KHF 47
Yau ta riga shi dawowa gida da wuri, driver ya sa ma ya je ya dauko ta.
Gabadaya ba ta Jin dadin jikin ta, tafiya ma da kyar ta ke saboda ko motsa jiki Mai kyau ba ta son you. A daddafe ma ta samu ta yi Sallah, tana idar wa ko hijab ka sa cirewa tayi ta kwanta a wurin, ba wani dadewa tayi a asibitin ba Amma Kuma ta Sha wahala saboda ranar supervisor inta ya Zo ganin ta. Wani azzababben ciwon Kai ke damun ta duk a zaton ta na gajiya ne shiyasa ma ta ke so ta samu bacci ga uban yunwa da ke kwakulan cikin ta Amma ba za ma ta iya tashi ta yi girki ba.
Da kyar ta samu wani bacci Mai nauyi ya dauke ta ba ita ta farka sai da aka Kira La'asar, sai dai Kuma ciwon kan Nan ya na Nan ba inda ya je sai ma Kuma rawar dari da ta fara, Baiwar Allah tunanin ta Daya Aliyu in ya dawo ba ta tanadar mishi komai ba ba zai ji Dadi ba, wayanta ta lalubo ta Kira shi dab da za su shiga wani meeting akan wani tarzoma da su ke so su kwantar a wani jaha cikin south Africa, ana son za a tura su wurin na one week, har yayi tunanin ya bari in sun fito ya Kira ta saboda ana jiran su sai Kuma zuciyan shi ta yi preferring akasin hakan, saurin daukan wayan yayi
"hello hubbie" ta fadi kasa kasa.
"Diva ya akayi?"
"Nace ba please in za ka dawo ko za ka saman Mana abinci a wani wuri, banji Dadi ba Zan iya ba" ba ma sai ta fada ba muryar ta kadai ya tabbatar mishi da bata Jin Dadi.
"Subhanallah sannu kinji, me ke damun ki?" A rude yayi maganan
"Ciwon Kai ne" ta amsa a sanyaye
"Sorry gashi Kuma ba yanzu Zan dawo ba Kar ki zauna da yunwa ba ra in Kira driver ya samo Miki yanzu ko"
Shiru tayi saboda maganan ma da kyar ta ke yi, ita ba ta yunwa ta ke ba Daman shi ta ke ji.
"Diva ko in ce ma Umar ya turo Miki Nanah ne"
"A a ka barta kawai" ta amsa sannan ta katse wayan.
Kokarin Kiran ta yake yi yaji ana mishi magana ya shigo. Ba musu ya shiga Amma kusa da Umar ya nema a hankali ya fada mishi abinda ya ke so ta yanda su biyu kawai za su ji.
SMS Umar ya tura wa Nanahn kawai.
Haka ta daure da kyar ta Mike ta yiyo alwala Sallan ma dole a zaune ta yi shi saboda jirin da ta ke ji yana diban ta inta tsaya, kafin kace kabo gabadaya jikin ta ya rufe da zazzafan zazzabi sai karkarwa ta ke yi, hakuren ta har hadewa ya ke sai Kuma numfashin ta ya fara kokarin daukewa ganin abun bana kare bane ya sa ta fara kokarin Jan jiki ta lalubo wayanta. Kusan 3 missed call ta Mai Amma shiru kake ji.
Ta Kai mintu goma a hakan da kyar ta dinga struggling da numfashin ta a hakan ta tsinkayi Sallama a kofan first parlor insu an ya Kai sau uku ba ta da karfi da za ta iya amsa.
Karasowa ciki Nana tayi Jin shiru ya sa direct ta nufi dakin Zahraun, da gudu ta karasa gunta ganin yanda ta ke, gam Nanahn ta ririketa tana Jan numfashi, tsorta Nanahn tayi Jin jikin ta ma yayi zafi kaman wuta gashi jikin ta sai rawa ya ke.
Rasa ma abin yi tayi kawai ta dauko wayan ta ta dinga Kiran Umar shiru Bai dauka ba ta dauki wayan Zahrau ma ta dinga Kiran Aliyu still dai ba response gashi Zahrau sai Kara jigata ta ke wani tunani ya fado Mata da sauri ta yi dialling numban Maman khalipha "hello Anty Amina please in kina gida ki Zo Zahrau ba lafiya sosai" a gaggauce ta fadi maganan.
Ba ta iya Jin abinda ta ke fada daga dayan bangaren ba illa kawai "gani Nan zuwa" da ta jiyo ta yi ending call in.
Mintuna goma cikaku basu yi ba Maman khalipha ta shigo gidan a rude "Subhanallah Nanah ya Kika barta haka oya maza kiga" rikota tayi ta dayan side in Nanah ta talloba ta ita ma, Allah ya so da hijabi a jikin ta takalmi kawai su ka sa Mata su ka karasa da ita mota.
