CHAPTER 19
Coffee dinshi ya hada hankali kwance dinshi yama manta da zancen wata minal
Stairs ya haura sai ya hango Kamar giftawan zakiyya tana shiga section dinta
Hankali kwance ya karasa dakin nata koda ya Shiga baisameta Ba amma yaji karan ruwa hakan yasa ya zauna bakin gado ya fara shan coffee dinshi
sip 2 yayi kamin ya laluma aljihunsa yaji babu wayarsa dayan ya duba still babu sai ya tuna Ashe yana dakinshi kuma yanaso ya Duba wasu important abubuwa hakan yasa ya ajiye coffee din sannan ya fita izuwa dakinshi
Tafiyarsa yake hankali kwance had ya isa izuwa dakinshi
Neman wanyan nasa ya farayi amma bai gani Ba
arching giransa yayi yana nazarin to ina yasa wayannasa?dube ya fara can wani mind yacemai why not ya Duba changing room dinsa tashi yayi ya Duba aikuwa ya hango wayarsa ajiye gaban mirror dauka yayi sai taga message daga mom
Budewa yayi Kamar haka:
"Good Morning habibi!
سأخرج،لا تقلق أرجع قريبا جدا إن شاء الله
(I will go out,don't worry I will be back soon Insha Allah)
Take care
Reply yayi mata
"Good morning to u too mom,is okay take care of your self see u later
Love yah😘"
Sa wayan yayi a aljihunsa kamin ya koma part din zakiyya
ZAKIYYA'S POV
A gajiye na Shiga dakina hakan yasa direct jakana kawai na ajiye na fada toilet kayana na fara cirewa sainaji an turo kofan dakina
Shower na kunna abina
I can't remember sanda masu aiki suka fara zuwa dakina Ba tare da na kirasu Ba jin wani sannannen turare da kuma alamun an zauna a gado na ya bani tabbacin Cewa Ba mai aiki bane jarabben baby nane ya lallabo ko me yaje nema ?oho
(Oni 'yasu kajimin zakiyya da tambayar banza Wai ko me yake nema?shaa later on zan tattauna akan mata masu irin wannan hali)
Alamun Kamar ya fita naji hakan yasa nayi Wankana sannan na fito sanye da da bathrobe koda na iso gaban madubi
Hango cup Nayi a ajiye juyawa Nayi name na dauko coffee ne mai zafi
Allah sarki baby na Kamar yasan yau zan bashi good news kuwa
smiling kawai tayi ta dauki coffee din ta dawo bakin gado ta zauna tana sha domin ita ta dauka yazeed din kawomata coffeen yayi
Budo kofan dakinta yazeed yayi ya hangota zaune saman gado ta daura daya akan daya tana shan coffee while scrolling her tablet
Sakoko yayi yana kallonta,shi hallin matarnan nasa yana basa mamaki ita bata hada masa Ba Shiya hadawa kansakuma ta dauka tana sha
Gyaran murya yayi ta dago tana smiling Kamar da gaske sai yaji wani babarakwai namiji da Suna haajara
Shi Rabon da tayi masa smiling had ya manta in fact wani zubin ma sai yayi kwana uku bai sata a idonsa Ba grimacing(yake) kawai yayi ya kamin ya gama shigowa dakin
Ajiye cup din tayi tazo ta rungumeshi tare da yi masa peck
Shide kallon ikon Allah yake
Janyo hannunshi tayi suka zauna akan gadon yatinda take kan cinyanshi
"Thanks for the coffee baby"
Smiling kawai yazeed yakeyi yana Dan Sosa keya sai mamaki daya cika shi Dan Rabon da tayi masa irin haka tun 4 months after bikinsu
(Gaskiya fa koni ina mamanki balle kai Wai ! ehm muje zuwa)
"Baby surprise!!!"
Dan hade giransa yayi yace and what is the surprise?
Smiling tayi sannan ta kwantar da kanta a kirjinsa kamin tace for the next 3 month Bazan dinga zuwa office Ba I will be at home zandinga monitoring din
Work ta gida
Yazeed yace my zakky zakky bakida dama yau kuma Yan tsokananne suka motsa ?
