CHAPTER 22
Sunansa YAZEED Dan gidan w.......
Bai karashe maganarsa Ba sakamakon ihun da minal tayi
Alhamdulillah! Baba da gaske ka saman miji ?ai Ba sai Nayi tunani Ba indai gidan akwai abinci shikenan anwuce gurin
Murmushi kawai baba Dan ya fahimci kuruciya na dawainiya da minal fatansa de Allah yasa mijin Ba Yaro bane inba haka Ba to Akwai matsala
Ya Abubakar ne yace iye iye 'yar kazamar kanwata zatayi aure an girma. Turo baki tayi "ni Ba kazama bace" yace ai na sani nan dai suka ci gaba da sabgogin gabansu
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Salati yazeed yayi lokacin daya bude idonshi
Ganinsa a dakin da Ba nashi Ba yasa ya tuna da abubuwan da suka wakana awanni kadan da suka wuce Wai yau shine matarsa kwance jikinshi batare da tashin hankali Ba balle ace ta tafi office.
Smiling yayi sannan yayi pecking dinta ya tashi ya fada toilet ya sakeyin wanka sannan yayi alwala ya fita domin yin sallh
Koda zakiyya ta tashi wanka tayi taci abinci sannan ta dauko laptop dasu tablet dinta ta fara Duba business
Yazeed ne ya shigo yace babyyyyyy!har kintashi?
Smiling kawai tayi sannan tace afternoon yace afternoon daga nan ya zauna yana shan green tea dinshi while tana aikinta
After ya gama sha yahau gefenta ya zauna suna Dan taba hiransu
___________________________________
/\/\om tana zaune a dakin ta wayanta ya fara ringing unknown number ne hakan yasa bata dauka Ba sanda aka kara kira sannan ta daga
Salamu alaikum
Wa alaik assalam mom ta fada zaka rantse bata iya hausaba
Mama ina wuni?Abubakar ne yayan Amina
Allah sarki Abubakar ykuke
Lafiya kalau,em........dama akan wannan magananne Toh ta amince
Alhamdulillah, to ai shikenan next week Insha Allah uncles dinshi zasuzo
To shikenan zan Fadawa baba,ina gaida brother Inlaw
Kacewa su baban Muna godiya kuma yazeed dinma zaiji
Bakomai mune da godiya
Da haka sukayi sallama mom na mamakin yadda akayi minal ta yadda Allah dai yasa Ba'a boye mata wani Abu Ba,emm Allah dai ya kyauta
Minal kam fita tayi zata koma gidansu zaliha bakinnan har kunne
Ahanya ta hadu da su haruna(Yan shaye shayen nan from chapter 2) dauke da wani ghana must go cikeda atamfofi
Ah ah hajiya minal dama kina duniyar nan ?
Eh inanan sai akayi yaya ?
Allah baki hakuri mu Ba masifa muke so Ba
Ghana must go din suka dauka sai nishi suke zasu cigaba da tafiya.
Minal tace amma kude Anyi ragwaye wallahi anji kunya yanzu duk girman kunnan bazaku iya daga Ghana must go 1 Ba ? Sai Anyi magana kuhau cika baki Wai June karfafan anguwa.
Suka ce wa? aimu bazamu hada kanmu dake Ba ina babu ma hadi, saboda cin fiskane agaremu ace an kwatantamu da mace.
Minal tace wannan kanku akeji sannan taci gaba da tafiyarta Dan taga alamun zasu bata mata rai
Murtala ne yace ma ta "inkincika ke yar malam yusufa baban kowa ne ki daga wannan jakar ance miki kayan wasa ne aciki
😏?
Basu ankare Ba kawai sukaga Ghana must go a sama ta daura aka.
Haruna yace na Shiga uku ni dan mutum 2 jikan mutum 4,murtala munji kunya ta d'aga!
