KHF 48

Kwanan ta biyu a asibitin aka sallameta a asibitin kaman yanda likitan ya fada, Nanah ce kwana da ita Anty Amina Kuma ta wuni, Aliyu ya so su barshi yayi jinyan ta da kanshi fir abokan su kaki, acewar su sai dai kace ba a tare dole ya sa ya hakura Kar su ji wani iri ganin Kara su ke son mishi.

Ba laifi ta warware sai dai Kuma cikin na matukar wahalar da ita, tuni ya Kira ya fada a gida gudun samun matsala, Ammah da Mami dai tunanin su daya Allah ya sa ba irin laulayin Mahaifiyar ta za tayi ba. Abbah da Baffah ko musamman su kazo har asibitin su ka duba ta tare da Hamza, Deedat, Shaheeda da Yusrah.

Aliyu ya nemi su bar mishi Shaheeda da Yusrah su zauna dasu saboda condition in Zahraun, akwai abun ya zo dai dai, Shahida ta gama secondary school ta na jiran admission, Yusrah Kuma ta gama junior secondary sai dai ita Nan da 3 weeks za ta koma SS1, ba musu Abban ya amince kasancewar shi ma ya na matukar tausaya Mata, Deedat aka yi Akan zai kawo musu kayan nasu da ke Yana yawan shigowa Abujan.

Tarairayan da Aliyu yake was Zahrau ya linka na baya sosai, wani irin tausayin ta ya ke ji ganin irin wahalan da ta ke Sha komai ta ja tana bukata Nan da nan zai yi kokarin yi Mata wani abun ma ba sai ta fada ba sai aukin bacci kace kassa.

Yau ma hakan ce ta kasance da kyar ya tashe ta tayi Sallan Asuba ta koma, sun yi da ita ranar za ta cigaba da zuwa asibiti amma shiru kake ji ba alamun za ta tashi, da ke ma bai fi 2 months ya rage musu su gama IT in ba gabadaya ma.

Hura Mata iska yayi a kunnen ta ko za ta tashi, dabarun da ya dinga yi sun fi a kirga Amma duk a banza coz ba Wanda yayi aiki Amma wannan in da alamun zai yi tunda har ta fara motsi da idanuwan ta. Yana bin ta a hankali sbd Bai so ta tashi a firgice ga situation in da ta ke ciki, gabadaya gani ya ke shi ya ja Mata komai na wahala da ta ke Sha tunda ajiyan shi ne a cikin na ta. Iskan ya Kara hura mata, a hankali ta fara motsi da idanuwan ta har sai da suka bude gabadaya, Murmushi ta sakan mishi immediately her gaze fall on him "Morning Hubbie" ta fada da muryar baccin da bai gama sakin ta ba.

"Morning Diva ba Zaki Hospital in bane?"

Kwalalo ido tayi "am i late?"

Girgiza ma ta Kai yayi "you can make it, kawai ki tashi"

Da sauri ko ta Mike tayi azaman shiga wanka, tun Yana jiranta har ya fara tunanin lfy? Ko da ya bude toilet in samun ta yayi tana ta bacci a cikin bath tub in, sakin baki yayi Yana Kallon ikon Allah dai dai Nan ko ta tashi tana mitsika ido "kinsan me? Kawai ki hakura Zan yi reporting case inki" ki tayi a dole ya taimaka Mata ta shirya ya sauke ta.

Kullum ko sai ta je Amma ba amfani, is either tana bacci ko Kuma ba ta Jin dadin jikin ta ta kasa yin komai gashi har yanzu ba wai ta daina Aman gabadaya bane, Daga karshe dole ya sa ya Mata Jan ido ta hakura da maganan asibitin kwata kwata.

Satin su Shaheeda Uku ya ce zai maida Yusrah saboda makaranta taso ta ce zata bishi Amma rashin ganin fuska ya sa ta kasa yin hakan, kwana biyu yayi daga ita sai Shahida a gidan Dan ma suna dasawa har labarin saurayin ta take Bata Wanda ya ke residing a Abuja daga karshe ma har gidan ya Zo gaida Zahrau Amma fa Aliyu na Zaria lokacin.

