KHF 49

A rude ya ke bin wayan da kallo, kasa aiwata komai yayi saboda jikin gabadaya rawa ya ke yi.
Da kyar ya Kai Kan shi tsakar gidan shi, da hannu ya yafito driver in shi ya karaso, key mota kawai ya Mika mishi sannan ya bude motan ya shiga.

Driver in Bai tsaya Kara wani tambaya ba domin ya gane abinda ogan shi ke nufi sai da ya fita titin layin sannan ya tmby shi inda za su je.

"Zaria" kawai ya amsa Mai sannan ya runtse ido, cike da mamaki driver in ya bishi da kallo, Anya kuwa ya ji da kyau? As in Zaria hakanan kawai.

"If you won't drive hand the key over!!" hannu ya mikawa driver in da ya daburce saboda tsawan da ogan shi ya mishi.

Nan da nan ya fara driving ya Kama hanyan fita Abuja, gudu ya ke sosai Amma Aliyu bai ganin hakan.

Sai da su ka iso zuba tunanin Kiran Deedat ya Zo mishi, Allah ma ya sa Yana gari. Numban Deedat in yayi dialling, Yana fara ringing ya dauko "hello Ya Aliyu"

"Kana Ina ne" ya tambaya direct.

"Ina Nan Asibitin, Doctors in suna kanta"

"Okay sai na zo" ya fadi sannan yayi ending call in.

 
In 3 hours su ka Isa Zaria, Kai tsaye samaru su ka nufa zuwa asibitin shika sannan ya Kira Deedat domin ya mishi kwatancen inda su ke.

Ko da ya Isa a kofan daki ya iske Hamza da Deedat in suna zaune, Daurewa yayi su ka gaisa sannan ya bukaci sanin halin da matar shi ta ke ciki.

"Alhmdlh komai yayi dai dai Ina ga ma bacci ta ke, ga dakin da suka ba mu Nan" Deedat ya fada Yana pointing dakin.

Handle in daki ya murda yayi sallama. Shahida, Yusrah, Fateema da Ammah ya tar a dakin, Amman ya fara gaidawa sauran su ka gaishe su ya amsa game da tambayan Mai jiki.

Ya na shigowa dakin ta farka sai dai jin muryar shi ya sa tayi lamo kaman da gaske baccin ta ke. Jefi jefi ake Hira a dakin shi dai ita kawai ya ke kallo ya na rokon Allah  ya sa ta farka ko sa yi magana, Kiran Sallan la'asar ya sa dole ya bar dakin su ka nufi masallaci. Ana idarwa ya yanke Shawaran wuce wa cikin Zaria ya gaida Mami.

A Falon ta ya iske ta tana cin kallo, bayan su gaisa ne ta ke tambayan shi Mai jikin. "Aliyu ni ko sai Inga kaman abu aka ma yarinyar Nan ya sa ciwon ta ke neman tasowa, Anya Aliyu?"

"Mami me Kika gani? Kinsan sha'anin masu ciki balle ma ita nata da ya ke bata wahala tun farko"

"To Allah ya sa, ni dai ban yarda da Kai ba, ka dai ji tsoron Allah, Allah ya kyauta" sosa Kai ya fara yi ganin Mami na neman turke shi, a hankali ya silale ya bar dakin kafin asirin shi ya Kai ga tonuwa gabadaya. Wurin Baffah ya nufa su ka tattauna wani business in da ya ke Shirin farawa, Abbah Kam Bai ma gari.

Sai da akayi Sallan Magrib sannan ya koma ko da ya Isa Isha'i tayi ya sa ya tsaya yayi Sallah sannan ya karasa dakin da aka yi admitting in nata.

Ko da ya Isa Ammah da Yusrah na Shirin komawa gida, Hamza zai Mai da su. Shahida da Fatima ne za su kwana wurin ta.

Su na tafiya Shahida ta fita haraban asibitin Wai za ta yo kallo, ni ko nace Anya kuwa?

Zaune ta ke Kan sallaya ta idar da Sallah tana tasbihi yayi Sallama ya shiga Fateema na gefen ta zaune akan plastic chair.

Bakaken ledan da ya shigo da su ya ajiye kan fridge in dakin, Fateema na ganin Shi ta Mike ta koma Kan gado ta bashi kujeran. "Thank you Amarya, ya jinya" amsa mishi tayi sannan ya dan fara Jan ta da hira ya na tambayan mijin nata kafin Zahrau ta gama tasbihi.

