyau kuma iyayi miki wani Abu ki sanar dani"

"Kina nufin oga sir?"minal ta tambaya hankali tashe.

"Kwarai shi"mom ta bata amsa. Atake minal ta.........

Finally,Nayi post kuma sai Kiyi supporting dina by voting and commenting.

love you all😘

Karamarsu babbarsu ce

Miss untichlobanty💕

21st September,2019.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top