KHF 7
My Appreciation goes directly to a wonderful lady @meenatty you have no idea how your comment makes my day, this page is specifically dedicated to you and FYI I decided to update just because of you, hope you will enjoy.
Asalin labarin
Justice Abubakar Tafida Dan asalin
Unguwar Alkali dake cikin Zaria city ne.
Family insu family sun gaji sarauta da malinta ta ko ina, yana Dan shekara Goma Sha biyu Allah yayi wa mahaifin shi rasuwa mahaifiyar shi daman tun wurin haihuwar shi ta rasu, hakan ya sa rikon shi ya koma wurin Baffahn shi da su ke abokannan wasa da mahaifin shi.
Ya taso cikin gata da tarbiyya na gari ko kadan bai San maraici ba don ko ya rike shi cikin gaskiya da Amana.
Ya'yan' Baffahn na shi biyu Ahmad da Al-ameen Turaki. Suna matukar girma ma shi kasancewar ya girme mu su nesa ba kusa ba haka kuma Kansu a hade yake.
Mami yar asalin jahar Gombe ce, sun hadu da Abbah wurin bikin Abokin shi da yaje can Gomben ita kuma yar'uwar Amaryar ce. Kaman wasa magana mai karfi ya Shiga tsakanin su har su kayi aure.
A gaskiya layout ya siya Babban fili yayi gini dayawa a cewar shi shi da kannen shi in sun tashi aure.
Muhammad ne Babban dansu sai Zainab sai Aliyu da ga nan kuma haihuwar ta tsaya musu don basu yi zaton za su kara samun wani ba. Aliyu na da shekara biyu Kannen baban sa suka yi aure su ka tare a gidajen da yayannasu ya tanadar musu. Ammah yar nan cikin Zaria ce, Mummy KO cousin in Mami ce ta gama karatun secondary ta zo mata Hutu a nan su ka hadu da Daddy Al-ameen.
Su gina zuri'a me kyau wurin fahimtar juna da kuma tafarkin Addini. Bayan shekara daya da auren Ammah ta haifi Deedat sai dai mummy shiru kake ji amma da yake ance komai lokaci ne abin bai dame su ba.
Bayan shekara Hudu Mami ta same cikin Hamza, sunyi farin cikin ba kadan saboda ba su yi tsammani za ta kara haihu ba saboda a lokacin Aliyu ya shekara bakwai ma. Bayan 2 years mami ta kara haifo yan biyu Amina (Ummiy) da Hauwa'u (Maijidda) Wanda kuma sai lokacin Mummy ta samu cikin ta na farko. Ba karamin wahala yake bata ba tun yana karamin shi amma sun danganta hakan da haihuwan farko ne shiyasa. Haihuwar yan biyun da one month mummyn ta haifo Fatima (Zahrau) bayan wahalan nakudan da ta gama sha Dan har an yanke shawaran yi mata operation ma Allah yayi ikon shi.
Tana da wata bakwai Mummyn ta tafi Gombe ganin gida, Daddy (Al-ameen Turaki) ya je dauko ta a hanyar su ta dawo wa suka yi hatsari.
Kiran su Abbah aka yi aka sanar musu, a gigice suka isa garin Gombe kasancewar inda suka samu accident in ba nisa da cikin Gari ya sa aka maida su Babban Asibitin Gomben.
Ba karamin rauni su ka ji ga karaya ko ta ina motan nasu ma kaca kaca yayi, wani ikon Allah Ba wani Abu da ya samu Fatima sosai.
Sati daya a na musu treatment ba wani cigaba har a yanke shawaran fitar da su waje sai dai suna nasu Allah na nashi domin a ranar Mummy ta amsa kiran ubangiji, sunji mutuwar ba kadan ba ya girgiza su haka wurin yan uwanta. Jin Mutuwar Mummy ya girgiza Daddy ba kadan ba tunda daga ranar ba su kare gane kan shi ba, Cigaba da shirin fitan su ka yi suka mai da shi Ahmadu Bello University Teaching hospital (Shika).
Awanni Uku bai yi cikakku ba ya bi bayan matar shi. Kulli nafsin za'ikatul maut babu makawa kowa sai ya tafi lokaci kawai ake jira. Tausayin kan Zahrau ya koma ganin tun kafin ta shekara daya a duniya ta zama marainiya ba uwa ba uba, hakan ya sa su ka dauki son duniya su ka daura mata. Yan'uwan mahaifiyarta sun so a basu ita Abbah yaki yadda ganin Mami na shayarwa ya'ya' har biyu ya sa ya ba wa Ammah ita. Sai dai har yau Zahraun bata San cewa iyayen nata sun rasu ba Dan ita duk a cewar ta Ammah da Baffah ne suka haife ta. Sun dai San akwai Mummy da Daddy da suka rasu ana cewa su dinga musu addu'a.
