KHF 9

                             6:06 pm

    5:30 na yammaci ake tashin su amma sai shida su ka isa gida a sanadiyar fadan da suka tsaye. Kaman yanda suka saba gudu suke ta shatatawa sai ka rantse gudun tseran rai su ke.

  Flowers in da ke kofan gidan ya sa ya ke son zama a wurin kasancewar shi mutum mai son iska. Kaman kullum da yamma yake zaman zaka ganshi da abokanan shi kala kala suna hira sai dai yau shi da Umar ne kadai.

  Abokan takan su da Umar in ya fara ne time in lokacin da suke JSS1, suna labari ne sai Umar ya ke ce shi ma dan Zaria ne, "ta wani area?" Aliyu ya tmby, "Gaskiya layout but kwanan muka yi relocating" Gano wa da suka yi su yan unguwa daya ne ya sa suka fara shiri sosai. Wasa wasa har iyayen su suka San juna, presently kam tare suke a ke kai su in zasu koma haka dawo wa har ma da visiting tare ake zuwa musu, duk inda kaga daya ko shakka bbu dayan ma na nan. Zuwan yanzu sun wuce abokanai sai dai mu kira su aminai ko ma yan'uwa.

Umar in ne ya fara hango su suna tahowa "Ga fa mutanen ka sun Faso" ya fada yana kallon irin gudun da suke, shi kam ko kadan ba sa bata mai rai, yaran kawai abubuwan su dariya da nishadi suke sa mai.

"Mtsww" tsaki Aliyu ya ja hade da fadin "yara sai kace dabbobi, ba su taba komai cikin natsuwa"
"Aliy kenan they are just a kids ai zasu dena"

Su na ganin shi a bakin gate su ka daina gudun hade da Shiga taitayin su, a daddare su ka gaida su "little angels, are you back?" Umar ya tambaye su.

Dukkan su bin shi suka yi kawai da kallo ba wai Dan sun fahimci abinda yake nufi ba. "Can't I have an answer?" Ya daga musu gira.

Da za a ba Ummiy wuka to ba abinda zai hana ta caka mishi Dan ita a ganin ta ya ma fi Uncle Aliy iyayi don shi bai musu turancin saboda ya San basu iya ba.

"Me kuka tsaya yi a hanya?" Kaman daga sama suka ji tambayan Aliyun

Dukkansu shiru suka yi suna kallon shi ba wacce ta iya bashi amsa.

"Ba magana nake muku ba dukkanku kun wani bini da wasu munanan idanuwanku na mujiya, ni sa'an Ku ne?"

Da sauri suka sadda kan nasu kasa "maza Ku Shiga ciki Ku cire kazaman kayan da ke jikin Ku Ku dawo yanzun nan"

  Da sauri su ka nufi gate in Shiga, yanda suke rige rigen fara wuce ne ya ba Umar dariya "Aliy wlh ba ka da kyau ji yanda su ke reacting kaman sunga mala'ikan mutuwa"

Ba su dauki cikakkun mintuna goma ba su ka dawo kiran da yake musu, daidai lokacin Napep ya sauke Anty Zainab, mantawa su ka ma yi da Aliyu na wurin su ka ruga wurinta suna "Oyoyo ga Antyn kano"

  Ita ma cikin Murna ta bude musu hannunta su ka karasa ta rungume su duka Ukkun "Oyoyo yan kannena,  I miss you"

  Sai da ta sake su Umar ya gaishe ta yana fadin "Anty kin mana zuwan bazata" Murmushi ta yi sannan tace "Abinka da yan Jami'a"

Sai a sannan Aliyu ya dago kanshi cike da girmama wa yace "Ina wuni Anty zee, kin sha hanya" hararan shi tayi "Ba zan amsa ba wato kai jin kai sai kowa ya gama magana za ka yi ko?"

