CHAPTER 23
.....inaso inje ziyaran family na ne maybe nanda wata 4 kuma zanyi wata 1
Yazeed yace Allah ya kaimu nima next week zan tafi wani mission kuma zanyi Kamar 2-above month kamin na dawo
Mom tace toh Allah ya kaimu. Yazeed yace tare zaki tafi da Jamal kenan? mom tace eh,yace that's good daganan kowa ya kama harkansa
🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹
Akwana atashi yaune yazeed zai tafi mission dinshi zakiyya tace baby inajin zan Komai aiki tunda kaga tafiya zakayi
Yazeed perfume ya fesa kamin ya tako Inda take ya zauna ya rike hannunta yace Ba Komai u can resume sannan ya danyi pecking lips dinta
Hararansa tayi tace kaga matsalarka kenan kai da an zauna ana magana sai ka fara canjawa jiya abu daya akayita yi amma baka gaji ba ni matsa Dan Allah ta fadi hakan tana dan turesa
Yace haba mine na bankwana fa zamuyi 2 months fa zanyi babu ke
Tace ni rabu dani bacci nakeji
Haka yazeed ya gama nacinsa amma zakiyya ta rufe idonta tace Sam
Dole ya hakura ya tafi tace Allah ya tura keya
Sannan ta kara lafewa acikin bargo ko wankan tsarki batayi ba sai bacci after 5 min ta zaburo a guje ta bude wani drawer ta dauko tabulet ta watsa kamin ta koma ta kwanta
🍀yazeed kuwa direct dakin mom ya tafi ya sameta har lokacin tana kan sallayanta tana azkar Dan lokacin to 7 ne
Assalamu alaiki ya Ummi
Wa'alaika Assalam son,kaif asbahata ?
Asbahatu bikhairin,just came to to say bye to u
Take care of ur self u know that I will miss u ryt?
Yes mom I do
Matsowa kusa da ita yayi yayi hugging dinta tare da peck a goshi miyar masa tayi ya dago sai taga idonshi ya ciko da kwalla tace son when did u became a cry cry baby ne?
Murmushi yayi yace kawai zanyi missing dinki ne
Kumatunshi taja tace karka damu kaji ?just concentrate on ur mission
Okay kawai yace mata sannan ya fita
Jamal ne ya rakashi har airport akayi clearing dinsa jirginsu ya tashi by 8am on the dot.
🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹
Akwana atashi yau yazeed zai dawo kuma saura 3 days adaura aurenshi da minal
Mom ta hadowa minal lefe na gani na fada tayi order from different countries; atamfofi,laces,material,jewellery,takalma,perfumes kayan kwalliya,inner wears etc
Abangaren su minal Komai ya kankama domin mom tace musu karsuyi kayan daki dakyar suka yarda amma dukda haka sukace zasuyi mata gara da show glass mom tace Ba matsala.
Minal ko gyara takesha sosai ta kara kyau sosai mom ma ta loda musu kudi tace idan Suna bukatan karu suyi magana
Dakyar tukun suka karba tare da yarjeniyan mom bazata kara kashe musu kudi Ba daga wannan.
🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀
Motoci ne Jere suka danno kai cikin jidmar mansion kamin suka tsaya yazeed ne ya fito ya kara kyau sosai yayi fari jikinnan sumulsumul
Ciki ya Shiga yayinda aka Parker motocin mom ne tayi masa sannu da zuwa tare da yaushe rabo kamin tace yaje yayi wanka sannan yaci abinci
Around 9 O'Clock Suna zaune a parlour mom tace yazeed yace yes mom ?
Tace akwai abinda nakesan fadama da fatan bazàka watsamin kasa a ido Ba
Yace mom kawai ki fadi magarnarki
Tace jibi za'a kawo Amarya gidannan
Amarya kuma?Jamal ne zaiyi aure?
Ah ah
To amaryan Waye?
Naka ne
Nawa?!mom kin manta I already married?
Nope,kasan Cewa zakiyya zabinka ne,kuma duk abinda kakeso nima inaso to shiyasa na yarda ka aureta Toh yanxu sai ka auri Wanda nakeso ko?
Amma mom kinsan banida burin kara aure?
Bata rai mom tayi tamike zata tafi yazeed yayi saurin rikota yace indai haka kikeso to na yarda
Murmushi mom tayi Allah ya maka albarka son
Ameen,amma mom wacece ita?
sunanta Amina Idan tazo zaka ganta
Karki damu sweetheart koma wacece ni zan aureta ai farin cikinki shine nawa kuma Ind.......
