KHF 44
Da sallama ya shigo Falon, da kyar ta iya amsa mishi tsabagen fushin da ta ke dashi. Harara ya maka Mata sannan ya ce "haka ake tarban miji?" Banzan tayi dashi "ki fa bi a hankali Dani fa" ya fada Yana murmushin mugun ta.
Tsabagen takaici ba ta San sanda hawaye masu zafi su ka sauko daga idon ta tun tana sheshekar kukan har ta saki kukan baki Daya. Sakin baki yayi Yana Kallon ta Bai taba sanin Zahrau yarinya ba ce sosai sai yau.
A hankali ya matsa kusa da ita ya jawo ta jikin shi Yana lallashi "sorry kinji"
"Ni dai kawai ka barni inje Dan Allah"
"Haba Fateema shin Wai baki ga baki da lafiya bane? Sorry Mana Allah za mu je ranar suna I promise"
Kara turo ba ki tayi tana fadin "ni dai gsky ka barni inje in ma ba za ka kaini ba Zan hau motan kasuwa"
"Allah ya tsare ba motan kasuwan da Zaki hau ma"
"Har fa maijiddah da ke Kano fa ta je ni ko tun ranar da aka yi haihuwan ban koma Kuma jibi suna" ta fada tana gunguni.
Bakin na ta da ta turo ya bi da kallo sai jin hannun shi tayi a Kan lips inta Yana shafawa "You know what? I love this" little pink cute lips in ta ya shafa, tuni ya kashe ma ta baki ta kasa magana, kullum da hakan ya ke cin galaba ana barin maganan tunda ya fahimci week point in nata.
Maganan kaduna kuwa kememe ya ki zancen tunda ya fahimci ba ta Jin dadin jikin ta saboda wani Dan guntun zazzabi da tayi gashi Kuma tana dan dingishi tun ranar. Bai ki kullum ya shigo ya ganta a gaban shi ba Tsabagen wani irin soyayyarta da kullum ya ke Kara shigan shi, ji yake in su ka fita wasu za su kalle ta ta birge su shi ko abinda ya ke gudu kenan, wani mahaukacin kishi gare shi dama tun asali, balle Kuma yanzu da ta zame mishi zinariya gani yake kaman yanda ba zai iya resisting kallon ta ba tare da tayi having effect on him ba wasu mazan ma haka ne.
Tarairaya kaman ta na Shan shi ba karya har wani murmurewa ta fara yi, ta Kara haske shiyasa ma ba ko yaushe ta ke taso da maganan zuwa kaduna ba Saboda salon Soyyayan shi da ke mantar da ita kowa da komai, Ita kanta ta shaida shi gwarzo ne wurin soyayya sai ka rantse a India ya taso, sai ko in Yan uwan na ta sun Kira ta suna tambayan Wai ba za ta zo bane sannan rigiman ke tashi.
Ranar ma dai haka tayi giving up sai ko da yamma da su ka kirata suna Mata tsiyan har sun ga tazo tuni ta rude Mai da kyar ya lallabata tare da alkawarin gobe zai kaita da sassafe. Sai Kuma ta tsiro wani rigiman wai sai dai ya barta ta kwana tunda washegari za ayi suna, fir ya ki karshe ma ya nuna ba ta baccin ranshi, hakanan ta hakura ganin chance in zuwa a ranar ma za ta rasa shi.
Sha biyun Rana ya sauke ta a kofan gidan maijiddah bayan sun je sun gaida Anty Rukayya.
Da sauri ta yi yunkurin bude kofan yayi saurin kamo hannun ta, sumbatar bayan hannun na ta yayi "ba sallama? Won't you miss me?"
A dole ta saki murmushi duk da fushin da take dashi ganin Irin Kallon kauna da ta ke bin shi dashi "Kai Unclee kullum fa muna tare" murde bakin ta yayi ta saki yar Kara "Allah ni dai ka takura ma bakina nikab ma Zan fara sa wa"
Hararan ta yayi "wa za ki sawa nikab? Kuma ma ai maganin ki kenan, I thought na hana wanna sunan right?"
"To ni me zan ce ma?"
