CHAPTER 21
DAN ALLAH KARKU MANTA DA FOLLOWING DINA SECOND BIYAR KACAL ZAI DAUKA.
Shiru parlourn yayi yayinda kowa ke nazari aransa,mom tana fata Allah yasa su yarda
Yayinda baba ke nazarin me Yan anguwa zasuce ai Dan abin duniya ya aurarta, Yayinda inna ke Mazarin anya minal zata iya zaman gidan miji kuwa?
Yayinda ya abubakar ke farinciki finally dirty sister dinshi ta samu miji nagarcacce Duba da mutuncin mahaifiyarsa kuma dai ruwa da kankara Abu daya ne samfuri ne kawai ya banbanta
Baba ne ya dago ya kalli mom kamin yace agaskiya hajiya.........
Minal koda ta fito hanyan gidansu zaliha tayi malam bala ne yayi saurin kunna mota tare dayi mata horn sannan ya zuge glass yace hajiya kihau nakaiki Inda zaki mana
Allah ya gani malam bala naaon yarinyan saboda babu ruwanta gashi batada girman kai irin na madam zakiyya
washe baki tayi kamin tace malam bala da ka barhi kawai
yace a ah dai kizo muje
shiru tayi tana Neman hujjan da zata bayar da taji medulla oblongata dinta bai harbo mata Ba kawai sai tahau baya
Owners kwana ta Shiga sai tayi wani das da ita kamar hajiyar gaske
Kwatanta mai ta fara yi.........
Zaliha's POV
Hm
Swthrt Wai me ya samekine duk kin canja min gashi na kosa na ganki amatsayin matata
Dagaske?
Eh dagaske nake, kina gida ne?
Eh ina gida Kasan tunda aminiyata ta bata jiya....hhhh....na dawo..daga....gid......
Sai kawai ta fashe da kuka
swthrt me kike Cewa kina nufin Amina jagwal ta bata?
Tace eh,yace
Kiyi hakuri ganinan zuwa kinji ki yi shiru kinsan kukanki yana tada min hankali.
Toh kawai tace kamin suka datse kiran taci gaba da kukanta
After 10 minutes
Karan mota zaliha taji a kofar gidansu ana horn
Mamaki take Dan Ba haka karan motan Suleiman yake Ba
To kodai yasai wani mota ne?
Hakadai ta dinga sake sake yayinda take saka hijabi da takalmi Dan yau Ba kwalliya aminiya ta bata
Kofar dakin iya taleka tace mata Suleiman yazo
Iya tace to tamai iso mana tace Toh sannan ta fita
MINAL kuwa tun ahanya take sake sake yanda zatayi surprising zally Suna isowa tace baba kayi mata horn Dan Allah
Yace toh yata sannan yayi horn Kamar bayan minti biyu saiga zaliha ta fito
Tsayawa tayi sakoko tana kallon motar kawai sai ta basar tahau waige waige tana Neman motan future hubby dinta da taga dai babu alamarsa kawai sai ta juya zata koma ciki tana mai yana kyau irin na motar
Daidai lokacin minal tace wa bala ya sauke mata window ta control din wajensa akwai Abu a hannunta
agaskiya dai babu Komai a hannuta tana tsoran kar yaje ta taba abinda Ba daidai bane ta lalatawa mutane mota wannen azzalumin oga sir din ya kasheta Dan bayida imani
(Kaji fa minal Wai bayida imani hmm Allah dai ya kyauta)
Yana saukewa kuwa tace "Yan mata ki mana" tana dariyan shekiyanci
Zaliha dai inba kuskure take Ba to lallai muryan minal taji may be depression na batan minal din yasan ta fara imagining things
Juyowa tayi aiki karaf suka hada ido murza idonta tayi yayinda bakinta ya budu mamaki da tambayoyi fal ranta
Da sauri ta karaso tana mai saka hannu domin taba fiskan minal Dan ta tabbatar da kokontonta
Aiko minal dince Ba gizo gizo Ba
Cikin dashasshiyar murya tace minal
Smiling minal tayi tana gyada kai
Zaliha tace Kece ?minal tace nice
Bude kofan motan tayi ta sauko kamin suka daka tsalle atare suka rungume juna suna ihu tare da juyi
Smiling kawai baba bala keyi
Nanfa minal ta juya tacewa baba bala zai iya tafiya
Yace hajiya kin tabbata Ba matsala? murmushi ta masa alaman eh kamin sukayi jikin gida aguje sai dakin iya bakinnan nasu har kunne
Aiko iya taji dadin ganinta sosai bayan ta mata jaje ne suka fito suka koma dakin zaliha
Zaliha tace kawas wayar dani, Wai yankan kai kika fara ne?ko sata?ko kidnapping?
