CHAPTER 14

Tsugunawa yayi a gabanta yace kawo hannuki !
Kallonsa take a ranta tana Cewa dama oga sir Dan iska ne?

Dama yawanci sojojin nan mazinata ne ga shan giya da sigari
Dan iska me zibin samudawa

Tafadi hakan a zuciyarta domin it a atunaninta wani abin zaiyi da hannunta domin tun batakai haka Ba inna ke ce mata duk namijin da ya tabata bada sannin innar Ba to Dan iska ne amma banda baba da ya abubakar

Tsawa ya daka mata aiko ta miko hannun nata. Igiyan ya fara shirin kulla mata ai atake ta fara kuka da hawaye

Kallon ta yayi kamin yayi murmushin gefen baki yace:
Ashe de baki cika jarumar Ba
ai nadauka taurin kanki bazai bari kiyi kuka Ba.

Ajiye igiyan yayi a wajan ya fita daga dakin ya jirkita pin din ya rufe.

Kuka ta fashe dashi tana burburwa a kasa har ciwon dake hannunta ya fara jini bata saniba

Wani sautin da cikinta ya bayar shi ya tuna mata da cewar bataci abinci domin sau biyar takecin abinci banda kananun kwamulashe da take yi

Tunawa tayi da wani lokaci

Flash back

Inna Wai haryanzu baki gama miyar bane nifa kinsan bama er mutunci da yunwa

Inna dake kitchen tace Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un
kinga ni ki rabu dani kinfiso Nayi irin wannan miyan naku na 'ya'yan yanxu

Amina ce tafara waka tana buga gwannon hannunta da

Iyya yunwa batada kara,iya yunwa ba'a mata lahaula,iya yunwa batada Sabo wayyo iya yunwa na iya karwa Iya yun..........

Muryan inna ta jiyo wadda ta leko tana kallon ikon Allah

ta Ce to ai bazansan kinajin yunwa Ba sai kin fara bin makwabta

Turo baki tayi tana guna guni ta mimmike kafa a kofar daki tace
inna shiyasa nace kiban na dafa kika ki ki Duba fa yadda dare tayi

Inna tace wai karfe biyar kike so na dinga gama abincin dare ne ?

Kara turo baki Amina tayi tace inna to ai.........

Sallaman da baba ya Watso shi ya sa ta antayo da guru tana Cewa baba sannu da zuwa

Yayinda take turo baki ta huhhura hanci
baba yace :
Uwata ya akayine?

Minal tace inna ce had yanxu bata gama abinci Ba gashi yunwa nakeji gashi had dare yayi

Murmusawa baba yayi yace uwata yanzun ne dare yayi?karfe 6:30 ai beyi Ba

kinga dauko mana taburma

Taburman taje daukowa yayinda inna ke Cewa
mallan an shigo kenan,ya aikin?ai wannan sususun bata ma bari min gaisa Ba

Baba yace Alhmdllh ,uwartawa ce Ba tada dama muryarta suka jiyo ta leko ta taga(window) tana Cewa
Allah ya kawo Mani har kunnena gulmata akeyi ko?

Dariya suka fashe dashi yayinda baba yace ja'irar yarinya kasa kasa

Inna tace malam bara in kawo maka ruwa

Sai a lokacin Amina ta fito ta shimfida tabarmar yayinda baba ke Cewa
ina Kanwar taki deeje ko duk gajiyar makarantan ne?

Tace Ba wata gajiya baba tana can de tana abinda aka saba baccin asara

Baba ya Dan dara yace gaba de baccin asara ai tana kokari kayi kusan wata hudu a makarantar kwana (boarding) baka ganin iyayenka ga wahalar labour ai dole tayi bacci

Labulen da aka banko ne yasa suka dago dukkansu suka kalli kofar

Deejeh ce ta fito tana watsa hamma Amina ta dauje bakin tace ke dallah rufe mana shegen bakin naki me zubin sokawe

Dije tace a ah salga ne Ba sok..............

Ai bata karashe Ba taji bugu.
Babane yace uhm yarannan bara kuga, ya mike ya tafi waje domin yayi alwala yaje masalti ya samu falalar jiran liman domin yasan idan suka fara Toh sai Allah.