Kiran mijin na ta ya shigo wayanta, da ma ta fuskanci Aliyu na bukatar magana da Zahrau n hakan ya sa ta fita waje kafin ta yi picking in call in.

"Sannu Diva ya jikin?"

Kallo ta bishi dashi galala sannan ta tabe baki "Am alive" ta bashi amsa.

Wani murmushi ya saki da ya Kara fiddo ma ta da kyaun mijin na ta sosai "am sorry please, tuba na ke" ya fada Yana hadda hanayen shi alamun neman afuwa.

"Hmmmm" kawai ta ce.

"Kinsan me? Ke fa Kika ja ni Kuma I never thought abin zai Kai da haka, infact na zata ki daina damuwa da nine"

"To ni me nace?" Ta fadi tana kokarin fiddo wayan ta.

Taso yayi ya karaso inda ta ke hade da karban wayan na ta ba musu ta sakan Mai. Sai ranar ta yadda tayi missing in shi, hannayen su kawai da su ka gogi juna ya tabbatar ma ta da hakan.

"I miss you" ya fadi Yana kokarin jawo ta jikin shi. Kasa mishi musu tayi saboda wani irin kewan kwanciya a jikin shi da taji tana yi.

"Sorry my Diva kinji?" Ya fada Yana shafa Kan fuskan ta kafin ya koma Kan cikin ta Yana shafawa, "ya babynmu, ya fara motsi"

Turo baki tayi tace "you don't even care to know ai, hadda blocking Ina kayi a WhatsApp da Kar inga hotunan Yan matan da za ka daura right?"

Tsaro idanuwa yayi "waya fada Miki? Kishi ko? Haushi Kika bani, sai nayi tunanin in na horar da ke ta hakan za ki yadda ko 2 days ki Zo ki min a Abuja"

"Hubbie ba fa kin zuwa nayi ba, Karatu ne ya min yawa Kuma na sanar da Kai mun kusa fara exams"

"Da karatu da aure wanne ya fi mahimmanci, haba Fatima ni fa ba dutse bane, I've feelings. To Bari ma in fada Miki gsky, I almost fall on a lady trap Allah ne ya kare ni" Saurin janye jikin ta tayi da gare shi ta ja baya.

"Me kake nufi, Zina?"

  Hade Rai yayi ya Sha mur "nace Miki nayi? Kuma ma da ya afkuwa ai woh hadda laifin ki"

"To Kai me ya hana ka zuwa" ta bukata.

"I've no chance, yanzu ma taking risk nayi, tun dazu Ma Umar ke Kira na sai da na fada musu halin da ake ciki sannan su kace za su San abin yi"

"Ni dai to Kar ka Kara min haka"

  "Sorry my lady ba zai Kara faruwa" sun Dade suna hira game da kokarin nuna wa juna yanda su kayi kewan kasancew tare, sai da Shahida ta shigo dakin tukunna ya musu sallama ya wuce gida.

Washegari da sassafe yayi samakkon zuwa asibitin, dole ranar zai koma saboda uzurin sa, sun dan Jima suna tattaunawa kaman Kar ya wuce haka ya daure ya koma.

Zahrau ko abinda ya fada Mata gabadaya ya tadar Mata da hankali, tsoron ta Daya Kar Matan Nan na bariki ma rasa kunya da tsoron Allah su yi nasaran kwace Mata miji, shikenan fa ta shiga uku ta lallace.

A ranar aka sallameta su ka koma gida, Allah Allah ta ke su gama Exams ta koma gida saboda gudun samun matsala, duk bayan awanni sai ta Kira shi duk Wai dan gudun samun matsala, abin ba daganan ya ke ba Hajiya Zahrau.

                           "

  A daddafe ta gama Exams in, kwana biyu ba ta Kara ba tayi wa Abuja tsinke, sai da ta tabbatar da mijin ta ba da wani alaka da wata tukunna hankalin ta ya kwanta coz ya tabbatar da kewan ta da yayi.

Cikin ta ko ya tsufa sosai, tafiya ma da kyar ta ke, 1 week to EDD inta Nanah ta haihu su ka je Kaduna suna daganan ya karasa da ita Zaria coz can su ka shirya za ta haihu da ma.

Actually the book has come to an end...

Vote, share, comment and comments. It matters to me please.

Nagode.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top