"Shahida babba ne fa, he looks responsible aure za kiyi ne soon?" Ba kunya ta gyade kanta "Anty Ina son shi fa sosai Kuma ya ce min Yana so yayi settling soon, Maman shi ta dame shi da maganar aure Kuma ni Kinga ban son na rasa shi".

"Abin na ki da gaske ne, Wai ma Ina kuka hadu dashi?" Zahrau ta tambaya.

"A kano da na je wurin Anty Zee, Neighbors insu ne"

"Abbah zai barki Shaheeda? Ki Bari ki fara schl Mana to sai ku taso da maganar"

"Haka na fada Mai Nima"

"Ma Sha Allah Allah ya tabbatar Mana da alkhairi"

"Ameen" Shahida ta amsa sannan su ka cigaba da kitson da suke yi bayan sun dasa sabuwan hira.

     Cikin jikin Zahrau na wata Uku ta warware gabadaya, ba ta da wani matsala in ba kwadayi ba mijin ta ko ya tsare ma ta wannan sai Kara shagwaba ta ya ke yi, tayi fari tayi kiba tayi kyau abinta Ma Sha Allah.

Wata ta Kama December, A lokacin su ka tafi Zaria bikin Ya Deedat. Lokacin kuma yayi dai dai da fara registration in su na shiga Level Four, waya ga su Zahrau a final year.

Shi dai gogan na ta ba wai Yana son komawa school in da za tayi bane saboda shi zaman shi ba zai yiwu a Abuja kaman yanda dole ta zauna a Zaria gashi final year balle ya fara maganan transfer, Dan ba yanda xai yi ne Amma da makarantar ma barin shi za tayi tunda dai Allah ya hore mishi Kuma ya tsare Mata komai. Hmmmm ni dai nace ko waya fada wa maza amfanin karatun mace Dan Wanda za ta aura Bai dashi ne? Allah dai ya kyauta Mana kawai.

Hamza ya sa ya mata registration in, anyi biki angama har ma da na Sumayya Amma Kuma ba su koma ba Saboda shi ma Yana hutun karshen shekara, Kiri Kiri ya Hana ta komawa sai bayan New year.

Budewan school insu yayi dai dai da komawan aikin shi, Lokacin cikin ta ya fara fitowa Dan ma ba Mai tsinin ciki bace.

Tana hada kayan da zata koma samarun da su ya shigo daki ya same ta, Zama yayi a hankali kusa da ita jikin shi duk yayi sanyi "Diva yanzu ba za ki Zo mu koma Abujan ba?"

Juyowa tayi dan ta ga gskyn abinda ya ke fadi aiko ba ta ga alamun karya ba a fuskan shi "So kake in bar makarantan ne?" Ta fada with a shaky voice, kafin ya Kara wani har ta fara hawaye "shknn tunda ba kason cigaba na na hakura ba Zan koma ba" wullar da kayan hannun ta tayi ta fita ta bar mishi dakin.

  Bin ta yayi da kallo a fili ya ambata "Daga magana" girgiza Kai kawai yayi shi ma ya fita masallaci domin Sallan Azahar.

Ba shi ya koma gidan ba har sai bayan la'asar, a falo ya iske ta tana Kallon Korean series. Yana sallama ta taho da gudu ta rungume shi tana Mai sannu da zuwa, saurin ture ta yayi ta dago tana Kallon shi cike da mamaki, kunnen ta ya Kama a hankali ya ciza ta saki Kara "ba na hana ki gudu ba wai"

"Sorry sir" ta fadi tana murmushi.

Mamakin saurin saukowan ta ya ke ita ko dama ba tayi da wani manufacturer bane sai dan Kar ya Kara Mata maganan komawa Abujan don tsaf ta San zai iya dagewa Kuma shikenan karatun da ta Dade tana yi ya tashi a banza, shiyasa Nan da nan ta nuna mishi baccin ranta.

"Kin daina fushin kenan" ya tmby.

Girgiza Kai tayi "Ba a fushi da hubbie, shine kaki dawo wa tun dazu ko?"