"Anty ba fa haka bane, kinga ai zanyi distracting insu kema kuma zaki rasa wa zaki ma responding"

Girgiza kai tayi tace "Allah ya shiryeka Aliy, mu karasa ciki ko"

"Assalamu Alaikum" aka fada daya sa dukkan su juyawa Dan ganin me magana.

Dan matashin saurayi ne kusan sa'an Aliyun da yarinya mace karama, Ummiy na ganin ta ta ruga zata Shiga gida, wani tsawa Aliyu ya daka mata.
Dolen ta ta tsaya, da kagansu ukun kasan ba su da gaskiya.

"Nan ne gidan?" Saurayin ya tambayi yarinyar da suke tare

"Ehm Yaya ga su nan ma" ta fada tana nuna su Zahrau.

Hannu ya ba su Aliyu su ka gaisa sannan ya fara mishi bayanin abinda ya kawo su. "Daman nazo Dan Allah ya kamata ka sawa kannen nan naka ido dalili kuwa shi ne suna takura wa yara yan'uwansu in an tashi Islamiyya sai su jasu fili su musu taron dangi, kaga yarinyan nan ita da yar'uwarta da sauran kawayen su na kusa damu sun musu ba sau daya ba ba sau biyu ba shine dai aka turo ni kila in aka musu fada a gida zasu daina."

Ba Wanda ya mishi magana har ya kai aya. Anty Zainab bin su tayi da kallo game da fadin "daga dawo wa na ba za Ku Sani magana ba daman Aliyu shine daidai da Ku" shiga ciki tayi niyya Zahrau ta rike gyalenta kaman za tayi kuka tana rokon ta da idanu kar ta tafi Dan tasan mai cecen su yau sai Allah.

"Bakomai, Nagode, Dan Allah ka bada hakuri zamu dau mataki" Aliyu ya fada ma yaron

"Bakomai, ni ke da godiya"

   Dukkansu ukun ya kamo sai zare idanu su ke  suna kiran Anty zainab ta cece su "A dai yi sassauci Soja"
"Ke dai Anty je ki kawai"

  Frog jump ya sa suyi kowacce round Talatin, duk sun jigata gashi ba daman tsaya wa Hutu ko kuma suyi cucuwa Dan kar ya ke kallon su.

Duk round in da suka yi in za su koma sai Umar ya ce musu "Sannu fah" hakan na kara kona musu rai ganin cewa shi bai taba bada hakuri in ana zaluntar su (a cewarsu) ba kuma zai sa hannu ba haka kuma ba zai tura ba sai dai zai yi duk abinda ya San tsokana ce dan ya kara bata musu rai.

Sai da aka kira Sallahn magreeba sannan ya kyale su duk sunyi sanyi, da kyar su ka iya karasa wa cikin gida wurin mami sai hakki su ke.

    Sai Bayan Sallah Isha'i ya koma gida, sassan Mami ya nufa ya same ta ita da Ammah da Anty Zainab suna hira. Gaishe su ya fara yi suka amsa

"Daman jiranka nake ka dawo ka fada min in yarana ma sun zama sojoji ne?"

"Mami me ya faru?"

  "Au bama kasani ba frog jump in da kasa su fa"

"Mami yaran naki ne terrorist ne Allah, Anty Zainab bata fada miki me suke yi ba"

"Naji ta fada amma hukuncin ka ya musu tsauri, duka duka nawa suke?"

"Shknn Mami, za a rage"

  Ko da ya nemi su kawo mishi spellings in da ya basu da kyar kowaccen su ta iya kawo biyar biyar a sakamakon wahalan da su ka sha a wurin shi yammacin ranar.

Ranar ko da zai koma makaranta yanda kasan an musu albishir da Aljanna haka suka dinga ji.

They are free again, rashin ji sai abinda yayi gaba karatu ko ko oho baya gabansu, anyi fadan a gida har an gaji, kullum cikin kawo karar su ake, yau sun tsokani wannan gobe sun bugi wancan sai ya zamo Allah Allah Aliyun ya dawo ake a gidan dan shi kadai ke iya musu.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top