KHF 46
Kallo ta bi dashi cike da mamakin abinda ya Zo ma ta dashi, shawaranta fa ya ke nema gsky she can't believe it. "Ke fa na ke saurare ya tunasar da ita"
"Why not ka raba kudin Kashi uku" ta fada tana Kallon reaction in shi.
"Wai miye kike ta kallo na"
"Allah hubbie ba zan boye maka ba ko am suprise ne"
"Why are you suprise"
"Wasu mazan fa ko da wasa ba sa Bari Matan su su San karuwan su fa ballan tana Kuma neman shawarar su"
Murmushi ya saki sannan ya ce "kin San me?" Girgiza mishi Kai tayi.
"We are building a family so Dole na yi shawara da ke domin duk abinda ya same ni ya same ki ne ke da Ya'ya'n da Zaki haifa min" ajiyan zuciya ya yi ita ko ta yi jim tana Kallon shi "so Dole ke ce abokiyar shawara ta" ya cigaba "Its our benefit ko ha Haka ba"
"Hakane" ta amsa
"So stop wondering Ina jinki"
"Ehmm as i was saying ka raba Kashi uku, Daya business za a nema a fara komai a rayuwa ya na bukatar plan sbd gaba are hangowa ba yanzu ba, profit a bude separate account a dinga tarawa believe me tym in da nauyin yara zai hau kanmu za suyi amfani wurin bukatun yaran". Gyade Kai yayi sannan yace "shawarar na yayi Fateema Kuma hakan zai sa mu ga riban kudin da muke tarawan Nan gaba"
"Yauwa toh na biyun Kuma gidan marayu, asibitoci da prisons ya kamata akai taimako, ka San ance abinda ka ba ma wani shine na ka ranar lahira mu tunda Allah ya hore Mana sai mu taimaka musu, you have no idea wani irin ceton rai za kayi hubbie hakan zai Kara maka cigaban rayuwa ma gabadaya"
"Gsky kina da tunani me kyau shi fa ya sa aka ce shawarar Mata abun dubawa ne, wannan Abu ne Mai kyau da yakama ta na fara tun tuni but Kinga kwata kwata na shagala, don in kin banni kadara Zan siya da kudaden Nan wlh Ashe alkhairi ya sa nazo neman shawara gunki". Murmushin alfarma ta saki "hakane hubbie Daman Dan Adam Yana bukatar tunatarwa a koda yaushe shi ma ya sa shawaran ke da kyau ai"
"Na ukun fa hajiyata?" Hararan shi tayi sannan ta hade Rai "na tsufa ne da za ka ce min Hajiya"
"Au sai ka tsufa ake ce ma hakan?"
"To ba Babban Mata ake cewa haka ba" ta fada cike da shagwaba.
"To sorry my baby"
Tabe baki tayi "sai dai kace wata Yar tsana"
Girgiza Kai yayi Yana fadin "Diva ba ki dai da dama"
"Toh ka baza ka bani hakuri ba?" Ta fadi hade da turo bakin na ta da ya riga ya zame ma ta jiki.
"Ke dai wlh Yar rigima ce Kuma ki maida bakin Nan naki kafin in yi maganin shi" ba shiri ta koma ta saki fuska don ta San hali yanzu ya saka ta a wani hali na tunani...
"Yauwa ka na ji ba su Ammi da Abbah za ka yiwa amfani dashi, they will proud and za su sa ma ka albarka ka San addu'an iyaye Kan ya'yan'su"
"Diva me su Abbah su ke bukata, Alhmdlh Allah ya hore musu komai" ya fada cike da mamaki.
Girgiza Kai tayi sannan ta fahimce shi sosai "Aa Hubbie hakin su ne ko suna dashi ya kamata ka sauke, Abu ne ma da ya kamata ko da ko Allah ya hore mu su ba ma su kadai ba har ma sauran family members in akwai kyautatawa ko Dan a karfafa zumunci"
Ajiyan zuciya yayi "Shawaran ki yayi Diva sosai na ji dadin shi, Allah ya Kara kaifin basira, ya bar Miki ni, ya bamu ya'ya' masu albarka"
"Ameen" ta fadi tana dariya hade da rufe idanuwan ta.
"Wai ke fa da gaske kunya ta kike ji ko?" Gyade mishi Kai tayi still idonta a rufe tana sunne Kai kasa.
Shaking head in shi yayi sannan ya ce "You are not serious Allah, Allah ya shirya min ke, haka yaran za su Zo ana Jin kunyan babansu?"
Tsuke baki tayi sannan tace "yanda fa kake maganan yaran Nan sai kace gobe xa su xo gabadaya"
"Indai da rai da lfy ai abin kaman gobe ne ke dai kawai ki rokon Mana Allah masu albarka, ko baki son su ne?" Da sauri ta dago Kai ta kalle shi cike da mamaki.
"Ai naga kaman ba ki damu ba ne saboda reactions inki in nayi maganan su"
"With time" ta fada tana lumshe ido sannan ta kwantar da kanta Kan cinyan shi.
Gashin kanta da ya Sha kitso ya fara shafawa zuwa fuskan ta. Firgigit, kaman ya tuno abu ya tsaya "keh kinsan me?"