"Oho ke za ki nema"
"Yaya Aliyu?"
Tsaki ya je sannan ya ce "Allah ya kyauta, Kar ma ki fara"
"To me kake so?"
"We will talk about it anjima in mun koma Zaria"
Murmushi ta saki sannan ta ce "can i go?"
Gyade ma ta Kai yayi "as you wish my dear"
Bude kofan tayi tana fadin "I will miss you for sure"
Tana fita ta juyo tana mishi waving hand Shi ma waving in ya Mata sannan ya ja motan ya tafi suna Kallon juna har ya bar layin ta na Kallon motar shi sannan ta juya za ta shiga gidan ai ko four eyes su ka yi da Nanah da Ummiy su na Kallon ta.
Wani irin kunya ta ji ya lullube ta Amma Kuma sai ta yi kokarin basarwa, dariya su ka kwashe dashi a tare "ki ce ga abinda ya Hana ki zuwa za ki wa zazzabi sharri" Ummiy ta fada ci ke da tsokana, hararan ta tayi "ke Ummi mi ye Haka already tana bakin ciki rabuwa da masoyin ta Kuma za ki Kara ma ta wani" Nanah ta fada wannan karon ai ko a tare su ka Kara kwashe da dariya, tsaki ta je ta shiga ciki ta bar su a wurin "yi hakurin ba mu mu ka Kar zoman ba ko ratayan ma ba abu ba wlh" ba ta tsaya sauraran su ba ta karasa ciki.
Mai jegon na ganin ta fara washe baki tana fadin "Matan Yayanmu yau dai Allah yayi, hope dai kin warke" murmushi kawai Zahrau ta yi sannan ta dauki baby.
Sai bayan isha'i ya Zo daukan ta su ka tafi, tana jin Ummiy na Mata tsiya ta share ta Dan Nanah ma mijin ta ya Zo ya dauke ta.
"Ehmm muna magana dazu" ya fada immediately bayan sun sauka daga gadan kawo.
"To ai ba Ka fada min sunan ba"
"Ke Zaki zaba ai Kinga Nima sai in zaba Miki nawa mai Dadi ko?"
Murmushi tayi sannan ta sadda Kai kasa "ke Wai yaushe za ki daina kunyan Nan ne?"
"Kana so in daina ne?"
"No kingane ya na Miki kyau Amma ya kamata ki dan rage kadan"
"Yauwa kaga kaja min maijiddah da Nanah na ta min dariya ko?"
"Dariyan me toh?"
"Wai Kai ka kulle ni a gida ka boye ni banje ba"
"Ai ba karya bane su kayi ba" saurin rufe bakin shi yayi ganin irin kallo da ta ke mishi.
"Au Haka za ka ce?" Ta fadi tana turo bakin ta
"Sorry i mean ai ba Haram Kika yi ba Koh?"
"Kai Unclee"
"Nace fa banso"
"Au yi hakuri"
"So choose a name for your husband"
"Ehmm let me guess then"
"Ina jiran ki"
"Ehmm Captain?" Hade rai yayi ya sha mur.
"Me kike nufi da Captain"
"Aikin ka Mana"
"Ka yanzu dan kaniyan ki colleagues Ina su Kira ni captain kema ki Kira ni captain?"
"To ni ban San me Zan ce ba kuma miye laifin captain in?"
"Just finds something special"
"Ni Uncleeee ko Yaya Aliyu In Kuma ba kaso in daina Kiran sunan ka"
Hararanta ta yayi "Ashe ko Zan fasa kanki"
"To kaima fa Fateema kake cemin"
Ba abinda ya Kara ce Mata har su ka Isa Zaria.
Washegari suna yarinya ta ci sunan Maman Ibrahim mijin maijiddah.
....
Bayan Sallah da Yan kwanaki su ka fara Shirin komawa Abuja ita dai Zahrau ba wai tana so bane don har ga zuciyan ta tafi jin dadin Zama a Zaria, don haka kwana biyu gabadaya gungunai ta ke mishi.
Zaune ya ke a gaban system in shi yana wani aiki ta shigo Falon ta zaune gab dashi "sannu da aiki" ta fadi ba tare da ya kalle ta ba ya amsa "Yauwa sannu daga Ina kike?"
