G

*GAREKU MATA MASU NEMAN ILIMIN SANIN ILLOLIN ISTIMNAI DA ABUBUWAR  DA RAYUWAR YA' MACE YA KUMSA WANDA YAFI KARFIN TSAFI KO SIHIRI*
_A CIKIN LITTAFIN_ 👇🏿

*♡KUDI..kumbar susa🌺*

Written by
_SURAYYAHMS_

_AN FARASHI RANAR 26_

_Dandano_

Kasancewa yau rana ce ta farin ciki Daddadan sautin algaita,kakaki,ganga da sauran nau'o in traditonal drums and trumpet su suka cike babban filin.

Da yamma ne da misalin bayan la'asariya,Kusan kowani mahaluki yau ya fito kwansa da kwartan sa duk ana tsaye ana kallon hawan dabar,durbar al'ada ce wanda duk wani jinin sarauta ke cike ta ayayin kasancewar duk wata muhimmin hidima musamman hidiman daya shafi na nadin saraura, aure ko bukukuwan sallah.

Cikin wata kasaitacciyar royal canopy fari kar na hangota ta hakimce cikin burgewa da nitsuwa akan kujera golden colour mai  sheki,jikin ta a kawace yake da white french lace wanda aka sakaya shi da transparent golden alkyabba issashe har yana bin kafarta

bold make up din ta ya dada fallasa matukar kyaun datayi،kawayen ta ne a gefe sanye da shudiyar dogayen riguna kowacce dauke da bridal maids palates an rubuta nicknames din su da kyau gwanin ban sha'awa.

A Dayan canopyn kuma mai girma sarkin sokoto ne da hakimai magada arziki da sauran representative din shugaban kasa,some ministers,senators and many other distinguished visitors.

Daga cinkoson mutanen dake tunkarowa a sannu a hankali suka fara darewa suna bada hanya inda a kallo na farko naga wasu yan maza biyu sun bayyana a gaba sanye da green and white garland sun rike babban black and shiny gold royal signboard suna bin  sautin kidin suna rausayawa suna nunawa

,"Sr,Ahj Aliyu shettima bulama,
Matawallen sokoto Aka rubuta boldy akan board din..
Wanda Tun kafin na hangosa na jinjina ma kwalisar sa

Sai bashi kara akeyi Da alama shine Angon ranar,dan ko jikin shi ma a kawace take da pure white babban riga,ko inansa a tsare yake da launi daban na expensive golden desgner accessories kama daga kan takalmi agogo kai hatta links dn dake jikin hannun jumfar sa abun nazari ne,kwalliyar sa yayi matukar kyau shima an kuma sakaya shi gaba daya ne da golden and black alkyabba
Akan dokin sa daya sha kwalliyar shiny golden dresses yake tahowa quiet slow
And majestic.

Zagage da yan banga sune a gefe da gefen hannun dama da hagun sa,makada,yan koroso da  masu busa algaita da kakaki sune agaba kowannen su sanye yake da irin tasa colourful garlands din.

"Allah yaja zamanin ka matawallen sokoto,dan gaban sultan kuma surukin sarki,Allah ya jikan hussaini da dan fodio..maroka ne ke fadan hakan sau bila'adadin suna kuma maimaitawa da xakin murya sakamakon 1k notes da ake musu yayyafin shi

Isowar dokin sa tsakiyar filin yyi daidai da lokacin da yan bindiga suka shiga sake sautin harbin alburusai domin bada signal din isowar sa,anan har akayi leading dokin sa gaban canopyn da amarya da kawayen ta suke

Beutifully dressed Anties da kawayen amarya su sukayi ma amarya fatima zarah muhammad jagora har gaban dokin mijin ta.

A hankali take takawa dagwas dagwas kuma cikin nitsuwa da haduwa har ta kai ga gaban dokin a lokacin kusan hankalin kowa na kansu

Amarya Fatima tana dan aje kanta kasa cikin jin kunya Wani irin Kirari maroka suke zuba mata ana raha ana bin bayan ta da turare cikin nishadi har ta iso daf gaban sa.

"sautin guda mai shiga rai mata suka sake ayayin da shikuma ya dube ta cikin shauki yace.." Tubarkallah,u look so beautiful fatima.

Gyada kai kawai tayi bata tare da ta dago ba tace thanks
A matukar kunyace

Anan aka bude shafin daukar hotuna kowanni professional photo artist yana deban portrait dinsu ta kowani angle..

Murmushi take zubawa mai taushi tana ji aranta kamar Tun da take bata taba ganin mutane kamar na yau ba,duk da kasancewar ta layin karshe acikin jerin yayan sarkin sokoto
Wanda Allah bai nufa zasu auru da wuri ba amma sosai auren ta yayi albarka.

Fatima zarah yar sultan sarkin skt ce kuma itace mace ta farko ajerin yayan sa mata bayan aysah rukayya,hafsa da ummi da aka aurar.

She is 32,kyakkwa mai ilimi da sanyin hali,quiet unsual da Allah bai bata miji akan lokaci ba amma bata taba daga hankalin ta ba.

Wasa wasa sai jinkirin ya kasance mata alheri wajen samun old time boyfriend din ta tsohon dan siyasa Aliyu shettima wanda dama qaddara ne ya rabasu kuma wani qaddaran ya sake dawowa da su a matsayin ma'aurata.

Daga nan Babu bata lokaci aka cike duk wani gutsiru tsome da rububin biki
Har ma da na al'adun gidan sarauta Karfe 10 na safiyar washe gari akayi rakiyar amarya filin jirgi domin kai ta chan abuja inda gidan mijin nata yake.