"Na dauka ba ki son ganina ne ai yanzu ma shahada nayi na taho"

"Wa ya gaya maka akwai San da ban son ganin ka, mu je kaci abinci" ta karasa tana Jan hannun shi.

Washegari da Yamma ya maida makarantan bayan ta je ta yi ma su Ammah sallama duk sun Mata fatan alkhairi. Sun fi 30 minutes a mota su na jimamin rabuwa fa juna, wani irin sabo su kayi na ban mamaki kowa ya San zai ji jiki in har ya rabu da Dan uwana shi.

Sai da Fateema ta Kira ta tana tambayan lfy ta jita shiru da ke ita since ta iso daga Kano. "Hubbie ya kamata ka tafi Kar dare ya maka a hanya"

"Au Kora na ma kike yi kenan Koh"

"Lah Wlh ba haka bane Naga yamma nayi kenan"

"Shknn bara na wuce inda ake nema na"

"Ni dai bance komai ba"

"Nima ai bance kin fada ba"

A tare su ka fita daga motan ya bude Mata boot "wa zai shigan Miki da kayan"

"Ina zuwa" ciki ta shiga ba dadewa su ka fito da Fateema da wasu yara.

Yaran su ka shigan Mata da kayan, Fateema ko su ka tsaya gaisawa da Aliyu.

Gaishe shi tayi cikin sakewan fuska ya amsa "lafiya kalau Amarya, an iso lfy".

Mamakin da Fateema ta shiga kasa boyuwa yayi a fuskan ta, she can't believe Aliyu ke Mata magana cikin raha har da wasa.

"Lfy kalau, mun same ku lfy?"

"Kalau, ya kanon na KU ne" hira ya ta janta dashi sosai ta ke mamakin abun, ni Kam nace mamaki ma tukunna fati.

"Bara in wuce ina Kan hanya" ya fadi ya na duba agogon hannun shi.

"To Allah ya kiyaye hanya"

"Ameen nagode Amarya ga Kuma amanar tawa Amaryar Kar wani Abu ya taba min ita" murmushi kawai tayi.

"In ba Hakan ba Kuma" ya cigaba "Angon Nan na ki barrister Zan sa a kama"

"Lallai muna da zaman kotu Ashe"

"Ahhhh rufa min asiri" ciki ta shiga ta Basu wuri suyi sallama

"To Diva ba ra na je ko" daga Mata gira yayi Yana Kallon cikin idon ta itama in shi ta ke kallo cike da so da kauna kaman su tsaya a haka su yita Kallon juna.

"Ka tafi hubbie" ta fadi tana kokarin janye hannuwan ta daga cikin nashi.

"Ehmm" ya amsa, sunkuyo da kanshi yayi yayi perking inta a cheeks "Take care of yourself for me" hannu ya Kai Kan cikin ta ya shafa "and our baby" daga mishi Kai kawai tayi ya shiga mota sai da yayi reverse sannan ya dago Mata hannu ita ma hannun ta dago mishi tana Kallon motar shi har sai da ya bar layin, kaman ta daura hannu a Kai ta kurma ihu haka ta ke ji, jiki a salube ta lallaba ta shiga gida.

Sai da ta shiga jiki sannan Fateema ta lura da cikin da ke jikin ta Nan fa ta hau Mata tsiya tana kumbure kumbure kafin kace kwabo ta fashe da kuka, sakin baki tayi tana Kallon ta, ko Zahrau ta mance da yanzu ba tare da hubbie ta ke ba? Fahimtar hakan da tayi ne ya da tayi saurin share hawayen ta, Sai a sannan suka fara Hira Fateeman na fada Mata irin mamakin canzawan Aliyu da tayi, ba ta ga mamakin ba kuwa sai da taga wayan da suka yi yafi uku kafin ya Isa Abuja, bini bini zai Kira ta Yana tambayan ta ya take ita ma da taji shiru za ta Kira shi.

            3 weeks later.