Dagowa tayi tace am serious kasan I don't have time for jokes
Kallon idonta yayi tabbas shide baiga alamun karya Ba
Yace like seriously my zakky zaki zauna dani a gida for 3 months? tace "yap"
Tace ko bakajin dadi ne yace no no no that's not the issue Ba haka bane kawai de am shocked ne bama surprise Ba
Tace you shouldn't be kaji ko?ka kwanta bari in saka kaya inzo
Toh kawai yace da ita kamin ya kwanta yanata binta da kallo tsohon sonta na Dada hauro masa
Dogon Riga ta zaka irin cotton dinnan na zaman gida
Sannan ta dawo gaban mirror ta saka roll on kawai Dan bataso ta dagawa yazeed tsohuwar liki gefensa tazo ta kwanta ta juya masa baya
Matsowa yayi ya rungumeta tare da Cewa zakky kinsan banason ana juyamin baya koh ?
Muryarsa Kasai ya isa ya fahimtar dakai yana cikin wani yanayi
Juyowa tayi tana facing dinsa kamin tace baby am sorry we can't......
Bata karasa Ba ya fara kissing dinta sanda yayi kusan 3 min sannan ya tsaya shan iska
Zai Koma tace baby am off
Wani ras yaji Wai shikam me yasa rayuwa ke masa haka da yaga ci sai yaga rashi ?
Amma dai dukda haka bazai bar dama ta wuce masa Ba Dan haka romancing dinta yayi sosai sanda ya rage zafi tukunna ya tashi yayi wanka tazo ya kwanta a gefenta a lokacin harta bingire da bacci
🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹
Around 7:30am su mom suka isa unguwan su minal.
Minal kam sai washe Baki take yawa gonar auduga zataga innanta da baba
Kallonta kawai mom takeyi tace daughter dadi ma kikeji zaki rabu dani ko?
Girgiza kai minal tayi tace kawai Nayi kewarsu ne shi yasa
Mom tace Allah sarki anguwanku akwai amajir dayawa gasu abin tausayi duk a ramko kayan sawa basuda shi kiga wancan Dan karamin ko takalmi baiyida shi danma saiya ya cancanta a taimaka musu they need some help
Minal tace mom Ba amajir bane fa almajiri ake Cewa sai kuma tayi Dan tunawa da turanci da mom tayi a karshe help kawai ta sani sai kawai ta basar
Tace baba bala kwanar dama zaka Shiga
Kamin ta juyo ta kallo mom tace ai almajiran unguwarmu ai sunada Khan gani akan wasu.
Wasufa ko wanka basuyi basuda wajen kwana amma wadannan Ba laifi wasu fa inkika gansu Kamar masu cutan ehmm......kwa..?!kwash....
Mom tace kwashoko
Minal ta gyada kai kamin tace kwarai shi cutan tamowa Ba
Sai tace ganan gidan mun iso
Tsayawa sukayi suka sauko daga motan almajirai da masu tuyar kosai da samarin anguwa Yan zaman kashe wando Suna bawa idonsu abinci
Acikin Land cruiser fara kal suka zo
ko minal ma tasha mamaki lokacin da akace Anan zasu tafi dan San da akayi cakwakiya da ita tukun tahau domin tala Cewa akayi in bata hau Ba za'akira oga sir
Saukowa minal tayi zata antaya da gudu mom tace daughter tafiya zakiyi ki barni ?
minal tace Ahe tare tare zamu higa
(tofa minal wannan phonetics din Yan kauye ko daga ina?)
Shiga sukayi yayi da akabar malam bala awaje domin jira
ASSALAMU ALAIKUM INNATA !INNA!!INNAROS!
Hazbiyallahu la'ilaha illahuwa alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azeem wa nakeji Kamar aminatu na
Inna ke fadin haka cikin murya mai alamun zatayi kukan dadi
Fitowa tayi yayinda baba yake biye da ita rike da hotan minal a hannunsa domin kaiwa gidajen talabijin
Let me take a nap,hmm da fatan kunyi enjoying long chapter nan mude je zuwa
Ina team zakiyya ne ?are you happy da suka dinke da yazeed?
Team minal kada kusami damuwa everything happens for the best a gaba zaku gane dalilin dinkewar
Team yazeed how far mutumin naku fa zai danyi chilling inji Yan birni😀
Masoya Ina jiran comments dinku
Your comment determine the longness and sweetness of next chapter
Love you all takuce
Miss untichlobanty💕
23th August, 2019
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top