Daga isar su abujan Anan ma wani sabon liyafa mai kayatarwa aka bude shafin sa,wanda dangin ango musamman ma mahaifiyar sa hjiya binta bulama ta sa aka kawata shi ya hadu har ya zamto abun kwatance a kasa.

A yadda ake zumudi ana tattalin amarya fatima in kai bako ne bazakayi saurin cewa akan kishiya za'a aje ta.ko da shike da alamar kishiyar nata bata san anayi ba dan ko idanun ta ba a gani a hidimar  ba bare kafafuwan ta.

Sosai aka sha hidima,da dare kuma aka yi cuncurudon convoy na motoci zallan kirar benz da mesarati har gaban wata kasaitacciyar mansion a unguwar maitama.

As a mansion as it is,ko ina haske yake yi kamar ba dare ba daura da bakin gate din xaka ga inda aka manna _Bulama JNR_ residence adan karamin gold plate mai shining,shuke shuke da flowers su suka kawata outdoor view na environment din sosai

Daga cikin gidan kuma gini ne mai na dauke da 15 correct bedrooms with bathrums of full sized jacuzzis,sai 7 big and well furnished palours 55 feet long royal dining table da garnished and lush interior decors komi anyi arranging dinsu tsaf.

A wani bangaren gidan akwai sites na fully loaded gym,a classy snooker hall sai manya manyan swimming pools of different designs and shape kowanne a side dinsa, garage ne ta waje da yaji cars tsadaddu na zamani kala kala wasu har an ajiye su waje under shades a haraban gidan.

Daidaikun matan ne suka fito tare da amarya cike da nuna tattali,a lokacin magajiyar matar sarkin skt da ayarin ta ne suka sauya sautin iskan gidan da zazzakar sautin gudan su

Amarya har ila yau sanye take da cotton maroon lace an rufe mata fuska da tsaddaden mayafi mai sheki assorted with expensive swrasvoki stones hannayen ta sunji asalin jan kumshi duk inda suka wulga da ita tana fida wani irin azaban qamshin traditional acent ahaka har sukayi cikin gidan da ita.

Duka duka Lokaci kalilan suka deba suna xaga wajen dukan su yan kawo amarya kowa yana raha ana sam barka,daga nan Har sashin amarya aka bi aka mata ban kwana cike da kewa kowa ya wuce mota domin a maida sa masaukin sa.

Itace a lullube luf zaune a tsakiyar fankacecen king sized italian canopy bed.

"Anty fatima toh zamu tafi...Allah ya bada zaman lpya.

Kanwar ta rukayya dake kusan tafi kowa damuwa da ita ta fadi haka ayayin da magajiya take kokarin rabasu da kyar dan kuwa dukan su hawaye ne akan a fuskan su.

Tun isowar su da safen rukayya ta kasa boye damuwar ta wajen nuna zakewa da tambayar shin ina kishiyar anty fatima take?dake kusan dukan su basu taba ganin ta a fili ba,ita kam ko da sau daya ne tana so ta gan ta da idanun ta

A Jiya Tunda suka zo abuja ba ace musu komi game da ita ba kuma ko yau din ma ance musu tana nan acikin gidan.

Abun ya dame kusan kowa amma dayake anyi bikin babu hayaniya sai ake yawan danne tsegumi

Magajiya dake ita ta manyan ta sosai in taga wani magana ya fara tashi sai tja rukyn gefe cikin ja mata kunne tana cewa"Anyi auren nan lpy rukayya ki iye bakin ki mana,be zama mana lallai sai mun ganta ba,kusan kowa yasan labarin hjya RAMAT,Bakar mutuwa ce wacce rashin ganin ta bashi zai hana fargaban gamo da ita ba.

Ita kuwa rukayya sam bata son jin haka dan har yau da fargaban auren dadan nata take kwana take tashi

Magajiya kuwa takan hakimce ne da yi mata bayani
Sai tace."Yo me aciki dan anyi biki har munzo bata fito ba?rashin fitowar ta ai Alheri ne agaremu

karki manta sarauniya fatimar mu yau ta kada tarihi mai girma a cikin gidan nan,dan kuwa itace mace na farko acikin jerin mata takwas da Alhj aliyu ya aura sumul garau Batare da anyi wani hayaniya da matar san ba Ajiyar zuciya kawai Rukayya ta sake Cike da daurewar kai da yake dada fallasa halin fargaban data ke ciki...

Tace"Magajiya ni fa bawai na matsa bane sai mun ganta,wani bin ne sai ina ganin kamar dan bata sani akan lokaci ba ne yasa tayi shiru,ai naji ance bikin anty faty sai ana daf taji labari kO?...

Mata takwas bata barsu ba sai ace akan anty fati ne xatayi shiru?

*HMM🤧🤧 kanemi naka kasha labari*
👇🏿
_YADDA AKE BIYA,HOW TO SUBSCRIBE,plus payment details_

_FARASHIN SA👇🏿_

#300 naira ne
#450 naira for VIPs

*1- Biya Ta bank acct*

_Use👇🏿_

Account name:
Surayyah muhammad suleh
Acct number 0152983148
Bank: GTB

*Sai ki tura screen shot shedan ki wa 👉🏿08036651119*

*2.MTN RECHARGE CARD OR VTU TRANSFER👇🏿*
*08060712446*

*Sai ki tura screen shot shedan ki wa 👉🏿08036651119*

*3:yan kasashen da ba nigeria ba masu biya ta PAYPAL,OR*
Use👇🏿

Account name:
Surayyah muhammad suleh
Acct number 0152983148
Bank: GTB
Phone Number :07058797141
CITY:bauchi

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top