page2

*KUDI..*
_Kumbar susa_ !

2

Bangaren amarya fatima kuwa bayan sun idda nafila shafin hira mai dadi mai tsafta suka bude tsakanin ta da angon ta alhj aliyu,acikin hirar har yake mata tambayoyi dayawa daya shafi addini wanda aganin shi ya kamata ace kowacce ya mace tana sane da su kafin auren ta

Yau dai Wani nishadi da kwanciyar hnkli ke ratsa shi wanda ya dade baiji irin sa ba,duk dama yasha gwada kawo mata amma Allah bai nashi nasarar samun nazama ba amma fatima ta dabance aransa

She feels so differnt with her،ita ba zabin mahaifiyar sa ko dangin sa bane old time love ce wanda ya sa rai ita zata warkan da zuciyar  sa akan abunda  daya dade yana damu wa da shi akan rayuwar auren sa.

Ko ba ace ba yasan matarsa ramlat tamkar buhun kaya ne akansa kamar yadda ta zame kashin kifi wajen uwar sa da kuma dangin sa.

Sudai Basu taba cewa ramat itace makasudin rashin zaman amaren nasa ba anma abun a fili yake tunda takanyi ikirarin bata taba bari anyi auren sa lpya batare da ta tada mumunnan hargitsi ba sai akan wannan.

Karfe 10cas agogon batman dake jiki  bango ya buga nan alhj aliu ya mike ya shige closet domin rage kayan jikin sa
Inda amarya fatima take xaune kunya yama hanata motsawa mayafin ta kawai ta iya cirewa ta kishingide akan makaken gadon ta tana aduoin da malamai suka bata

A haka cikin so da shakuwa alhj aliyu ya lallabata suka raya daren,cike da tatttali da nuna kwarancewar sa wajen iya nuna soyayya ya tarairaiye ta

Da shagwaban nata duk yabi ya like yana rarrashin ta don ko a cikin cikakkun mata masu niima yau ya dada sanin fatima ta dabance.

Tsaban ta wahala a hannun shi Ko bacci da kyar ta iya komawa,jikin ta yayi matukar kyau cikin nityn data sa dayake kalar ruwan powda ne da kyar ya iya runtsawa ya bar kallon ta

Da asubahi ma shi ya fara farkawa ya shiga gyara mata kwnciya ganin alamun ta jigata sosai a hannun shi ya sa bai tashe ta
Ba Kawai sai ya dora towel a kugun shi ya nufi bathrum abnsa

Murdawa da Rufewar kofar sa yyi dai dai da bude idon ta,tarwal ta bude idon kamar wanda dama ba baccin takeyi ba

Innalillahi wa inna ilaihi rajiun take son furtawa Har Cikin ranta amma sai taji ta kasa yin motsi da lips din ta,ga sautin kiraye kirayen sallah  memakon taji hakan ma sautin Kiran ramlat kawai takeji a kunnen ta ita da ilahirin jinsinf masihirin tan ta.

Ji tayi kirjin ta na bugawa a zauce zuciyan ta na wani irin kakarin tunxira ta ko xata fasa ihu amma hakan baiyu ba cikin zautuwa ta shiga finckewa ita kadai alaman tana  neman taimako

Duk nishi da buge bugen dataso yi bata iyawa Wani irin bankarewa ma kirjin ta yayi kamar wacce aka daure ta,da kyar tayi wuf tayo jefa da dankwalin kanta tana yi tana mai mikewa tsaye kamar zautacciya

Wani irin numfashi mai ban tsoro taja Ba bata lokaci ta fixge jiki ta bude kofa ta bar dakin,daga ita sai nityn ta take tafiya babu dankwali bare aron slipers akafar ta cikin kiftawar ido da bude shi sai gata abakin makaken gate din gidan

Allah ne ya bar makansa sani  yadda ta tsere ma securites ta shige ta kofar dake garkame da makullai wanda ba a ko sa lahadin bude shi ba

Hanya kawai fatima ta saita ta mike baji ba gani har sanda ta bace ma ganin kowa....