"Na ji ka shiru ne shine na tafi gaida su Mami"
"Wa Kika tambaya?"
"Su Mami ne fa"
Taba baki yayi "ba dai kyau Mace ta dinga fita ba tare da izinin mijinta ba Kuma kinsan da hakan"
"Allah ya ba Ka hakura" ta fadi tana turo baki Daman Mai neman zuwa fada ne balle sarki ya Kira shi.
Da sauri ta tashi ta bar gun ta nufi dakin ta tana matse kwalla kafin kace kwabo ta fara kuka.
Sheshekan kukan ta ya jiyo, ya rasa me ke damun ta kwata kwata kwanan Nan abu kiris ta dinga kunkuni sai kuma kuka shi dai ya San da ba Haka ta ke ba though ya San tana da Saurin kuka Amma ba a banza ba. Infact in za ayi kwatancen Mai hankali a gidan ita ake fadi a cewarsu ta fi yaran gidan gabadaya natsuwa, tarbiyya da hankali, gashi ba ta da haniya riko ne kawai shaida da aka Mata Mara kyau. Shin ko dai shine ya canja ta? Ya tambayi kanshi hade da girgiza Kai, halin ta ne hakan in ka ganta sai ka rantse in aka sa Mata yatsa a baki ba zata cija ba Daman ace kaji tsoron shiru shirun mutum na ciki na ciki ne ko da wasa fa ba daman ya Mata fada sai ta Bata Rai. Tabbas gsky ma su iya magana da su ka ce Komin hasken farin wata dare abin tsoro ne, ga dai Zahrau Nan halayen ta na fili abin yabawa Amma Kuma na boyen masu firgitarwa.
Dakin na ta ya nufa da sauri Jin da gaske ta ke kukan na ta Bana kare bane. "Fateema" ya Kira ta Kai tsaye Amma shiru ba ta amsa ba, Folding hands in shi yayi ya hade rai "Wai ba magana na ke Miki ba?" wani irin tsawa ya Mata ba shiri ta dago tana Kallon shi "ta so ki zo" kawai ya ce ya fita ya bar dakin.
Sai da ta tsaya ta dauraye fuskan ta sannan ta fito ta same shi, Kashe system in na shi yayi ya dago ya fuskance ta "Zo ki fada min miye matsalan ki me ke damun ki" kusa dashi ya nuna Mata ba musu ta matso "me ke saki kuka? Gsky ne ba ki so" ya cigaba "ko ni dinne ba ki son Zama da da komai na Miki sai ki dinga ba ta Rai ki koma kuka."
Girgiza kanta tayi yace "baki za ki bude mu yi magana fa Baiwar Allah"
"Ka yi hakuri saurin kukan hali na ne tun asali"
"Na sani Amma Kuma ai ba ki kin gsky ko?"
"To ba Kai bane kaman ka daina so na" ita kanta sai da tayi magannan sannan ta yi saurin rufe baki. Bai son lokacin da ya saki dariya ba Yana Kallon ta "to ke kina Sona ne? Ai mutum Yana son me son shi ne"
"To ai ni bance bana sonka ba ko"
"To kina Sona kenan?" Ya tambaya sadda kanta kasa tayi cike da kunya.
"Come on Zo ki fada min" ya jawo ta jikin shi, ko Bata fada ya San cewa tana son nashi sosai ma Amma he want to confirm. Daga kanta tayi sannan ta yi saurin boye kanta a kirjin shi tana dariya kasa kasa.
"Kunyan Kuma na mene ne? Ki dena min fushi kina kuka Kinga Yana ba ta min Rai sosai fa"
"To Kai ka daina min fada banson fada"
"Ba fada na ke Miki ba Fateema Na ke fada Miki"
"Shi ne Kuma kake daure fuska?" Shiru yayi alamun tunani can ya ce "na daina ke ma ki daina kinji?"
Gyada Mai Kai tayi daganan Kuma aka luluka duniyan masoya.
Washegari su ka tattara yana su Yana su su kayi Abuja.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top