Kayi magana Kamar kana zugasu kayi duka su dau gaban duniya su daurawa juna

Inna da ta dawo da ruwanta a hannu ta taradda tabargazan dake faruwa nan ta saita ma kowanne notin kansa

Nan suka ballawa kuna harara wadda yake nuni da mun daura gaba.

Innako takaici ya mata yawa

Amina akwai gajan hakuri,saurin hannu da tsiwa

itako khadijah fitsara ta mata kaka tuku a tsuliya

Bayan baba ya dawo daga masallati nan ya dauko ledan daya shigo dashi dazu yace

Uwata d'azu dazan dawo isubu mai gashi yaban tsirannen yace na kawo miki. Minal tace kace Allah ? Tana mai jin dadi.
Inna ce ta shigo da farantin tuwo malmala biyarne a ciki ta ajiye.

Washe hakwara Amina tayi tace kai inna kin kyauta wallahi Dan Nasan bazan iya kara minti 30 me kyau Ba yunwa zata kar ni

Bude naman baba yayi yanke 5 ne Dan haka ya mikawa minal yanka uku ta karba tana Washe baki sannan tace na gode. Yanka biyun ya mikowa deejeh wacce keta cika tana batsewa,Inna na zabga mata harara.

Juya kai tayi tace bataci tunda na Amina ne girgiza kai baba yayi kamin ya mikawa Amina yanka daya.

Karba tayi ta ajiye akan ukunta alokacin har ta cinye Mara daya ta yanko wani loma kenan baba yace
Haba mana uwata ci ahankali ai Mara biyun duka naki ne wannan lomar aiko katan gardi meji da karfi a jika albarka.

Itadai Amina ko ta Kansu bata bi Ba wani loman ta yanko Wanda yafi na farko zatakai baki idonta ya fada akan iyaye nata

Gani tayi sunata fafatawa da yanka daya Ashe ma me kitse ne.

Hawaye ne suka cika mata idanu kawai sai ta dauki daya dake gabanta takai baki.

Wani kara ta saka duk hankalin su ya dawo kanta

Ajiye musu musu ukun tayi kuma manya ne tace baba gashi kuci banaci hakorina

Inna tace kici dai sai kici ta dayan gefen tace a ah na koshi

Mikewa tayi ta fita ayayinda take leko su

Allah ya gani tanason ci amma bazata iya cinyewa iyayenta suci kitse Ba.

Wanke hannunta tayi taje ta kwanta Dan already tayi sallan issha'i

Can wajajen karfe 10 lokacin gidan yayi shiru alamun sun kwanta.

Sanda tayi ta bude kofa ta shigo falon iyayen nata Inda aka rife guntun abincin aka ajiye a saman fridge tunda Ba nefa danma garin da sanyi

Ahankali ta bude farantin aiko taga sunci sun bar yanka 2.

Dauka tayi ta gutsira wani lumshe ido tayi harda girgiza kai tana murmushi sannan ta dauki cabbage ta harba tare da kuli kuli.

Inna da baba dake labe Suna kallonta domin sunji sanda ta bude kofan suka kalli juna komawa ciki su kayi suka zauna bakin tsohuwar gadonsu hawayene fal idon inna.

Tace ashe babu abinda ya sami hakorin nata kawai dama so take iyayenta suci?
wani kaunar minal ne ya Kara dabaibaye mata zuciya. Baba yace aini Nasan Ba abinda ya sami hakorin domin naga sands ta dago taga abinda mikeci idanunta suka ciko da kwalla Nasan zatayi wani abun
Shi yasa nace miki mubar yanka 2.

Rungumesa innar tayi kamin ya rarrasheta suka kwanta zuciyarsu fal cike da son yar tasu.

Hawayen da ya gangaro kan kumatunta shi yasa ta sauke ajiyan zuciya

Tayi missing iyayenta,itakam Allah ya isanta da wannan oga sir me kama da aljanu

Toooooh Anan zan dasa aya
kwana biyu kunjini shiru wallahi makaranta ne kunsan mu Yan 100 level dole mu zage dantse balle yanxu da muke second semester atayani dai da addu'a Allah yayi mini tsari da carry over

Seriously need your prayers!

Thanks for understanding me

Show some love by:

Sharing
Voting
Commenting

10 July 2019

Mzz untichlobanty💕

Karamarsu babbarsu😘

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top