KHF 8

                                2:30  pm

                        Gaskiya layout

Motar da ke dauko su daga school ne yayi parking a harabar gidan su. Zahra ta fara fitowa saboda ta fi kusan da kofar, barret in da ke kanta ta cire tana fadin "kai ni wannan abun ya isheni, mutum ba kwaikwaido ba ace sai ya sa wani barret" Dariya yan'uwan nata su kayi sannan Ummiy ta ce "wai wai Zahra Allah da bamu da gashi da mun Shiga Uku wurin ki"  Hamza ne ya fito daga kujeran mai zaman banza rike da shahida da ya dauka, a jikin shi kawai ta ke in har za su school dalili kuwa Aliyu ne ya tsawatar mishi da kar ya sake ya ganta tare da su Zahrau kar su maida ta kaman su, su ma ko ko ajinku su Dan ko kallon banza shahidar ba ta ishe su ba a cewarsu ba su son raini. Karshe Zahrau cire ribbon in kanta tayi sannan ta bazo gashin. Gaf da za su Shiga sassan Ammah su kayi kicibis da Aliyu.

Da sauri shahida ta fada jikin shi tana mishi oyoyo, daukan ta yayi yana fadain "little sis hope dai kinyi karatu a school ko" Gyada mi shi kai tayi sannan Hamza ya gaishe shi.

  Mutannen shi ko tun da su ka ganshi su ke dar dar Dan kar su kuma wani laifin ya sa su ka tsaya gaishe shi Sannan su ka nufi sassan Mami da gudu.

"Kaiii" wani irin tsawa ya daka musu har hanji cikin su sai da ya kada "Ku ba Ku iya komai a hankali? mahaukatan banza kawai Ku zo nan dan kaniyan Ku"

  Jiki na rawa dukkansu ukun su ka karasa wurin shi, Harara su ka bishi dashi Wanda suka wa fassara da kallon tsana ya ke musu domin duk gidan su kadai ya takura ma wa.

"Ban hanaku gudu ba?" Ya tambaya "a tare su ka girgiza kai jikinsu sai kadawa yake " ni kadangare ne zan dinga muku magana kuna amsa min da kai"

"Aa kayi hakuri Dan Allah ba za mu sake ba" Wannan karan ma a tare su ka amsa Zahrau kan har ta fara kwalla kasancewar duk ta fisu tsoro.

"Ku wuce Ku ban wuri kuma zan zo Ku fada min ina kuka je kuka jikin Ku jiya"

Da sauri su ka bar wurin maimakon sassan Mami Sassan Ammah da su kayi niyyan zuwa tun farko su ka nufa.

Zahrau da ke baya ya jawo gashin ta ya ja, har cikin kwakwalwarta taji zafi amma tsaban tsoro ta kasa ko da kukan. Kunnen ta ya ja "ke ce mai kunnen kashi ko? Ban hanaku barin kai a bude ba? To wlh duk ranar da na sake ganin daya daga cikin Ku ta fara kai bude dukkanku zan hada inma aski ai bakin Ku daya."

  A tare su ka juyo suna kallon shi ya ko galla musu harara, jiki na kyarma su ka bar wurin, Zahrau ko duk a zaba ne ya ishe ta, tsabagen tsoron da ta ke mai ne ya sa ta kasa sakin kara, Ranar dai da ciwon Kai ta kwana don har islamiyya ma bata je ba.

   Asalin Rashin jituwar Aliyu da su Zahrau ya samo asali ne saboda rashin jin da suka sa a gaba ga wasa ba abinda ya kai shi mahimmanci a wurin su. A bangaren karatu kuwa za a iya basu 0.000... Till infinity % saboda ba abinda su ka Sani, bai gaban su ko kadan, ba dadikai bane Aa mai da hankalin ne kawai ba sa yi both boko da islamiyya sai dai tonon fada da kuma wasan da su ka sa a gaba. Primary 1 suke amma yanda kasan ko na awa daya ba wacce cikin su ta taba zama a aji Dan ko shahida dake Nursery 1 tafi su sanin karatun, lesson teachers kala kala ba Wanda ba a dauko musu ba amma gajiya suke cause ba su taba mai da hankali balle suyi gaining. Ummiy ce oga don ita zata fara tabo daya daga cikin su to daga nan zancen karatun ya tsaya saboda fada za su kaure da though daman they are not concentrating.

Ba karamin konawa Aliyu rai hakan ke yi ba, yayi bugun, zagin duk a banza hakan ya sa da kanshi ya ce yana so ya dinga koya musu, aka ko bashi dama.

Dalilin da yasa suke ce mishi uncle kenan sai dai har yau din ba wai suna mai da hankalin bane, ba irin punishments da dukkan da basu sha a wurin shi ba amma duk a banza, ba dai fada ko wasa A'a tsoron da su ke mai ne yasa basu fahimtar komai.