Jim kadan da Fitowar alhaj daga bathrum yayi zaman mamakin rashin samun ta akan gadon amma sai bai daga hankali ba sanda had yaga ya shafe awa guda baiji duriyar ta ba

Bayan ya kimtsa kansa tsaf ya shiga neman ta acikin gidan sai dai duk wanda ya tambaya sai yace masa shima bai ganta ba

"Wani irin bugawa kirjn sa ya shigayi Sam Baiji dadin hakan ba,dmin hakn ba komi yake shirin tuna masa ba sai amaryan sa  na karshe wato Khadija da ake zargin itace ta dawo kurciyan da aka samo akan gado sa a ranar daren auren su.

Ya jinjina kai idanuwan su duk sun kawo ruwa

"Whats happenin?
Ko nayi ma Allah wani laifi ne...bakin ci na rawa cikin fargaba yace
Yar sakin ma is no wher to be found? ya subhanallahi ya dada runtse idanuwan sa

"Kafin karfe tara na safiyar ranan kusan hankalin sa dana familyn sa yayi matukar tashi

"Where is fatima?"..

Kusan tambayar kowa kenan

Achn sokoto Wajen iyayen ta da kannen ta kuwa Bakin ciki da tsoro sosai ya mamaye  su...

hjy binta bulama da tun faruwar abun take gidan itama ta daga hankalin kowa ana kan aikin neman amarya

In tayo tagumi sai tace"Li'ilafi khurayshin..aniyar kowa ta bishi

Sosai hjiya binta take habaici tana cewa sarauniya fatima dole xata fito Aniyar kowa dole zai biishi

Ramat kuwa tana dakin ta ko fitowa batayi ba,da sassafen kawarta hjy hamida take sanar mata cewa taje gidan malam takai farin kyallen kuma yatabbatar mata da yuyuwar nasaran aikin su kuma ba mai datsawa wannan karon ma suneda nasara akan fatima

"Zuciyan ta tarr... Wani nishadi ne ya mamaye ta

Sautin Wakar ta na sa'adu bori mai taken hadixa yar malamai ta kunna tana hayagaga tana rausaya kanta na kaduwa kamar tsohowar kadangariya,chan ta kunna hayakin tsadadden tabar marlboro ta bula masa wuta tana busa shi yana fadada hayaki da gayya ta shiga hura hancin ta ita kadai tana yatsinawa ...

Sosai abun ya shige ta hernesy mai zafi ta kwalkwala a wine glass shima ta masa zuka daya sanda taji tayi nak sannan ta shige bathrum ta lume cikin haddaen strw berry rich jacuzzi warm bath ta shiga wanke fatar jikin ta hankalin ta a kwance.

Koda alhaj ya shigo yana neman jn bakin ta akan faruwar abun,ci kan ka batace masa ba sai famar lailaya mayukan qamshi take ajikin ta tana shan qamshi

Hakan ya dada sosa masa rai Shi Baiga dalilin da amaryan sa xata bace,kowa na jaje ita tana abun daya dame ta ba.

Abun sai ya dame sa He is soo tensed  har bai lura cewa batar fatiman ya sa shi yau da kusan kowa ma yau yake masifa,Allah yasani... Har cikin ransa yana kaunar fatima kuma ya sa rai sosai akan itace xata zamto masa that missing rib da zai dai daita duk wani al'amri dayake manne a krjinsa wanda bai taba gaya ma kowa ba

"kwana daya tal agida na ace fatima ta bace,?...yo mema xaice da mai martaba sarki muhammd daya yarda da shi duk dama yaji labarin yadda abubuwan ke kasancewa da shi in xai kara auren?

Tunani dayawa sun dame zuciyar sa

Ayayin da Tsaki kawai ramat taje ja tana shiru tana jin kananun bambamin sa

"Wani bn Ba abunda yake cewa illah  ramla ki taimaka min kifito min da fatima dan girman mahaliccin ki ..

