Shimfida
Zahrau ce tsugunne gaban iyayenta Abba, Baffa, Mami da Amma suna mata Nasiha akan Zaman aure.
Zaune kawai take ba wai Dan kwakwal warta na daukan wa'azin da suke mata ba illa tashin hankali da bala'in da take ganin iyayen nata sun jefa ta a ciki Wanda su a ganin su gata suka mata.
"Allah ya miki Albarka, tashi kije ana jiranki" Firgigit ta dawo cikin hayyacin ta, Anty Zainab da Anty Rukayya ne rike da ita sai kuma Maijidda da Ummiy dake biye dasu tare da wasu yan uwa, Sai guda ke ta tashi duk farin ciki ke fuskan yan kai amaryar inka cire maijidda da Amina da su ke ta kuka. Anty Zainab ke ta musu fada akan zasu tada ma amaryar hankali, Mutane da yawa ganin su rabuwa da Amaryar ya sa su kuka sai dai su suna mata kukan takaicin gidan da zata ne, gidan da su ka kira bakin gida Wanda su ke da tabbacin ba komai a ciki sai tsangwama, Wahala, mugunta da dai duk wani abin takaicin rayuwa.
"Anya su Abbah sun San abin da suka hada kuwa?" Ummiy ke tambayan kanta a karo na ba adadi, ta so ba Fatima bace zata fada wannan gida at least da ace ita ce ko maijidda ba shakka za su iya kwato yan cinsu amma Zahrau duk cikin su tafi su tsoro da sa abu a rai. "Bakomai ai in ya sa mata ciwon zuciya ta mutu kowa ya huta"
A haka suka isa motan da aka tanada domin amaryar, Hamza ne ke tukin sai Ummiy a gaba, Amaryar da Maijidda da Anty Zainab a baya. A hankali motan ke tafiya, mota daya a gaban su daya a bayan su, duk dai close families ne a cikin. A jere motocin suka fita birnin zazzau ...
Tabdi jam wai shin wanene wannan Wanda ake ma ikirarin azzalumi?
Me yasa su uku kadai suka fahimci hakan?
Sai dai an CE
KOMIN HASKEN FARIN WATA DARE ABIN TSORO NE...
Updates will becoming Once or twice in a week in sha Allah
Ku biyo ni
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top