Shahida, Yusrah da Adnan Ammah ta haifa bayan Deedat. Gaba daya Zuri'an nasu kenan.
August 2005
Zahrau ce zaune kan wani dakali wurin kan kwanar layin gidan su, daga wurin tana iya hango ko mai da ke faruwa a kofan gidan, kayan Islamiyya ne a jikin ta Dan da Alamu an tashe su daga Islamiyyan ne, Yunwa ne ya kora ta tabar yan'uwanta sai dai tsoron abinda take gani a kofan gidan nasu ya hanata komawa.
Tana zaune ta marairai ce kaman tayi kuka sa'anninta suka wucewa da gudu wai suna rige rigen zuwa gida, Turus su kayi ganin ta a zaune.
"Sarkin jin Yunwa gidan kenan" Ummiy ta fada cike da tsiwa, sannan Maijidda ta amshe da fadin "Kai wlh Zahra kallo ya wuce ki in gaya miki bugun tsiya mu ka musu Hadiza sannan muka tsero kar su hada mu da malamai kinsan su shegen tsoro ne dasu" "Hmm duk ba wannan ba" ta katse su "Ku kalli kofar gida Ku gani"
A tare suka maida hankalin nasu kofar gidan abinda su ka gani ba karamin kidima su yayi "Mun Shiga Uku, Uncle Aliy ya dawo Hutu" Maijidda ta fada tana zaro idanu, Ummiy ko wuri ta samu ta zauna tana fadin "ban ga laifin ki da kika zauna ba Zahra ni Babban takaici na ma wancan Abokin nashi mai iyayin tsiya yanzu ya tsare mutum da turanci shi ala dole Dan boko" Hamza ne ya zo wuce Dan shi har yaje gida ya canja kaya wurin Abokin shi ya je amsan abu. "Lafiya har yanzu ba Ku koma gida ba?"
"Ina fa lfy ka na ganin Uncle Aliy na gida" Ummiy ke magana cike da tsiwan da ya hali nata. Dariya ya kwashe dashi hade da fadin "Haba shiyasa na ga ana turo baki, ko ba komai rashin jin Ku zai tafi na kwana biyu" Gwalo ya musu. Hararan shi Ummiy ta yi Maijidda ta ce "Haba Hamza harda kai, shknn" Dan darawa yayi sannan ya ce "Ku ne ba Ku ji gashi ba Ku son karatu shiyasa ba Ku shiri da Yaya Aliyu" Juya mishi kai su kayi su ka yi banza dashi, Zahrau ko yunwan da ta ke ji ne ke kwakular cikin ta, rabon ta da Abinci tun breakfast. Za ta ci suka azzaza be ta taso su tafi wai su kama benci da wuri yanda za su yi rashin Mutunci.
Ganin da gaske su ke ba za su tafi ba yasa Hamza yayi tafiyan shi ya barsu.
Hadari ke haduwa a wurin kafin kace mai ruwa mai karfin gaske ya sauko kasancewar watar August ne.
Da gudu su ka tashi su ka fake a jikin wani gida amma duk da haka sai da suka jike. Tsaye suke a wurin suna rawar dari har aka kira Sallahn magariba sannan ruwan ya tsagaita sai da su ka hango mazan gidan su sun fita masallaci sannan su ka ruga gidan.
Ba su San gudun gara su kayi su ka afka gidan zago don a bakin gate su ka hadu da Aliyun yana sauri kafin a tada Sallah. Kallo ya bi su dashi ganin yanda Uniform insu da jakukunan su su kayi sharkaf da ruwa, harara ya bi su dashi ya jawo Ummiy da Maijidda ya gwara Kansu wuri daya, wani irin gigicewa su kayi amma tsoron da suke mai ya hana su kuka. Koma yayi kan Zahrau ya ja kunnen ta sannan ya rankwashe ta a kai bare baki tayi zata fara kuka, kallon da ya mata ya sa ta yin saurin mai da kukan. "Bari in dawo daga Sallah sai kun fada min inda kuka tsaya Ku ka jika jikinki" ya fada hade da yin saurin karasa wa masallaci. Su kuma a guje su ka karasa cikin gidan.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top