Sai Ta dada share shi,Fafur ta bushe idanun ta dan Ko kulasa bata jin zata iya sa lkcn yi har suka fito falo yana tafe abayan ta

Ana hakan ne saiga Shigowar hjy binta da sauran yan uwansa su xakiyya da maryam site din,ramat tana jin su sai  ta mike tsaye ta hayayyako ta tsaya masa akai tana mai dada daure fuskan ta,tasan duk sun tsane ta matukar tsana so Cike daff bori ta bushe idanun ta fara masa masifa
Tace "Ka wuce ka fita...Ta riko kugun ta tana fada da wani irin guts da gadara uwa itace mahaifiyar shi na asalif

"Wallh Aliyu baka isa kaci min mutunci ba ni nace kayi aure ne d xaka sa ni agaba?

Da kayi auren ina har boyemin ake dan an dade da laka min sharrin cewa nice nake hanaka aure? ..to gashi dai na tsame kaina akan wannan kuma babu abunda ya sauya,aure bai karbe ka ba amma an nace maka da shi kamar shan kunun dan wuta To ni dai a sararamin, nagaji..a yadda na cire kaina tun farko hakan zai cigaba,kaje ayarin ka su tayaka neman missing bride dinka
Ka fita a harkata

Ni Babu ruwana akan maganan bacewar matarka kawai ka fice ni bana son hayaniya .....

. .cike da mamaki alhj aliyu yace ramla mani kike fada ma haka dan na tambaye ki?

,turo dangwalin ta gaba tayi tare da turo baki,cike da nuna rashin da'ar ta tace pls the door is open right behind you..sai ya sake baki galala

Hmm kawai hjy binta tace tana kare musu kallo musamman ma ita cikin dakewa ta nemi waje ta xauna

" Tace,ke karamar yar iska ce ramla,
Wato Duk wannan bayani da akeyi ke baki damu ba ko?ramla ko wani yace kin dauki fatima ne kike wannan borin kunyar?

"Da sauri Tayi rau da idanu irin mani ce xa'a ce ma borin kunya? tsaban hade ran datayi fiskan ta kamar zai fashe cikin dauriya mai nuna ladabin dole datake ma hjy bintan adan sadade Tace"Ba'ace ba hajya amma me ruwana a acikin batar matan sa da xaizo ya sani agaba?Ina ruwana da auren sa..nidai a fitamin ina da abubuwan yi...

Hjy tace"Ke? ta dube tana mai Kada kanta wai shin kin manta Kece uwargidan sa
Ne?Oh to Da shigar ki hidima da rashin sa agun mu duk abu daya ne tunda kina auren sa, agidan nan duk abu mai kyau ko mumunan abu da xai faru in har ya shafe shi kema ya shafe ki...ramla kina ji na?

" juya keya tayi tana yatsinawa kusan minti 3 tana shiru a Dan dolen ta ta kau da kai kasar makoshi ta ce naji hjy.

"Hjya bata kula taba tace To daga yau,kada
ki sake daka ma dana tsawa agaba na,dan ina mai shaida maki watan gurjuwan bakin ki yakusa kamawa

Uffan bata sake cewa ba har suka gaji da surun sukayi waje suka barta

Daga nan Dakin ta ta nufa a gaggauce tana rufe kofar kuwa Dariya mai ban haushi ta fashe da shi

...ta bingire da wakar sa'adu bori  tana gintsewa.