Da sauri Anty Aminan ke driving har su ka Isa asibitin su ma suna hanin condition inta su ka wuce da ita Emergency.
Sun samu sun daidaita numfashin na ta har ta samu bacci, two hours tayi ta na bacci an sa Mata drip Dr yayi suggesting a sa ma Mata abu Mai ruwa ruwa ta ci ko da su ka tmby ta kunu kawai tace za ta iya Sha, gabadaya Bata da appetite, Anty Amina ta sa aka kawo da ga gidan ta, ta dan Sha da dama sannan ta Sha magani zazzabi da ke jikin ta ya dan sassauta sai dai ciwon Kai. Tana gama Shan magani ta nemi ruwa ba musu Nanah ta Mika Mata ai ko tana gama Shan ruwa ta amayo komai da ke cikin ta, Nan take gabadaya ta galabaita.
Dai dai lokacin Aliyu, Umar da Salim su ka shiga sun lokacin an idar da Sallan Asuba.
Sannu su ka dinga Mata da Kai ta iya amsa musu ba karamin Jin jiki ta ke ba, kasa jurewa Aliyu yayi ya karasa wurin nata har Kan gadon ya hau ya riko hannun ta "Diva me ya faru?" Kanta nuna mishi, fahimtan da yayi ba za ta iya magana ba yasa ya juyar da tambayan shi wurin su Nanah. Nanar ce ta mishi bayanin komai ta fada mishi tana ta Kiran su basu dauka ba "mun shiga meeting ne, Ina doctor in?"
"Ya fita, sun dauki jinin ta Wai za su Mata test"
"Okay bara na ganshi" ya ce sannan ya fita dakin.
Nurse ya haduwa da za ta shigo dakin da magunguna, dakatar da ita yayi ya tambayeta Dr ta mishi kwatancen office in shi.
Knocking office in yayi aka bashi izinin shiga, Murmushi doctor in yayi sannan ya nuna mishi wurin Zama "Bismillah" ya ce sannan ya Mika mishi hannu su ka gaisa.
"How may i help?"
"Am here about the case of ur patient, Fateema maitama"
"Are you her husband?" Nodding Kai yayi
"Ma Sha Allah, perfect couples"
"Thank you"
"My pleasure, you know am just working on her case and planning on coming to the room after am done but its good that you are here"
Shiru Aliyu yayi Yana sauraran shi "Your wife is pregnant Mr Aliyu right?" Bude baki Aliyu yayi Yana Kallon shi cike da mamaki, happiness is written all over his face.
"So congratulations" Doctor in ya Kara fadi, murmushi kawai Aliyu ya ke yi ya ma kasa rufe baki balle yayi ma doctor in magana.
"Normally kasan Mata kala kala ne kowacce da irin laulayinta so ita nata naturally haka yake za ta dinga Sha wahala. Frankly speaking we can't do anything to avoid it totally but we will try, akwai magungunan da za mu Mata prescribing more expecially na Hana amai da Kuma na zazzabi da sauransu, sai Kuma matsalan daukewan numfashi inaga wannan due to ciwon ta ne na asali coz a tests In da muka mata mun gano tana dauke da matsalan heart, sai Kuma treatment in BP da muke ganin ya kamata a daura ta a Kai kasan normally masu ciki suna fama da matsalan so sai ana hadawa da medical checkup before ta Kai time in da zata fara antenatal. Kuma za mu dan riketa zuwa gobe ko jibi haka saboda ta dan samu karfi, ehmmm ta dinga cin abinci masu gina jiki Kuma"
"To Likita mun gode sosai Kuma in Sha Allah za mu kiyaye" Aliyu ya amsa.
Ko da ya shiga dakin samun ta yayi ta na amai gabadaya ta galabaita, duk wani iri yaji da sauri ya karasa gurinta yana Mata sannu tana gama Aman ta samu bacci.
"Oh wannan ciwo lafiya ko Mai ta Sha sai ta amayo" Anty Amina tayi maganan duk da dai tana zargi.
"Gsky kam ba na lafiya ba, me doctor ya ce maka yana damun ta?" Salim yayi tambayar yana Kallon Aliyu.
"She is pregnant" ya amsa mishi.
"Ma Sha Allah" kusan a tare su ka fada.
Poor Zahra
Who is happy?
Well, am planning on ending the book before my upcoming exams...
Thanks for your support
Don't forget to Vote, comments and share. Ur motivation is all i need Dearies.
Okay, let me ask you this. is my book interesting? Please let me know in akwai wani gyara da ku ke ganin ya kamata ayi, this is just a trial and am planning on writing some more stories.
Nagode.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top