KHF 6
11:00 Am
Safiyar Asabar
Dubban mutane su ka shaida daurin auren Aliyu Abubakar Tafida da amaryarsa Fatima Al-ameen Turaki. Daurin auren ya samu halittar mutane da dama Wanda ya hada da Manyan sojojin Nigeria, Manyan malamai, masu sarauta, yan siyasa dama ma'aikatan gwamnati ta wani bangarorin Nigeria. Both Abbah da Baffah mutane masu hulda da jama'a dayawa shiyasa in kaga dimbin mutane da motoccin da suka samu halattar auren sai kayi tunanin yar wani mai fada aji a kasan nan ne tayi auren.
Gagarumin Reception mazan suka wuce daga wurin daurin auren,
Ba kauyanci ba ni dai nace ba irin cuisines in da babu a wurin nan, Naira ta Sha kuka.
Dole ta sa Aliyu sakin ranshi saboda dimbin mutanen da suka zo taya shi murna su a cewan su kenan shi kanshi Mutum ne mai jama'a sosai.
*************
A can gida ko, ko ta ina ya kicime da mata da kuma yara sai kai kawo su ke a ko ta wani bari na gidan.
Amaren dole ya sa su barin sashen su da ke cikin gidan su ka koma bangaren Babban Yaya. Ita kanta Amaryar tayi mamakin kawayen da ta gani duba da yanda yanayin auren ya zo, ita da kanta ba tayi gayyata ba aikin su Maijidda ne da kuma su fati.
Tana ganin Sha daya yayi gaban ta ya fadi, shakka babu yanzu haka daura auren ake, auren ma nata kuma ba da Abdul rahman ba ba kuma Sulaiman ba A'a da Uncle Aliy mutumin da tun tasowarta ba Wanda ta ke tsoro irin shi, ganin shi kadai fadar mata da gaba yake balle magana ta hada su.
Bayi ta shi ta dauro Alwala hade da gabatar da Sallah raka'a biyu tana rokon Allah neman dukkan abin Alkhairi a rayuwarta. Kawayenta suka sa ta a gaba suna ta tsokanar ta wai tana tsoron auren share su tayi ta cigaba da azkar inta amma abin ka da taron yan bodin sai da su kayi nasarar sa ta kuka, nan kuma sai su ka koma lallashinta gama daman sun Santa da saurin kuka, ai ko sai da ta samu yan'uwan da suka taya ta kukan.
Set in kaya kala biyu aka mata hakan ya sa aka jera daya a nan bangaren shi da ke kusa da na Babban Yaya dayan kuma Abuja a ka kai.
Samun Abbah Aliyu yayi ya sanar dashi suna da wani important aiki da za suyi ranar Monday a Abuja, ko kallon banza Abbah bai mai ba balle ya hana shi sai ma ce mishi da yayi ita ma Zahrau ranar Monday din za a kai ta can Abujan saboda bai ga reason din da zai sa a barta a nan ba bayan an daura auren.
Sarai ya gane Abbah ya dago shi ne ya sa ya mai hakan sai ma yayi dana sanin abinda ya fada wannan shi ne anyi gudun gara an fada gidan zago gashi kuma ba zai iya samun Baffah ba ko ba komai ido ai da kunya.
Cigaba da sha'anin bikin aka yi, Walima na mata kawai Wanda aka yi a cikin gidan, malama ce wacce tayi wa'azin.
Monday
4:00 pm
Ba abinda ya rage na game da shirin kai amarya gidan ta da ke babbar birnin tarayya Abuja.
Ba wasu mutane masu yawa bane, close relations ne kawai mota uku.
Ta sha kuka idanun ta duk sun kumbura, kawayen nata ma sai da aka Samu masu tayata kuka hatta kannen ta shahida, Yusrah da Adnan a bar su a baya ba.