Akaci kwana biu ana haka,yau dadi gobe babu amma ko akwalar rigar ta,gashi ko borin kafin aure da tasaba yi kulluma batayi akan fatima ba bare media sunemi jin bakin ta kamar yadda aka saba,abun dai baiyi ma kowa dadi ba,kuma akasan xuciyoyin mutane duk ansan wacce ke haddasa hakan amma basu da ta cewa tunda basuji ba basu ganii ba

Both families saii aka dukufa da neman taimako,duk da haka Adduar da ake yi da istikaran duk idanun ta nakai

Hjy hamida babban aminiyar ta  ma nacan a tsaye tana kare musu gida.

a rana na sha ukun cikin ikon Allah sai aka tsinci fatima.
.
" kowa na murna ana gode ma Allah
,ana cewa ba shakka Allahu sami'ud dua,da shike fatiman bada kafafun ta take yawancin tafiyar tan ba ba aljanun ke deban ta,so a kwana uku ma kawai har tayi nisan daya raba tsakanin abuja da jos,haka take ta tsaga wajaje babu iya neman dan adam da baayi ba amma ba'a ganta ba,sai ranar kamar a mafarki taga ruwa mai tsafta a gaban ta yana kwalala ga yunwa na yawan damun ta ga wahalan masifan data ke ji acikin sassan jikin ta gata ba a suturce ba

wani zuciyar ke ce mata ta bar wajen kar ta shiga ruwan amma wani bangaren ya turassa ta har ta tsoma kafa a ruwa aikuwa tana saka kafafun ta sai gashi ta bace
Bat,bata fito a ko ina ba sai bakin kofar babban massalacin mahaifin ta sarkin skt

Abun ya bada kowa al'ajabi A Cikin kalilan lokaci
Aka yi da ita cikin gida aka fara bata taimakon gaggawa,
hakama alhj aliyu da danginsa duka suka qarzayo masarautar in no time ana ta addu a ana duba jikin nata ana jajan tawa.

"Bayan kwana uku da dawowar fatima sai ya zamto kuka kawai take iyayi ba tacin komi kuma ba sha bare magana

Akwana na hudun ta shiga ficike ficike tana yage duk wani suturan da aka rufa mata asiri da shi sai ta barka,kamar da wasa kuwa cikin dare tana bacci sai Allah ya karbi ranta.

Sosai akayi bakin ciki da jimami Haka aka ci kwana bakwai mai cike da magagin faruwar al'amarin amma ramla bata zo ba bare ta jajan ta.

Bayan komi ya lafa Dawowar su alhj aliyu daga skt zuwa abuja ne suka samu labarin ramla har ta cika ma rigar ta iska izuwa kasar italy,dan anan kayan  datayi oder zasu sauka....

_Wassssh🙆🏿...ahe anan abun ya tsaya🙈_ _"uhm uhm ina yan mata da uwaye  masu bukatar karanta littafi domin samun karin ilimin sanin  istimna'i wato(masturbation )?nau'oinsa,illarsa na fili dana boye?...labarin kudi kumbar susa ya kafa jigo ne da hikiman Allah,zamantakewar Aure,yarda da qaddara da abunda ya shafi sihiri da son duniya'kks littafi ne mai tsada badon kudin da za'a saka mashi sai dan darasun da zaizo da shi wanda suka fiye faruwa agaske shin ko kina so ayi budirin nan dake?TOH👇🏿.._

_MAZA GARZAYA KI NEMI KUJERAN ZAMAN KI A KKS PAID GRP,domin kuwa labarin Kudi... kumbar susa zai fara zuwa ne a ranar Ashirin da shida ga watan mayu 26/5/2020 AMMA Kofa a bude take ga duk mai bukatar biyan kudin labarin iyanzu".FARASHIN SA #300ne kacal,zaka iya biya direct ta ACCT  0152983148  @surayyah muhammad suleh GTB ko VTU transfer ko mtn digits ta wannan number 08060712446 sai ka tura shaidar biyar ta 08036651119 domin Asanya ka a grop din!..hey masoya  abun alfahari inbada kaina a sare domin ku inje gida ince ya fadi😁kuyi kokri ku shigo adama daku don tsabar kauna da nake muku yasa bazan so ace wannan labari ya wuce masoyi na ko daya ba😆ITS GONNA be WORTH..insha Allah!_

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top