Minal ta kyalkyale da dariya tace Kamar kinsan yanxu haka kanki nazo cira kuwa
Ai bashiri zaliha ta rufe kanta
Wannan karan minal dariya take harda buga cinya tace ke dallah wasa nikeyi matsoraciya
Zaliha tace anji ai tsoran ma da dalili nakeyi nidai yi mini bayanin yadda akayi kika samu mota irin wannan kuma harda driver
Minal tace "jiya........
Nan ta labarta mata abinda ya faru Kamar yadda mom ta tsara har izuwa yanzu zaliha ko sai gyada kai take Kamar kadangaruwa alamar gamsuwa
Minal ko taki fada mata Gaskiya ne saboda tasanta da karadi yanxu sai tayi subul da baka ta fada Ba tare da tasani Ba
Aiko hira suka kafa minal na bata labarin yadda gidan su yazeed din yake wani abin ma Zaliha sai tace "kai minal arage na tomorrow"
minal tayita rantsewa amma zaliha bata yadda ba
Wayan zalihanne yayi ringing ta Duba Suleiman ne dauka tayi yace mata ya iso tace to gatanan zuwa kamin suka fito ita da minal
Jingine yake ajikin motarsa kin 406 Yace lallai ma swthrt dama kawai so kike kiga fiskana shine kika wani cemin minal ta bata minal tace eh hakane na bata amma yanxu na dawo
nan zaliha ta labarta masa abinda ya faru yace Allah dai ya kiyaye na gaba tace Ameen
Hira suka ci gaba dayi abinsu sai wajen azahar tukunna minal tace zata tafi Suleiman yace bari ya rage mata hanya
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
.........agaskiya hajiya Duba da irin mutunci da karamci da kika nuna mana dukda Cewa kin fimu arziki zamuso kuma zamuyi farin ciki ace Mun hada jini dake saide wani hanzari Ba gudu ita yarinyan bamusan ra'ayinta Ba
Dan! Dan!! Dan!!!
Gaban mom ne ya fara lugude lallai dakyar minal zata yarda da wannan batu Duba da irin abinda yazeed din ya mata saide ikon Allah
Tace to shikenan ga card dina duk shawaran da kukayi sai kusanar dani ko?sukace Insha Allah
Sannan ya Abubakar ya amsa card din
Yayi waje shida baba yayinda inna ta bisu da Karin kumallo sannan ta dawo ta sami mom bata fara Ciba
Tace hajiya kick mana mom tace aike make jira muci tare sannan ki dena ce min hajiya kicemin yar uwa
Toh kawai inna tace sannan ta zauna suka fara ci tana mai kara jin mom har cikin ranta
Wajajen azahar saiga minal ta Shigo alokacin mom ta Dade da tafiya
Baba da ya Abubakar ta gani zaune suna dan hiransu yayin da inna ke dafa abinci
Tsalle minal ta daka taje ta fada jikin sa
Baba yace yi ahankali kada ki karya Mani d'a
/\/\inal tace ai Nayi kewansa ne nan ta jona aka ci gaba da labari da ita can inna ta leko tace a ah har kin dawo kenan? Tace eh
Inna tace ya kika tadda kawar taki minal tace lahiyatta lau kawai de tayi kuka ne baba yace Allah sarki
Inna ce tayi ma baba Alama da ido Cewa ya fada mata
Gyara zama yayi yace AMINATU
Tace na'am baba yace ki saurareni da kyau sannan Kiyi tunani
Tace Toh
Yace nasama maki miji sunansa YAZEED........
Tofa fans kuna ganin minal zata amince da wannan batu?
Ya ake cikine tsakanin yazeed da
Zakiyya
Ina jiran comments dinku kada ku manta da offer na.
NAGODE
takuce @mzz_untichlobanty
24 August, 2019
Miss untichlobanty💕
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top