  Presently SS1 ya ke a Air force base, burin shi ne tun yana karami ya zama soja hakan yasa bai je ordinary secondary school ba.

   Time table ya ke musu yau na islamiyya gobe na bako, yau inma zaune su ke a suna kallo yana musu spellings da basu wuce Three to four letter words ba, yana karantawa suna amsawa da karfi ba wai don ransu na so ba Aa Dan ba yanda su ka iya ne.

Ya maimaita ya kai sau Ashirin sannan ya ba wa ko nashi 10 10 ya koya personally. Wa'azi ya fara musu me ratsa jiki don su dinga mai da hankalin su kan karatu, abin mamaki yanda su ka natsu suna sauraran shi za ka dauka da gaske shigan su yake nan ko shiga yake ta daya kunnen ya fita ta dayan. Kusan 20 minutes ya basu su duba sannan ya yace ko wa ya ko nashi. Ta kan Ummiy ya fara abin ya mugun daure mai kai ganin ko daya kasa kawo mai tayi har gwara Zahrau da Maijidda sun kawo Uku da kyar.

Tsabagen takaici shiru yayi ya rasa abin cewa, to su yaran nan me za a musu su dauka? Fadan yayi, dukan yayi, wa'azin duk a banza... Shi ya dauka wasa ke hana su mai da hankali or are they naturally dull? In ko haka ne ba zai taba gajiya ba, kannen shi ne zai yi komai ya ga su na koyan ko yaya ne.

Hawan machine ya sa su, kasancewar shi Dan Air force ba irin kind of punishment in da bai Sani ba, duk kafan su sai da ya sage suna kuka sannan ya bar su su je su kwanta da sharadin gobe za su kawo mai spellings in.

  Zahrau ce zaune a dakalin da ke gefen ajin su, tayi tagumi tana tunanin haduwar su da uncle Aliy anjima. Zahrau mutum ce mai surutu da tana karama girmanta ne ta koma so calm.

"Hey princess" taji an fada hakan ya sata dago kanta, Abdulrahman ta gani a gaban ta yana mata murmushi itan ma murmushin ta mai da mai, ya kan tuno mata da yayanta Deedat da ke Zaria Academy jss2.

"Lfy na ganki ke kadai ina frnds"

"Sun tafi wasa, ni ka gan ni nan matsalata Uncle Aliy ya bamu spellings kuma ban iya ba kuma duka yake duk tsoro nake ji"

"Ayya princess kawo in koya miki mana"

Da gudu ta je ta dauko littafin a school bag inta ta mika mai.

Da ke ta sa kanta sai gashi ta iya nan da nan, sweets ya bata ta koyi murna sosai.

A daya bangaren ma Maijidda seat mate inta ya koya mata.

**************************

Yau ma kaman kullum suna dawo wa suka tafi islamiyya, malam na fita aka fara yan ture turen benci, wata yarinya tsautsayi ya sa ta ture Zahrau ta fadi yan ajin kaman jira suke suka sa dariya ai ko nan da nan ta fashe da kuka, Maijidda ce da wata suka daga ta suna rarrashin ta Ummiy ko zuwa tayi ta shake yarinyar tana wlh baza ta yadda ba sai ta rama, kafin kace me aji ya kame da hayaniya sai kokarin raba su ake, Ummiy ko ba ta hakura ba sai da ta daga hannunta ta kifa wa yarinyar wani lafiyayyen Mari, ba shiri ta sa wani kara hakan yayi daidai da shigon malam.

  Dukka yan ajin ya hada ya Zane, abin ya musu dadi dukkansu ukun dariya su ka ta wa sauran yan ajin har da gwalo ace war su hakkin dariyan da suka wa Zahrau ne.

Bayan an tashi Islamiyya yarinyar da suka yi fada da Ummiy ta tare su ita da yayarta wai ba za su yadda ba sai ta rama Marin ta. "Ba matsala aje filin can sai ki raman" Maijidda ta fada tana hararan su.

Filin a ka tafi, suna isa suka ajiye jakunku nan su hade da cin dammara.

Jiyo wa yarinyar tayi da sunan zata rama Marin Ummiy ta cafke hannun ta mirda shi, ji kake Ttassss ashe rabon wani Marin ne ya kawo yarinyar.

Yayar ce tayi kan Ummiyn sai dai kafin ta isa  Maijidda ta jawo ta zubar a kasa.

Maijidda da Zahrau ne suka tarun ma yayar saboda tafi su kadan Ummiy kuma da yarinyar sai da suka musu lalaga lalaga sannan suka ruga su ka bar su a wurin.

•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••

To fah... We are seriously dealing with a great  fighters.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top