A haka aka kaita wurin iyayen nata domin su sauke nauyin da ke kansu. Daga Mami har Amman dauriyan yi Mata magana su kayi coz su ma ba karamin alhinin rabuwa da ita za su yi ba. Nasiha su ka Mata mai ratsa jiki sai dai jinsu kawai ba wayai ta na fahimtar abinda su ke fadin ba Dan tuni ta yi nisa a duniyar tunanin rayuwar da zata afka.
Bayan an fita da ita wani irin Farin ciki ne hade da annashuwa ya ziyarci zuciyoyin iyayen nata Dan ganin sun sauke nauyin da Allah ya basu. Sun sauke Amanar da Dan'uwansu ya bar musu.
A jere motoci ukun ke tafiya... Umar ne ke tukin second car tare da Nanah, fati sai Anty Rukayya last car in kuma Deedat ke tuki da Yusrah a gefen Shi sai Anties biyu da shahida.
6:30 pm a cikin Abuja ta musu a gidan Aliyun da ke Asokoro Villa. Har an yi magriba da ke lokacin sanyi ne so suna isa Sallahn su ka fara gabatarwa. Ita dai Zahrau dar dar dar kawai ta ke don ta kasa yadda nan ake nufin ta zauna a matsayin gidan auren ta kuma wai da Uncle Aliy. Ya ilahi anya su Abbah sun duba abin nan kuwa.
Gidan ya hadu sai santin Shi suke tayi brain ma da aka sa kayan nata.
Babban gida ne da ka shigo side in mai gadine ta left side sai parking lodge na gaban Shi. Wani small garden ke facing wurin an shuka differents kinds of fruits a wurin an shinfide da grass carpet ta gaban Shi ko flowers ne da sukayi brightening wurin so alluring. Steps uku ne zai sada ka varendar first parlor in Wanda akayi decorating in Black and ash, kujeru, carpets, pots of flowers da frames in pictures. Dayan parlorn in coffe brown da milk, kujerun kadai abin kallo ne balle a kai da Babban television in da ke a jiye a wurin. By the right side corridor ne na 2 bedrooms, daya daga ciki Shi ne na Amarya, in purple and cream aka shirya Mata dakin da ka ganshi kasan kudi yayi kuka sai dayan room in ne dai empty da Alamun gida yayi Shi ne Har zuwa nan gaba. By the left nan ma 2 bedrooms ne nan master bedroom ya ke Wanda ya ke shirya in Royal blue gaba daya, sai dayan room in computers in Shi da bench in books ne a wurin da Alamun dai study room ne. Dinning ne kafin ka kai rooms in da suke left side in Shi ma sai an sauka daga steps tukunna sai kitchen a gefen Shi, kayan kitchen in ba karamin kyau su kayi ba in lemon green and ash ne komai ma masha Allah za a ce.
Sai da suka yi Sallah sannan Aliyun ya zo su ka gagaisa ya sa aka kawo musu Abinci.
Sun dade suna rarrashin ta da yi Mata nasiha Banda Ummiy da ke bata shawaran in ya Mata Wani Abu ta fadawa Abbah kar ta yadda ya wahalar da ita a nan har Maijidda sai da ta bata rashin gaskiya su ka nuna Mata tun da an riga an daura hakuri Shi ya fi komai.
Washegari bayan Azahar su ka shirya komawa Zaria bayan sun Kara yi Mata nasiha, da kuka ta raka su haka duk kawayen nata da suka zo kukan su ke yi sai Anties in nasu ne ke musu fara. Sai da Umar da Deedat su ka sa baki tukunna su ka yi shirun.
Da gudu ta koma cikin gida ganin motansu ya fara tafiya, dakin da aka kira nata ta shiga tana bi da kallo komai na gidan ya Mata in aka cire Shi mai gidan da kanshi, ko Wani irin rayuwa za suyi? Wahala mana za ki ta sha wata zuciyar ta bata amsa.
A hankali ta fara tunano rayuwarta gabadaya, irin wahalan da su ka sha hannun Shi da kuma irin ta ta rayuwar soyayyar...
Asalin labarin...
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top