"No no no" ta amsa kasa kasa
"Ba ki taba ce min kina Sona ba"
"Kai hubbie mana"
"Bawani yarinya na ki wayan sai kin fada min"
"Allah hubbie fa ranar fa na fada maka a Zaria" ta fadi cike da shagwaba.
"Ba da bakin ki ka fada ba ni Kuma so nake na ji kin furta so can you please save us and say it?"
"Hubieeeee" ta fada tana Jan sunan.
"Kinga dagani ni tunda ba Zaki fada ba inda abin yi" mikewa yayi ya daure fuska ya fada feigning hurt.
"Ni fa bance ma ka Bazan fada ba"
Tabe baki yayi hade da shrugging shoulders in shi "as you wish"
"To ka zauna Mana hubbie sai in fada"
"Ni Zaki Bata min lokaci" tafiya ya fara yi.
Taku Daya biyu yayi na uku sai Jin mutum yayi a baya shi, rungume shi kankam ta yi, a hankali ta fada "I love you very much hubbie, Ina son ka sosai" da sauri ya juyo da ita ta gaba suna fuskan tan juna. For the first time ta yi juriyan hada ido dashi, a idon nashi ta gama karantar komai game da ita ba ta da haufi akan son da hubbien nata ya ke Mata, "are you sure?"
Ya fada Yana Kallon cikin idon ta still yayin da su ke kokarin aikawa junan su sakonni. Kai ta gyade mishi, at that moment zuciyoyin su sun gama aminta da kaunar junansu da ya riga ya fito baro baro, jinta su ke a kowani Bari na jikin su yana yawo, there is no doubt ba za su iya rayuwa ba tare da juna ba, Daman can they are created for each other kawai akasin fahimta ne.
"Ina sonki fiye da tunaninki Fateema" ya fada kafin ya rungume ta Kam Kam "You are such a blessing in my life Diva"
"I love you more than you love me hubbie, in ba Kai ba sai rijiya, I can't do without you"
"Ehm ehm haka matar tawa ta iya kalamai? Kar ki damu ba Zaki fada rijiyan ba ma am already yours remember?"
Gyade Kai tayi ta boye fuskan ta a kirjin shi cike da kunya dan ba ta ma San ta fadi maganan ba sai da ya fito ta iya releasing.
"Haba Yar soyayya ta wani Kuma kunya bayan an gama kashe ni da kalamai, come on be free am ur husband"
Dago fuskan ta ya fara kokarin yi tana noke wa da kyar ya rabo fuskan da kirjin shi Yana Kallon ta Amma ta rufe ido kyam kyam, lips in Shi ya Kai Kan idon nata yayi pecking insu a hankali har ya gangaro Kan lips inta.
Light fades
8:30 pm dai dai ya dauko ta daga gidan Maman khalipha, yau a can su ka wunin ma ta ita da Nanah, coincidence har fareeda ma ta je ranar ai sun Sha hira.
Tare su ka je daukan su shi da Umar Amma kowa a motan su, wani aiki su kayi tun safe sai Daren su ka samu suka gama, ko da su ka Isa fareeda har ta tafi while Zahrau ko har ta yi bacci.
Still sai da su ka taba hira da Salim kaman ba tare su ka wuni ba sannan su ka Mike. Da kyar Maman khalipha ta taso ta tsabagen baccin da ke idon ta.
Gyangyadi kawai ta ke har su na karasa motan da kyar "Diva Wai lafiyan ki? Wannan wani irin bacci ne"
Hamma tayi sannan ta kalle shi "ni fa kaina har ciwo ya ke ka tashe ni in mun isa Gida" wani hamman ta Kara yi ko kafin ya Kara magana har ta koma baccin ta, da suka isa Gida ma da kyar ya samu ta tashi sai da ya rungume ta a jikin shi tukun su ka shiga gida.
"Ni Kam Allah wani baccin na ke ji hubbie bara in shiga sai kazo" carab ya riko hannun ta "ba ki Isa ba Allah hira za muyi" make kafada tayi.
"See what i buy for yo.." ko kafin ya karasa maganan ta yi wuf ta kwace roban ice cream in da ke hannun shi.
"Hey ba kwace wa zanyi ba so calm down ki Sha a hankali Amma fa ki tsaya muyi hira"
Gyade Kai tayi ta dinga Shan ice cream in kaman an Aiko ta lbr ma ya ke Bata Amma hankalin ta Bai wurin.
Sai ta shanye tas sannan ta dago ta kalle shi "Hubbie ba wani" girgiza ma ta Kai yayi "Bbu Kuma ma dai kinsan Bazan barki ki Sha dayawa ba ko?" Turo baki tayi shi ko ya daure fuske gudun ta samu wurin yi mishi rigima, ya ma dauke Kai gabadaya.
Yayi mamaki da ya ji ba ta Kara complain ba ko kunkunai bai ji tayi ba, sai dai ko da ya juya mutuniyar ta shi ta dade da yin nisa. Murmushi kawai yayi ya kashe wutan Falon da TV gabadya, daukan jarirai ya Mata har daki Amma ko motsin kirki ma Bata yi ba.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top