ME NAKEJI KAMAR MAGANAN AURE ACIKIN GIDANNAN?!
Kwass....kwass zakiyya ta shigo tana wani yatsine tana daga kofar hanci idonnan Kamar zai fado tsabar jaraba.
Zuwa tayi gaban yazeed tace to Baka isa Ba,Wlh yazeed baka isa ba kayi kadan kawai saboda ka kaskantar dani shine zaka wani ce zaka yi aure?ta fadi hakan Kamar zata makuro yazeed din
Mom kam batace kala ba kallonsu kawai take tana ganin ikon Allah na yadda zakiyya ke Abu Kamar Mara lafiya sannan kuma me yazeed zaiyi.
Yazeed bai nuna alamun ransa ya baci ba illa gyara tsayuwa da yayi hankali kwance yace kika ce ban isaba Toh ke a suwa? Ko ince why bazanyi aure ba😕?
Babu abinda zakiyya ta tsana Kamar tayi banbami taga be batawa mutum raiba
Sai tace tabdi jam eehh lallai why ma zaka ce?....to because I said so kanaji na ko yazeed? au Wai dama dagaske auren zakayi ? Wallahi za'a yi tashin hankali.
Kallonta yayi with an expression of I thought u don't care about me,all u care about is your boutique,boutique, boutique.
With a less concern yace eh aure zanyi jibi ma kuwa thank goodness kinzo a dai dai so no need to stress my self.
Tsalle ta daka tace wallahi ni zakkiya nafi karfin ayimin kishiya god forbid ai ba haka mukayi zaka kara aure ba....na haramta maka yin aure a gidannan yazeed da fatan kana jina?ta fadi haka tana zazzare ido tare da huhhura hanci Kamar maiya
Mom ne tayi carab tace
Hey...hey...hey kikace kin haramta masa?and who the hell do u think u are ?ke asuwa kunun bayan ludayi....just a zero behind a decimal point....ran mom yayi mugun baci
Iyee, its all my fault da bansani Anyi wajen dake Ba kamin a Shiga da ita, shiyasa kika sani bakin magana. Listen to me very attentively! Idan kika sake kikayi mana tashin hankali a gida ki tabbata zaman ki ya Kare. Banason in zama sanadin daba aure amma abin naki ya isa. Kin fara wuce gona da iri.
Yazeed ne ya riko mom yace calm down sweetheart bade aure bane Anyi angama karki damu kinsan I love u ko?muje dakikinki. Haka ya tisa mom a gaba har dakin ta. Tanaji Kamar ta yarfawa zakiyya tafi amma batason ta zubda girmanta.
Zaunar da ita yayi ya bata ruwa sannan yayi assuring dinta Cewa ba mai hanasa aure sai Allah daganan ya fita...
Zakiyya kuwa tasan ta tabo Dan yadda taga ran mom ya baci babu abinda zaihana tasa a saketa she must calm herself down. Taso tayi musu hauka amma bazata iyaba saboda tanason igiyan aurenta
Haka taje dakinta aguje tahau watsarda abubuwa tana fasawa hannunta na jini kamin ta fada kan gado ta fashe da wani matsanancin kuka.....
Yazeed ne ya turo kofan dakin ya shigo
Tasowa tayi attachment dinnan duk ya wargaje tana sending masa murderous glare ahankali yazo ya zauna akusa da ita being conscious with the glasses kar ya taka.
Hannunta ya riko ta warce ya kara rikowa zata warta ya rike gam yace haba my zakky uhm....yanxu shine kikaje kikayi fada da mum kinsan mahaifiyata ne tanada hakki akaina ya kikeson Nayi kinaso na haukace ne?
Rungumeta yayi kamin yaci gaba da fadin na dawo ko kiss ban damu sai kihau yima mahaifiyata fitsara kin kyauta kenan?a hankali ta girgiza kanta yace ai kinsan ko Nayi auren ke nakeso waccan zabin mom ne ko?ta gyada kai yace promise me zaki bawa mom hakuri tace on one condition idan kayi auren bazaka hada gado da matar ba yace ai wannan ko baki fadaba kinsan haka yake Insha Allah.
Tace to nima zan bada hakurin yace good daganan aka Shirya kuma akayi wani duniyar.
Jamal kam sune kirjin biki bai samu haduwa da yazeed ba sai Washe gari Inda za'akai lefe
Your one and only karamarsu babbarsu
Miss untichlobanty💕
8 SEPTEMBER, 2019.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top