Ajiyewa tayi ta juya zata tafi murtala yace
"Nide ina baki shawara inkinyi aure a gaba karki nunawa mijinki kinada karfinnan Dan wallahi sakoki zaiyi Dan mu maza akwaimu da son mace me nuna rauni ko zata iya Abu ta nuna bazata iya Ba,macen da take nuna Cewa mu muka cika mata kuma muka gyara rayuwarta
kai haruna kama muje"
Jakarsu suka dauka simi simi suka tari Napep dama mamar murtalan ce ta aikesu
Minal ko tahiyatta tayi tana Cewa har Dan shaye shaye zai iya bada shawarar arzikine?yo jakar mafa Ba wani Nauyi gareta ba kawai de tsabar shaye shayensu har garkuwar jikinsu ta zamo batada karfi. Aikin banza!
Gidansu zaliha ta fada ta labarta mata abinda ta riska bayan ta koma gida nanko ta dinga tsokanarta sunata raha abinsu.
BAYAN SATI DAYA
Mom tayi magana da uncles din yazeed Kamar yadda tayi alkawari kuma sun sanarda ita zasuzo
Shirye Shirye ake agidansu minal makota da abokan arziki hardasu aunty fauxy da iya maman zaliha sun shishshigo ana ta aikace aikace domin taran baki
Minal kam Cewa akayi su Shirya itada zally su tafi gidansu zally
Suna cikin daki zaliha ke Cewa ke kawalliya na kasa yarda wai zakiyi aure
Minal ta daga hannu ta zuba mata duka acinya tare da Cewa da fatan kin fahimci Ba mafarki kike.....
Maganarce ta Koma sanda zaliha ta yarfa mata tafi abaya tare da fadin saura daya.
Bankarewa minal tayi saboda dukan ya shigeta kuma bazata akamata
Nan fa suka fara duke duke zaliha ce tayi surrender tace
Ke shegiya ni matsa hanunki saikace wuka
Minal tace zama Kiyi bayani
Suna cikin haka sukaji hayaniya ya karu
Lekowa sukayi sai suka ga luba Maman bilkisu tsaye tana fadin:Kamar da gaske ai dama wannan yar taku kazama ,ballagaza babu Wanda zai kalli ko Inda take balle ya shinshinata,yanxu haka Nasan sadakanta za'a bayar,wallahi kowaye ya karba ancucesa
Aunty fauziyya ne tace ke dakata inhar kinsan......
Minal ne tayi carab yayinda suke fitowa adaki rike da hijab dinsu tana mai Cewa "ko Ba Komai ai nafi su o'o tunda dai ankarbi sadakan nawa kuma zani da mutunci na wasu da ko a sadakan bazasu sadaku Ba fah?sai yawo a gari an zama shaddar kasuwa kowa zai iya tsuguna duwaunsa akai "
Daganan ta fizgo hannun zaliha sukayi waje yayin da ta balla mata harara
Sauran matanne da basufi goma Ba sukayi mata chaaa aka kowa da irin nasa comments din daganan akayi waje da ita
Bayan minti talatin saiga Yaro yayi sallama Wai inji baban kowa
Akawo abincin baki parlourn zaurensu.
Nan inna tace ya nemo yara biyu sai sukai. Haka ko akayi bayan sun gama cin abinci tare da santi suka sha zobo da kunun aya sannan aka tsaida aure nan da wata 3
Uncles din yazeed sunji dadi sosai da irin karamcin da akayi musu hakan yasa sukasan yazeed yayi dace domin lokacin da sukaje gidan su zakiyya ruwa da lemo kawai aka basu ko snacks basu samuba balle abinci gaisuwan ma sama sama .
Mom suka kira suka fada mata abinda yadda akayi aiko taji dadi daganan aka dinga Sanya alkhairi ana watsewa.
Minal sai 5pm ta dawo aka fada mata yadda akayi bakinta har kunne ya abubakar nata tsokananta.
AT NIGHT
mom,Jamal,yazeed and zakiyya zaune a parlour zakiyya na latsa waya while YAZEED and Jamal are watching football, mom kuma na rubuce rubuce
Mom tace yazeed,kowa juyowa yayi ya kalleta tace akwai aabinda nakeson in fada maka......
Dan! Dan!! Dan!!
Cabdi anxo gurin. Me mom zata Fadawa YAZEED kuma yaya zaiyi ko ince zasuyi reacting?follow me to find out....
Don't forget to like,share and comment
Ur one and only karamarsu babbarsu
Miss untichlobanty💕
8 SEPTEMBER, 2019
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top