Zuwa yanzu Fateema ta Saba da ganin kallan soyayyan Zahrau da Aliyu, Abu kadan ta ce Miki hubbie kaza, hubbie ya ce kaza komai dai hubbie har tsiya ta ke Mata tayi tayi auren ta yayi ta ji abinda ake ji in anyi aure, rasa baki magana Fateema ke yi ganin yanda Aliyu gabadaya ya canja Mata kawa kamar ba Zahrau da ta sani ba tun suna JSS1.

A Rana za suyi waya yafi sau uku a haka kullum Yana cikin bata hakurin aiki ya mishi yawa, video call ko in su ka fara har mantawa Fateema ke yi da suna wayan. Rayuwa juyi juyi kenan a sati ukun sau biyu yazo ganin Zahrau a cewan shi sai bikin fateeman zai Zo su tafi. Ai ko haka aka yi suna samun hutun mid semester ya Zo ya tafi da su Kano tare da Amaryan gabadaya. A hanya ya ke sanar Mata ranar a ka sa auren Shahida, ta Mata murna ganin cewa burin Yar uwar na ta ya cika, Amarya dai ta ga soyyaya kala kala kafin aka karasa Kano.

Ta so sauka gidan su Fateeman kawai Sam ya ki yarda a cewar shi gidan sha'ani cike ya ke da jama'a ita ko tana cikin situation in da bata son takura don haka suna sauke Fateema ya wuce da ita gidan Anty zee.

Ummiy ta so ta sauka gidan ta Amma fir ya ki "yaushe Ummiy tayi hankalin Kula kin da ke Diva ba zai yiwu ba ki dai je ki wuni Mata" ita Kam Kallon mamaki ta bishi dashi coz Ummiyn ma ta haihu already.

Dole su ka hakura sai dai ta je mata wuni, a gidan Anty zee ta zauna har aka kare bikin fateeman Nan Kano aka Kai ta Sokoto road, daurin aure kawai ya jira sannan ya koma Abuja straight.

Satin ta Daya da kwana uku a kano ya Aiko Hamza ya maida ta Zaria, hutun su saura kwana biyu a koma Amma ya matsa Mata sai tazo Abuja fir ta ki, a ganin ta final year ta ke so she have to focus, ga project Kuma da ya taso ta a gaba Dan ma Yaya Deedat na taimaka Mata sosai.

Sai dai me? tun ranar da ya Mata maganan zuwa Abuja ta ki yayi fushi Bai Kara Kiran ta ba sai dai in ita ta Kira shi, shima iyaka ya tambayeta ya take ba sa wani hiran kirki zai kashe a cewar shi akwai aikin da zai yi. Tun abun Bai damun ta har ya fara a haka su ka koma schl ya Deedat ke kaita ya dauko ta wata Rana Hamza da ke Fateema ba ta dawo ba tukun.

Gida duk ya Mata kunci ta rasa Ina za ta sa kanta a haka Fateema ta dawo schl, tuni ta hada kayan ta tawa samaru diran mikiya, karatu su ke sosai hakan ya sa ta rage damuwan abinda Aliyu ke mata.

Abu kaman wasa daga kwananki ya koma satuka daga Nan Kuma ya koma watanni kusa wata na uku kenan, gashi tayi nauyi sosai, still dai ba ta hakura ba tana Kiran shi shi ko a sati Bai fi sau biyu zuwa uku ba.

Ranar kaman ance Mata kunna data ta ganshi online a WhatsApp Daman kullum ce Mata ya ke aiki ya sa shi gaba in ta Kira shi, magana ta mishi yayi banza da ita karshe ma da ta ishe shi yayi blocking inta.

Bin wayan ta ke da kallo unbelievable, Nan da nan ta fara zufa ta Kira shi a waya "hubbie blocking Ina kayi?"

Kai tsaye ya amsa ma ta da eh, sakin wayan ta ya fadi kasa yayi dai Daya, kafin kace Mai numfashin ta ya fara kokarin daukewa da gudu Fateema ta yi kanta ta na neman agaji. Ina tuni ta Suma, neighbor insu da ke da mota ta taimaka aka Kai ta ABUTH emergency su ka wuce da ita direct. Da kyar Fateema ta lalubo wayan ta ta Kira Aliyun ta fada mishi halin da ake ciki...

Hmmmmmmmmmmm...

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top